78. an-naba
النبأ
Read Surah an-naba in full: surah 78, 40 verses, Meccan, Juz 30. Arabic text with Hausa translation.
- Ghunnah
- Qalqalah
- Ikhfa (Haqiqi)
- Ikhfa Shafawi
- Idgham with Ghunnah
- Idgham without Ghunnah
- Idgham Shafawi (Mimi)
- Madd Lazim (6 counts)
- Madd Wajib Muttasil (4-5 counts)
- Madd Jaiz Munfasil (2, 4, 6 counts)
Each word’s meaning appears right below it; the transliteration follows below the words.
Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
- عَمَّ يَتَسَاءَلُونَA kan mẽ suke tambayar jũna?1 Views
- عَنِ النَّبَإِ الْعَظِيمِA kan muhimmin lãbãri mai girma (Alƙur'ãni)?1 Views
- الَّذِي هُمْ فِيهِ مُخْتَلِفُونَWanda suke sãɓa wa jũna a cikinsa?1 Views
- كَلَّا سَيَعْلَمُونَA'aha! Zã su sani.1 Views
- ثُمَّ كَلَّا سَيَعْلَمُونَKuma, a'aha! Zã su sani.1 Views
- أَلَمْ نَجْعَلِ الْأَرْضَ مِهَادًاAshe, ba Mu sanya ƙasa shimfiɗa ba?1 Views
- وَالْجِبَالَ أَوْتَادًاDa duwãtsu turaku (ga riƙe ƙasa)?1 Views
- وَخَلَقْنَاكُمْ أَزْوَاجًاKuma, Mun halitta ku mazã da mãtã?1 Views
- وَجَعَلْنَا نَوْمَكُمْ سُبَاتًاKuma, Muka sanya barcinku hũtãwa?1 Views
- وَجَعَلْنَا اللَّيْلَ لِبَاسًاKuma, Muka sanya dare (ya zama) sutura?1 Views
- وَجَعَلْنَا النَّهَارَ مَعَاشًاKuma, Muka sanya yini (yazama) lõkacin nẽman abinci?1 Views
- وَبَنَيْنَا فَوْقَكُمْ سَبْعًا شِدَادًاKuma, Muka gina, a samanku, sammai bakwai mãsu ƙarfi?1 Views
- وَجَعَلْنَا سِرَاجًا وَهَّاجًاKuma, Muka sanya fitila mai tsanin haske (rãnã)?1 Views
- وَأَنزَلْنَا مِنَ الْمُعْصِرَاتِ مَاءً ثَجَّاجًاKuma, Muka saukar daga cikakkun girãgizai, ruwa mai yawan zuba?1 Views
- لِّنُخْرِجَ بِهِ حَبًّا وَنَبَاتًاDõmin, Mu fitar da ƙwaya da tsiri game da shi?1 Views
- وَجَنَّاتٍ أَلْفَافًاDa itãcen lambuna mãsu lillibniya?1 Views
- إِنَّ يَوْمَ الْفَصْلِ كَانَ مِيقَاتًاLalle ne, rãnar rarrabẽwa tã kasance abin ƙayyadẽ wa lõkaci.1 Views
- يَوْمَ يُنفَخُ فِي الصُّورِ فَتَأْتُونَ أَفْوَاجًاRãnar da zã a yi bũsa a cikin ƙaho, sai ku zo, jama'a jama'a.1 Views
- وَفُتِحَتِ السَّمَاءُ فَكَانَتْ أَبْوَابًاKuma, aka buɗe sama, sai ta kasance ƙõfõfi.1 Views
- وَسُيِّرَتِ الْجِبَالُ فَكَانَتْ سَرَابًاKuma, aka tafiyar da duwãtsu, sai suka kasance ƙũra.1 Views
- إِنَّ جَهَنَّمَ كَانَتْ مِرْصَادًاLalle ne, Jahannama tã kasance madãkata.1 Views
- لِّلطَّاغِينَ مَآبًاGa mãsu ƙẽtare iyãkõki, tã zama makõma.1 Views
