Mushaf Page 584
صفحة ٥٨٤
- Ghunnah
- Qalqalah
- Ikhfa (Haqiqi)
- Ikhfa Shafawi
- Idgham with Ghunnah
- Idgham without Ghunnah
- Idgham Shafawi (Mimi)
- Madd Lazim (6 counts)
- Madd Wajib Muttasil (4-5 counts)
- Madd Jaiz Munfasil (2, 4, 6 counts)
Each word’s meaning appears right below it; the transliteration follows below the words.
Surah an-naziat
- إِذْ نَادَاهُ رَبُّهُ بِالْوَادِ الْمُقَدَّسِ طُوًىA lõkacin da Ubangijinsa Ya kirãye shi, a cikin kwari mai tsarki, wato Duwã?1 Views
- اذْهَبْ إِلَىٰ فِرْعَوْنَ إِنَّهُ طَغَىٰKa tafi zuwa ga Fir'auna, lalle ne shi, ya ƙẽtare haddi.1 Views
- فَقُلْ هَل لَّكَ إِلَىٰ أَن تَزَكَّىٰ"Sai ka ce masa, Kõ zã ka so ka tsarkaka.1 Views
- وَأَهْدِيَكَ إِلَىٰ رَبِّكَ فَتَخْشَىٰ"Kuma in shiryar da kai zuwa ga Ubangijinka domin ka ji tsoronSa?"1 Views
- فَأَرَاهُ الْآيَةَ الْكُبْرَىٰSai ya nũna masa ãyar nan mafi girma.1 Views
- فَكَذَّبَ وَعَصَىٰSai ya ƙaryata, kuma ya sãɓa (umurni),1 Views
- ثُمَّ أَدْبَرَ يَسْعَىٰSa'an nan ya jũya bãya, yanã tafiya da sauri.1 Views
- فَحَشَرَ فَنَادَىٰSai ya yi gayya, sa'an nan ya yi kira.1 Views
- فَقَالَ أَنَا رَبُّكُمُ الْأَعْلَىٰSai ya ce: "Nĩ ne Ubangijinku mafi ɗaudaka."1 Views
- فَأَخَذَهُ اللَّهُ نَكَالَ الْآخِرَةِ وَالْأُولَىٰSabõda haka Allah Ya kama shi, dõmin azãbar maganar ƙarshe da ta farko.1 Views
- إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَعِبْرَةً لِّمَن يَخْشَىٰLalle ne, a cikin wannan haƙiƙa akwai abin kula ga wanda yake tsõron Allah.1 Views
- أَأَنتُمْ أَشَدُّ خَلْقًا أَمِ السَّمَاءُ ۚ بَنَاهَاShin, kũ ne mafi wuyar halitta ko sama? Allah Ya gina ta.1 Views
- رَفَعَ سَمْكَهَا فَسَوَّاهَاYa ɗaukaka rufinta, sa'an nan Ya daidaita ta.1 Views
- وَأَغْطَشَ لَيْلَهَا وَأَخْرَجَ ضُحَاهَاKuma Ya duhuntar da darenta, kuma Ya fitar da hantsinta.1 Views
- وَالْأَرْضَ بَعْدَ ذَٰلِكَ دَحَاهَاKuma, ƙasa a bayan haka Ya mulmula ta.1 Views
- أَخْرَجَ مِنْهَا مَاءَهَا وَمَرْعَاهَاYa fitar da ruwanta daga gare ta da makiyãyarta.1 Views
- وَالْجِبَالَ أَرْسَاهَاDa duwatsu, Yã kafe ta.1 Views
- مَتَاعًا لَّكُمْ وَلِأَنْعَامِكُمْDomin jiyarwa dãɗi a gare ku, kuma ga dabbõbinku.1 Views
- فَإِذَا جَاءَتِ الطَّامَّةُ الْكُبْرَىٰTo, idan uwar masĩfu, mafi girma, ta zo.1 Views
- يَوْمَ يَتَذَكَّرُ الْإِنسَانُ مَا سَعَىٰRãnar da mutum zai yi tunãnin abin da ya aikata.1 Views
- وَبُرِّزَتِ الْجَحِيمُ لِمَن يَرَىٰKuma, a bayyana Jahĩm ga mai gani.1 Views
- فَأَمَّا مَن طَغَىٰTo, amma wanda ya yi girman kai.1 Views
- وَآثَرَ الْحَيَاةَ الدُّنْيَاKuma, ya zãɓi rãyuwa ta kusa, (wato dũniya).1 Views
- فَإِنَّ الْجَحِيمَ هِيَ الْمَأْوَىٰTo, lalle ne Jahĩm, ita ce makõma.1 Views
- وَأَمَّا مَنْ خَافَ مَقَامَ رَبِّهِ وَنَهَى النَّفْسَ عَنِ الْهَوَىٰKuma, amma wanda ya ji tsõron tsayi a gaba ga Ubangijinsa, kuma ya kange kansa daga son rai.1 Views
- فَإِنَّ الْجَنَّةَ هِيَ الْمَأْوَىٰTo, lalle ne Aljanna ita ce makõma.1 Views
- يَسْأَلُونَكَ عَنِ السَّاعَةِ أَيَّانَ مُرْسَاهَاSunã tambayar ka game da sa'a, wai yaushe ne matabbatarta?1 Views
- فِيمَ أَنتَ مِن ذِكْرَاهَاMe ya haɗã ka da ambatonta?1 Views
- إِلَىٰ رَبِّكَ مُنتَهَاهَاZuwa ga Ubangijinka ƙarshen al'amarinta yake.1 Views
- إِنَّمَا أَنتَ مُنذِرُ مَن يَخْشَاهَاKai mai gargaɗi kawai ne ga mai tsõron ta.1 Views
- كَأَنَّهُمْ يَوْمَ يَرَوْنَهَا لَمْ يَلْبَثُوا إِلَّا عَشِيَّةً أَوْ ضُحَاهَاKamar sũ a rãnar da zã su gan ta, ba su zauna ba fãce a lõkacin marẽce ko hantsinsa.1 Views