Mushaf Page 583
صفحة ٥٨٣
- Ghunnah
- Qalqalah
- Ikhfa (Haqiqi)
- Ikhfa Shafawi
- Idgham with Ghunnah
- Idgham without Ghunnah
- Idgham Shafawi (Mimi)
- Madd Lazim (6 counts)
- Madd Wajib Muttasil (4-5 counts)
- Madd Jaiz Munfasil (2, 4, 6 counts)
Each word’s meaning appears right below it; the transliteration follows below the words.
Surah an-naba
- إِنَّ لِلْمُتَّقِينَ مَفَازًاLalle ne, mãsu taƙawã nã da wani wurin sãmun babban rabo.3 Views
- حَدَائِقَ وَأَعْنَابًاLambuna da inabõbi.3 Views
- وَكَوَاعِبَ أَتْرَابًاDa cikakkun 'yammata, tsãrar jũna.3 Views
- وَكَأْسًا دِهَاقًاDa hinjãlan giya cikakku.3 Views
- لَّا يَسْمَعُونَ فِيهَا لَغْوًا وَلَا كِذَّابًاBã su jin yãsassar magana, a cikinta, kuma bã su jin ƙaryatãwa.3 Views
- جَزَاءً مِّن رَّبِّكَ عَطَاءً حِسَابًاDõmin sakamako daga Ubangijinka, kyautã mai yawa.3 Views
- رَّبِّ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ وَمَا بَيْنَهُمَا الرَّحْمَـٰنِ ۖ لَا يَمْلِكُونَ مِنْهُ خِطَابًاUbangijin sammai da ƙasa da abin da yake a tsakãninsu, Mai rahama, bã su da ikon yin wata magana daga gare Shi.3 Views
- يَوْمَ يَقُومُ الرُّوحُ وَالْمَلَائِكَةُ صَفًّا ۖ لَّا يَتَكَلَّمُونَ إِلَّا مَنْ أَذِنَ لَهُ الرَّحْمَـٰنُ وَقَالَ صَوَابًاRãnar da Rũhi da malã'iku zã su tsaya a cikin safu, bã su magana, sai wanda Allah Ya yi masa izni, kuma ya faɗi abin da ke daidai.3 Views
- ذَٰلِكَ الْيَوْمُ الْحَقُّ ۖ فَمَن شَاءَ اتَّخَذَ إِلَىٰ رَبِّهِ مَآبًاWancan, shi ne yini na gaskiya; to wanda ya so, ya riƙa makõma zuwa ga Ubangijinsa.3 Views
- إِنَّا أَنذَرْنَاكُمْ عَذَابًا قَرِيبًا يَوْمَ يَنظُرُ الْمَرْءُ مَا قَدَّمَتْ يَدَاهُ وَيَقُولُ الْكَافِرُ يَا لَيْتَنِي كُنتُ تُرَابًاLalle ne, Mũ, Mun yi muku gargaɗin azãba makusanciya, rãnar da mutum ke dũbi zuwa ga abin da hannãyensa suka aikata, kuma kafiri ya ce: "Kaitona, dã dai nã zama turɓãya!"3 Views
Surah an-naziat
Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
- وَالنَّازِعَاتِ غَرْقًاIna rantsuwa da mala'iku mãsu fisgar rãyuka (na kafirai) da ƙarfi.3 Views
- وَالنَّاشِطَاتِ نَشْطًاDa mãsu ɗibar rãyuka (na mũminai) da sauƙi a cikin nishãɗi.3 Views
- وَالسَّابِحَاتِ سَبْحًاDa mãsu sauka daga sama da umurnin Allah kamar suna iyo.3 Views
- فَالسَّابِقَاتِ سَبْقًاSa'an nan, su zama mãsu gaugãwa (da umurnin Allah) kamar suna tsẽre.3 Views
- فَالْمُدَبِّرَاتِ أَمْرًاSa, an nan, su kasance masu shirya gudanar da umurni.3 Views
- يَوْمَ تَرْجُفُ الرَّاجِفَةُRãnar da mai girgiza abũbuwa (bũsar farko) zã ta kaɗa.3 Views
- تَتْبَعُهَا الرَّادِفَةُMai biyar ta (bũsa ta biyu) nã biye.3 Views
- قُلُوبٌ يَوْمَئِذٍ وَاجِفَةٌWasu zukãta, a rãnar nan, mãsu jin tsõro ne.3 Views
- أَبْصَارُهَا خَاشِعَةٌAlhãli idãnunsu na ƙasƙantattu.3 Views
- يَقُولُونَ أَإِنَّا لَمَرْدُودُونَ فِي الْحَافِرَةِSunã cẽwa "Ashe lalle zã a iya mayar da mu a kan sãwunmu?3 Views
- أَإِذَا كُنَّا عِظَامًا نَّخِرَةً"Ashe, idan muka zama ƙasusuwa rududdugaggu?"3 Views
- قَالُوا تِلْكَ إِذًا كَرَّةٌ خَاسِرَةٌSuka ce: "Waccan kam kõmãwa ce, tãɓaɓɓiya!"3 Views
- فَإِنَّمَا هِيَ زَجْرَةٌ وَاحِدَةٌTo, ita kam, tsãwa guda kawai ce.3 Views
- فَإِذَا هُم بِالسَّاهِرَةِSai kawai gã su a bãyan ƙasa.3 Views
- هَلْ أَتَاكَ حَدِيثُ مُوسَىٰShin, lãbãrin Mũsã ya zo maka?3 Views