- لَّابِثِينَ فِيهَا أَحْقَابًاSunã, mãsu zama a cikinta, zãmunna.1 Views
- لَّا يَذُوقُونَ فِيهَا بَرْدًا وَلَا شَرَابًاBã su ɗanɗanãwar wani sanyi a cikinta, kuma bã su ɗanɗana abin sha.1 Views
- إِلَّا حَمِيمًا وَغَسَّاقًاFãce tafasasshen ruwa da ruɓaɓɓen jini.1 Views
- جَزَاءً وِفَاقًاSakamako mai dãcẽwa.1 Views
- إِنَّهُمْ كَانُوا لَا يَرْجُونَ حِسَابًاLalle ne, sũ, sun kasance bã su fãtar sauƙin wani hisãbi.1 Views
- وَكَذَّبُوا بِآيَاتِنَا كِذَّابًاKuma, suka ƙaryata game da ãyõyinMu, ƙaryatãwa!1 Views
- وَكُلَّ شَيْءٍ أَحْصَيْنَاهُ كِتَابًاAlhãli, kõwane abu Mun ƙididdigẽ shi, a rubũce.1 Views
- فَذُوقُوا فَلَن نَّزِيدَكُمْ إِلَّا عَذَابًاSabõda haka, ku ɗanɗana domin haka, bã zã Mu ƙara muku kõme ba fãce azãba.1 Views
- إِنَّ لِلْمُتَّقِينَ مَفَازًاLalle ne, mãsu taƙawã nã da wani wurin sãmun babban rabo.3 Views
- حَدَائِقَ وَأَعْنَابًاLambuna da inabõbi.3 Views
- وَكَوَاعِبَ أَتْرَابًاDa cikakkun 'yammata, tsãrar jũna.3 Views
- وَكَأْسًا دِهَاقًاDa hinjãlan giya cikakku.3 Views
- لَّا يَسْمَعُونَ فِيهَا لَغْوًا وَلَا كِذَّابًاBã su jin yãsassar magana, a cikinta, kuma bã su jin ƙaryatãwa.3 Views
- جَزَاءً مِّن رَّبِّكَ عَطَاءً حِسَابًاDõmin sakamako daga Ubangijinka, kyautã mai yawa.3 Views
- رَّبِّ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ وَمَا بَيْنَهُمَا الرَّحْمَـٰنِ ۖ لَا يَمْلِكُونَ مِنْهُ خِطَابًاUbangijin sammai da ƙasa da abin da yake a tsakãninsu, Mai rahama, bã su da ikon yin wata magana daga gare Shi.3 Views
- يَوْمَ يَقُومُ الرُّوحُ وَالْمَلَائِكَةُ صَفًّا ۖ لَّا يَتَكَلَّمُونَ إِلَّا مَنْ أَذِنَ لَهُ الرَّحْمَـٰنُ وَقَالَ صَوَابًاRãnar da Rũhi da malã'iku zã su tsaya a cikin safu, bã su magana, sai wanda Allah Ya yi masa izni, kuma ya faɗi abin da ke daidai.3 Views
- ذَٰلِكَ الْيَوْمُ الْحَقُّ ۖ فَمَن شَاءَ اتَّخَذَ إِلَىٰ رَبِّهِ مَآبًاWancan, shi ne yini na gaskiya; to wanda ya so, ya riƙa makõma zuwa ga Ubangijinsa.3 Views
- إِنَّا أَنذَرْنَاكُمْ عَذَابًا قَرِيبًا يَوْمَ يَنظُرُ الْمَرْءُ مَا قَدَّمَتْ يَدَاهُ وَيَقُولُ الْكَافِرُ يَا لَيْتَنِي كُنتُ تُرَابًاLalle ne, Mũ, Mun yi muku gargaɗin azãba makusanciya, rãnar da mutum ke dũbi zuwa ga abin da hannãyensa suka aikata, kuma kafiri ya ce: "Kaitona, dã dai nã zama turɓãya!"3 Views
Teks Al-Qur'an: Tanzil Project (https://tanzil.net), lisensi CC BY 3.0. · Abubakar Mahmoud Gumi (Tanzil Project, tanzil.net)