Mushaf Page 555
صفحة ٥٥٥
- Ghunnah
- Qalqalah
- Ikhfa (Haqiqi)
- Ikhfa Shafawi
- Idgham with Ghunnah
- Idgham without Ghunnah
- Idgham Shafawi (Mimi)
- Madd Lazim (6 counts)
- Madd Wajib Muttasil (4-5 counts)
- Madd Jaiz Munfasil (2, 4, 6 counts)
Each word’s meaning appears right below it; the transliteration follows below the words.
Surah al-munafiqun
- وَإِذَا قِيلَ لَهُمْ تَعَالَوْا يَسْتَغْفِرْ لَكُمْ رَسُولُ اللَّهِ لَوَّوْا رُءُوسَهُمْ وَرَأَيْتَهُمْ يَصُدُّونَ وَهُم مُّسْتَكْبِرُونَKuma idan aka ce musu "Ku zo Manzon Allah ya nẽma maku gãfara," Sai su gyãɗa kãwunansu, kuma ka gan su sunã kangẽwa, alhãli kuwa sunã mãsu girman kai.0 Views
- سَوَاءٌ عَلَيْهِمْ أَسْتَغْفَرْتَ لَهُمْ أَمْ لَمْ تَسْتَغْفِرْ لَهُمْ لَن يَغْفِرَ اللَّهُ لَهُمْ ۚ إِنَّ اللَّهَ لَا يَهْدِي الْقَوْمَ الْفَاسِقِينَDaidai ne a kansu, kã nẽma musu gãfara kõ ba ka nẽmamusu ba. faufau Allah bã zai gãfarta musu ba. Lalle Allah, bã zai shiryar da mutãne fãsiƙai ba.0 Views
- هُمُ الَّذِينَ يَقُولُونَ لَا تُنفِقُوا عَلَىٰ مَنْ عِندَ رَسُولِ اللَّهِ حَتَّىٰ يَنفَضُّوا ۗ وَلِلَّهِ خَزَائِنُ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ وَلَـٰكِنَّ الْمُنَافِقِينَ لَا يَفْقَهُونَSũ ne waɗanda ke cẽwa "Kada ku ciyar a kan wanda ke wurin Manzon Allah har su wãtse," alhali kuwa taskõkin sammai da ƙasa ga Allah suke kuma amma munãfukai bã su fahimta.0 Views
- يَقُولُونَ لَئِن رَّجَعْنَا إِلَى الْمَدِينَةِ لَيُخْرِجَنَّ الْأَعَزُّ مِنْهَا الْأَذَلَّ ۚ وَلِلَّهِ الْعِزَّةُ وَلِرَسُولِهِ وَلِلْمُؤْمِنِينَ وَلَـٰكِنَّ الْمُنَافِقِينَ لَا يَعْلَمُونَSunã cẽwa "Lalle ne idan mun kõma zuwa Madĩnar, haƙĩƙa mafi rinjaya zai fitar da mafi ƙasƙanta daga gare ta, alhãli kuwa rinjãyar ga Allah take kuma da ManzonSa, kuma da mũminai, kuma amma munãfikai ba su sani ba."0 Views
- يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا لَا تُلْهِكُمْ أَمْوَالُكُمْ وَلَا أَوْلَادُكُمْ عَن ذِكْرِ اللَّهِ ۚ وَمَن يَفْعَلْ ذَٰلِكَ فَأُولَـٰئِكَ هُمُ الْخَاسِرُونَYa ku waɗanda suka yi ĩmãni! Kada dũkiyõyinku da ɗiyanku su shagaltar da ku daga ambaton Allah. Kuma wanda ya yi haka, to, waɗannan sũ ne mãsu hasãra.0 Views
- وَأَنفِقُوا مِن مَّا رَزَقْنَاكُم مِّن قَبْلِ أَن يَأْتِيَ أَحَدَكُمُ الْمَوْتُ فَيَقُولَ رَبِّ لَوْلَا أَخَّرْتَنِي إِلَىٰ أَجَلٍ قَرِيبٍ فَأَصَّدَّقَ وَأَكُن مِّنَ الصَّالِحِينَKuma ku ciyar daga abin da Muka azurta ku daga gãbanin mutuwa ta je wa ɗayanku har ya ce: "Yã Ubangijina! Don me ba Ka yi mini jinkiri ba zuwa ga wani ajali makusanci dõmin in gaskata kuma in kasance daga sãlihai?"0 Views
- وَلَن يُؤَخِّرَ اللَّهُ نَفْسًا إِذَا جَاءَ أَجَلُهَا ۚ وَاللَّهُ خَبِيرٌ بِمَا تَعْمَلُونَKuma Allah bã zai jinkirta wa wani rai ba idan ajalinsa ya je. Kuma Allah Masani ne ga abin da suke aikatãwa.0 Views