Mushaf Page 586
صفحة ٥٨٦
- Ghunnah
- Qalqalah
- Ikhfa (Haqiqi)
- Ikhfa Shafawi
- Idgham with Ghunnah
- Idgham without Ghunnah
- Idgham Shafawi (Mimi)
- Madd Lazim (6 counts)
- Madd Wajib Muttasil (4-5 counts)
- Madd Jaiz Munfasil (2, 4, 6 counts)
Each word’s meaning appears right below it; the transliteration follows below the words.
Surah at-takwir
Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
- إِذَا الشَّمْسُ كُوِّرَتْIdan rãna aka shafe haskenta1 Views
- وَإِذَا النُّجُومُ انكَدَرَتْKuma idan taurãri suka gurɓãce (wani ya shiga a cikin wani).1 Views
- وَإِذَا الْجِبَالُ سُيِّرَتْKuma idan duwãtsu aka tafiyar da su.1 Views
- وَإِذَا الْعِشَارُ عُطِّلَتْKuma idan rãƙuma mãsu cikunna aka sakẽ su wãwai, bã ga kõwa ba.1 Views
- وَإِذَا الْوُحُوشُ حُشِرَتْKuma idan dabbõbin dãji aka tattara su.1 Views
- وَإِذَا الْبِحَارُ سُجِّرَتْKuma idan tẽkuna aka mayar da su wuta.1 Views
- وَإِذَا النُّفُوسُ زُوِّجَتْKuma idan rãyuka aka haɗa su da jikunkunansu.1 Views
- وَإِذَا الْمَوْءُودَةُ سُئِلَتْKuma idan wadda aka turbuɗe ta da rai aka tambaye ta.1 Views
- بِأَيِّ ذَنبٍ قُتِلَتْ"Sabõda wane laifi ne aka kashe ta?"1 Views
- وَإِذَا الصُّحُفُ نُشِرَتْIdan takardun ayyuka aka wãtsa su (ga mãsu su).1 Views
- وَإِذَا السَّمَاءُ كُشِطَتْKuma idan sama aka fẽɗe ta.1 Views
- وَإِذَا الْجَحِيمُ سُعِّرَتْKuma idan Jahĩm aka hũra ta1 Views
- وَإِذَا الْجَنَّةُ أُزْلِفَتْKuma idan Aljanna aka kusantar da ita.1 Views
- عَلِمَتْ نَفْسٌ مَّا أَحْضَرَتْRai ya san abin da ya halartar (a rãnar nan).1 Views
- فَلَا أُقْسِمُ بِالْخُنَّسِTo, ba sai Na yi rantsuwa da taurãri matafã ba.1 Views
- الْجَوَارِ الْكُنَّسِMãsu gudu suna ɓũya.1 Views
- وَاللَّيْلِ إِذَا عَسْعَسَDa dare idan ya bãyar da bãya.1 Views
- وَالصُّبْحِ إِذَا تَنَفَّسَDa sãfiya idan ta yi lumfashi.1 Views
- إِنَّهُ لَقَوْلُ رَسُولٍ كَرِيمٍLalle ne shi (Alƙur'ãni) haƙƙan, maganar wani manzon (Allah) ne mai girma ga Allah.1 Views
- ذِي قُوَّةٍ عِندَ ذِي الْعَرْشِ مَكِينٍMai ƙarfi, mai daraja a wurin Mai Al'arshi.1 Views
- مُّطَاعٍ ثَمَّ أَمِينٍWanda ake yi wa ɗã'a (wato shugaban malã'iku) ne a can, amintacce.1 Views
- وَمَا صَاحِبُكُم بِمَجْنُونٍKuma abokinku ba mahaukaci ba ne.1 Views
- وَلَقَدْ رَآهُ بِالْأُفُقِ الْمُبِينِKuma lalle ne, yã gan shi a cikin sararin sama mabayyani.1 Views
- وَمَا هُوَ عَلَى الْغَيْبِ بِضَنِينٍKuma shi, ga gaibi bã mai rowa ba ne.1 Views
- وَمَا هُوَ بِقَوْلِ شَيْطَانٍ رَّجِيمٍKuma shi (Alƙur'ani) bã maganar shaiɗani, wanda aka la'ana, ba ce.1 Views
- فَأَيْنَ تَذْهَبُونَShin, a inã zã ku tafi?1 Views
- إِنْ هُوَ إِلَّا ذِكْرٌ لِّلْعَالَمِينَLalle ne shi (Alƙur'ãni), bã kõme ba ne fãce gargaɗi ga talikai.1 Views
- لِمَن شَاءَ مِنكُمْ أَن يَسْتَقِيمَGa wanda ya so, daga cikinku, ya shiryu.1 Views
- وَمَا تَشَاءُونَ إِلَّا أَن يَشَاءَ اللَّهُ رَبُّ الْعَالَمِينَKuma bã zã ku so ba sai idan Allah Ubangijin halitta Yã yarda.1 Views