Mushaf Page 427
صفحة ٤٢٧
- Ghunnah
- Qalqalah
- Ikhfa (Haqiqi)
- Ikhfa Shafawi
- Idgham with Ghunnah
- Idgham without Ghunnah
- Idgham Shafawi (Mimi)
- Madd Lazim (6 counts)
- Madd Wajib Muttasil (4-5 counts)
- Madd Jaiz Munfasil (2, 4, 6 counts)
Each word’s meaning appears right below it; the transliteration follows below the words.
Surah al-ahzab
- يَسْأَلُكَ النَّاسُ عَنِ السَّاعَةِ ۖ قُلْ إِنَّمَا عِلْمُهَا عِندَ اللَّهِ ۚ وَمَا يُدْرِيكَ لَعَلَّ السَّاعَةَ تَكُونُ قَرِيبًاSunã tambayar ka ga Sã'a. Ka ce: "Saninta yanã wurin Allah kawai." Kuma me yã sanar da kai cẽwa anã tsammãnin sa'a ta kasance kusa?1 Views
- إِنَّ اللَّهَ لَعَنَ الْكَافِرِينَ وَأَعَدَّ لَهُمْ سَعِيرًاLalle Allah Yã la'ani kãfirai, kuma Yã yi musu tattalin wata wuta mai ƙũna.1 Views
- خَالِدِينَ فِيهَا أَبَدًا ۖ لَّا يَجِدُونَ وَلِيًّا وَلَا نَصِيرًاSunã madawwama a cikinta har abada, bã su sãmun majiɓinci, kuma bã su sãmun mataimaki.1 Views
- يَوْمَ تُقَلَّبُ وُجُوهُهُمْ فِي النَّارِ يَقُولُونَ يَا لَيْتَنَا أَطَعْنَا اللَّهَ وَأَطَعْنَا الرَّسُولَاRãnar da ake jũya fuskõkinsu a cikin wuta sunã cẽwa, "Kaitonmu, sabõda, rashin biyarmu ga Allah da rashin biyarmu ga Manzo!"1 Views
- وَقَالُوا رَبَّنَا إِنَّا أَطَعْنَا سَادَتَنَا وَكُبَرَاءَنَا فَأَضَلُّونَا السَّبِيلَاKuma suka ce: "Yã Ubangijinmu! Lalle mũ mun bi shugabanninmu da manyanmu! Sai suka ɓatar da mu daga hanya!1 Views
- رَبَّنَا آتِهِمْ ضِعْفَيْنِ مِنَ الْعَذَابِ وَالْعَنْهُمْ لَعْنًا كَبِيرًا"Yã Ubangijinmu! Ka ba su ninki biyu na azãba, kuma ka la'ane su, la'ana mai girma."1 Views
- يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا لَا تَكُونُوا كَالَّذِينَ آذَوْا مُوسَىٰ فَبَرَّأَهُ اللَّهُ مِمَّا قَالُوا ۚ وَكَانَ عِندَ اللَّهِ وَجِيهًاYã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Kada ku kasance kamar waɗanda suka cũci Mũsã sa'an nan Allah Ya barrantar da shi daga abin da suka ce. Kuma ya kasance mai daraja a wurin Allah.1 Views
- يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا اتَّقُوا اللَّهَ وَقُولُوا قَوْلًا سَدِيدًاYã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku bi Allah da taƙawa kuma ku faɗi magana madaidaiciya.1 Views
- يُصْلِحْ لَكُمْ أَعْمَالَكُمْ وَيَغْفِرْ لَكُمْ ذُنُوبَكُمْ ۗ وَمَن يُطِعِ اللَّهَ وَرَسُولَهُ فَقَدْ فَازَ فَوْزًا عَظِيمًاYa kyautata muku ayyukanku, kuma Ya gãfarta zunubanku. Kuma wanda ya yi ɗã'a ga Allah da ManzonSa, to, lalle, yã rabbanta, babban rabo mai girma.1 Views
- إِنَّا عَرَضْنَا الْأَمَانَةَ عَلَى السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ وَالْجِبَالِ فَأَبَيْنَ أَن يَحْمِلْنَهَا وَأَشْفَقْنَ مِنْهَا وَحَمَلَهَا الْإِنسَانُ ۖ إِنَّهُ كَانَ ظَلُومًا جَهُولًاLalle Mũ, Mun gitta amãna ga sammai da ƙasã da duwãtsu, sai suka ƙi ɗaukarta kuma sukaji tsõro daga gare ta, kuma mutum ya ɗauke ta, lalle shĩ (mutum) ya kasance mai yawan zãlunci, mai yawan jãhilci.1 Views
- لِّيُعَذِّبَ اللَّهُ الْمُنَافِقِينَ وَالْمُنَافِقَاتِ وَالْمُشْرِكِينَ وَالْمُشْرِكَاتِ وَيَتُوبَ اللَّهُ عَلَى الْمُؤْمِنِينَ وَالْمُؤْمِنَاتِ ۗ وَكَانَ اللَّهُ غَفُورًا رَّحِيمًاDõmin Allah Ya azabta munãfukai maza da munãfukai mãtã, da mushirikai maza da mushirikai mãtã, kuma Allah Yã karɓi tũba ga mũminai maza da mũminai mãtã. Kuma Allah Yã kasance Mai gãfara, Mai jin ƙai.1 Views