Mushaf Page 173
صفحة ١٧٣
- Ghunnah
- Qalqalah
- Ikhfa (Haqiqi)
- Ikhfa Shafawi
- Idgham with Ghunnah
- Idgham without Ghunnah
- Idgham Shafawi (Mimi)
- Madd Lazim (6 counts)
- Madd Wajib Muttasil (4-5 counts)
- Madd Jaiz Munfasil (2, 4, 6 counts)
Each word’s meaning appears right below it; the transliteration follows below the words.
Surah al-araf
- ۞ وَإِذْ نَتَقْنَا الْجَبَلَ فَوْقَهُمْ كَأَنَّهُ ظُلَّةٌ وَظَنُّوا أَنَّهُ وَاقِعٌ بِهِمْ خُذُوا مَا آتَيْنَاكُم بِقُوَّةٍ وَاذْكُرُوا مَا فِيهِ لَعَلَّكُمْ تَتَّقُونَKuma a lõkacin da muka ɗaukaka dũtse sama da su, kumar dai shi girgije ne, kuma suka haƙƙaƙe, lalle ne shĩ, mai fãɗuwa ne a gare su, (aka ce): "Ku karɓi abin da Muka kãwo muku da ƙarfi, kuma ku tuna abin da yake a cikinsa, tsammãninku kunã yin taƙawa."4 Views
- وَإِذْ أَخَذَ رَبُّكَ مِن بَنِي آدَمَ مِن ظُهُورِهِمْ ذُرِّيَّتَهُمْ وَأَشْهَدَهُمْ عَلَىٰ أَنفُسِهِمْ أَلَسْتُ بِرَبِّكُمْ ۖ قَالُوا بَلَىٰ ۛ شَهِدْنَا ۛ أَن تَقُولُوا يَوْمَ الْقِيَامَةِ إِنَّا كُنَّا عَنْ هَـٰذَا غَافِلِينَKuma a lõkacin da Ubangijinka Ya karɓi (alkawari) daga ɗiyan Ãdam, daga bãyayyakinsu, a zuriyarsu, kuma Ya shaidar da su a kan rãyukansu, (Ya ce): "Shin, bã Nĩ ne Ubangijinku ba?" Suka ce: "Na'am! Mun yi shaida!" (ya ce): "Kada ku ce a Rãnar Kiyãma: Lalle ne mũ, daga wannan, gafalallu ne."4 Views
- أَوْ تَقُولُوا إِنَّمَا أَشْرَكَ آبَاؤُنَا مِن قَبْلُ وَكُنَّا ذُرِّيَّةً مِّن بَعْدِهِمْ ۖ أَفَتُهْلِكُنَا بِمَا فَعَلَ الْمُبْطِلُونَKõ kuwa ku ce: "Abin sani kawai, ubanninmu suka yi shirki daga farko, kuma mũ, mun kasance zũriya daga bãyansu. Shin fa, Kanã halaka mu, sabõda abin da mãsu ɓãtãwa suka aikata?"4 Views
- وَكَذَٰلِكَ نُفَصِّلُ الْآيَاتِ وَلَعَلَّهُمْ يَرْجِعُونَKuma kamar haka Muke rarrabe ãyõyi, daki-daki; tsammãninsu, sunã kõmõwa.4 Views
- وَاتْلُ عَلَيْهِمْ نَبَأَ الَّذِي آتَيْنَاهُ آيَاتِنَا فَانسَلَخَ مِنْهَا فَأَتْبَعَهُ الشَّيْطَانُ فَكَانَ مِنَ الْغَاوِينَKa karanta a kansu lãbãrin wanda Muka kãwo masa ãyõyinMu, sai ya sãɓule daga gare su, sai shaidan ya bi shi, sai ya kasance a cikin halakakku.4 Views
- وَلَوْ شِئْنَا لَرَفَعْنَاهُ بِهَا وَلَـٰكِنَّهُ أَخْلَدَ إِلَى الْأَرْضِ وَاتَّبَعَ هَوَاهُ ۚ فَمَثَلُهُ كَمَثَلِ الْكَلْبِ إِن تَحْمِلْ عَلَيْهِ يَلْهَثْ أَوْ تَتْرُكْهُ يَلْهَث ۚ ذَّٰلِكَ مَثَلُ الْقَوْمِ الَّذِينَ كَذَّبُوا بِآيَاتِنَا ۚ فَاقْصُصِ الْقَصَصَ لَعَلَّهُمْ يَتَفَكَّرُونَKuma dã Mun so, da Mun ɗaukakã shi da su, kuma amma shĩ, ya nẽmi dawwama a cikin ƙasa, kuma ya bi son zũciyarsa. To, misãlinsa kamar misãlin kare ne, idan ka yi ɗauki a kansa ya yi lallage, kõ kuwa ka bar shi sai ya yi lallage, wannan ne misãlin mutãne waɗanda suka ƙaryata game da ãyõyinMu: Ka jẽranta karãtun lãbãrun; tsammãninsu sunã tunãni.4 Views
- سَاءَ مَثَلًا الْقَوْمُ الَّذِينَ كَذَّبُوا بِآيَاتِنَا وَأَنفُسَهُمْ كَانُوا يَظْلِمُونَTir da zama misãli, mutãnen da suka ƙaryata game da ãyõyinMu, kuma kansu suka kasance sunã zãlunta.4 Views
- مَن يَهْدِ اللَّهُ فَهُوَ الْمُهْتَدِي ۖ وَمَن يُضْلِلْ فَأُولَـٰئِكَ هُمُ الْخَاسِرُونَWanda Allah Ya shiryar, to, shĩ ne Mai shiryuwa, kuma wanda Ya ɓatar, to, waɗannan sũ ne mãsu hasãra.4 Views