Juz 27
الجزء ٢٧
- Ghunnah
- Qalqalah
- Ikhfa (Haqiqi)
- Ikhfa Shafawi
- Idgham with Ghunnah
- Idgham without Ghunnah
- Idgham Shafawi (Mimi)
- Madd Lazim (6 counts)
- Madd Wajib Muttasil (4-5 counts)
- Madd Jaiz Munfasil (2, 4, 6 counts)
Each word’s meaning appears right below it; the transliteration follows below the words.
Surah adh-dhariyat
- ۞ قَالَ فَمَا خَطْبُكُمْ أَيُّهَا الْمُرْسَلُونَ(Ibrãĩm) ya ce: "To mẽne ne babban al'almarinku, yã kũ Manzanni!"0 Views
- قَالُوا إِنَّا أُرْسِلْنَا إِلَىٰ قَوْمٍ مُّجْرِمِينَSuka ce: "Lalle mũ, an aike mu zuwa ga waɗansu mutãne, mãsu laifi.0 Views
- لِنُرْسِلَ عَلَيْهِمْ حِجَارَةً مِّن طِينٍ"Dõmin mu saka musu waɗansu duwãtsu na wani yumɓu (bom).0 Views
- مُّسَوَّمَةً عِندَ رَبِّكَ لِلْمُسْرِفِينَ"Waɗanda aka yi wa alãma daga wajen Ubangijinka, dõmin mãsu ɓarna."0 Views
- فَأَخْرَجْنَا مَن كَانَ فِيهَا مِنَ الْمُؤْمِنِينَSa'an, nan Muka fitar da wanda ya kasance a cikinta daga mũminai.0 Views
- فَمَا وَجَدْنَا فِيهَا غَيْرَ بَيْتٍ مِّنَ الْمُسْلِمِينَSai dai ba mu sãmu ba, a cikinta, fãce gida guda na Musulmi.0 Views
- وَتَرَكْنَا فِيهَا آيَةً لِّلَّذِينَ يَخَافُونَ الْعَذَابَ الْأَلِيمَKuma Muka bar wata ãyã, a cikinta, ga waɗanda ke jin tsõron azãba, mai raɗaɗi.0 Views
- وَفِي مُوسَىٰ إِذْ أَرْسَلْنَاهُ إِلَىٰ فِرْعَوْنَ بِسُلْطَانٍ مُّبِينٍKuma ga Mũsã, a lõkacin da Muka aiko shi zuwa ga Fir'auna da wani dalĩli bayyananne.0 Views
- فَتَوَلَّىٰ بِرُكْنِهِ وَقَالَ سَاحِرٌ أَوْ مَجْنُونٌSai ya jũya bãya tãre da ƙarfinsa, kuma ya ce: "Mai sihiri ne kõ kuwa mahaukaci!"0 Views
- فَأَخَذْنَاهُ وَجُنُودَهُ فَنَبَذْنَاهُمْ فِي الْيَمِّ وَهُوَ مُلِيمٌSabõda haka, Muka kama shi tãre da rundunarsa, sa'an nan Muka jẽfa su a cikin tẽku, alhãli kuwa yanã wanda ake zargi.0 Views
- وَفِي عَادٍ إِذْ أَرْسَلْنَا عَلَيْهِمُ الرِّيحَ الْعَقِيمَKuma ga Ãdãwa, a lõkacin da Muka aika iska ƙẽƙasasshiya a kansu.0 Views
- مَا تَذَرُ مِن شَيْءٍ أَتَتْ عَلَيْهِ إِلَّا جَعَلَتْهُ كَالرَّمِيمِBã ta barin kõme da ta jẽ a kansa, fãce ta mayar da shi kamar rududdugaggun ƙasũsuwa.0 Views
- وَفِي ثَمُودَ إِذْ قِيلَ لَهُمْ تَمَتَّعُوا حَتَّىٰ حِينٍKuma ga Samũdãwa, a lõkacin da aka ce musu: "Ku ji ɗan dãɗi har wani ɗan lõkaci,"0 Views
- فَعَتَوْا عَنْ أَمْرِ رَبِّهِمْ فَأَخَذَتْهُمُ الصَّاعِقَةُ وَهُمْ يَنظُرُونَSai suka yi girman kai ga umurnin Ubangijinsu, sabõda haka tsãwa ta kãma su, alhãli kuwa sunã kallo.0 Views
- فَمَا اسْتَطَاعُوا مِن قِيَامٍ وَمَا كَانُوا مُنتَصِرِينَBa su kõ sãmu dãmar tsayãwa ba, kuma ba su kasance mãsu nẽman ãgaji ba.0 Views
- وَقَوْمَ نُوحٍ مِّن قَبْلُ ۖ إِنَّهُمْ كَانُوا قَوْمًا فَاسِقِينَDa mutãnen Nũhu a gabãnin haka, lalle sun kasance waɗansu irin mutãne ne fãsiƙai.0 Views
- وَالسَّمَاءَ بَنَيْنَاهَا بِأَيْدٍ وَإِنَّا لَمُوسِعُونَKuma sama, mun gina ta da wani irin ƙarfi, alhãli kuwa lalle Mũ ne Mãsu yalwatãwa.0 Views
- وَالْأَرْضَ فَرَشْنَاهَا فَنِعْمَ الْمَاهِدُونَKuma ƙasã Mun shimfiɗa ta, To, madalla da mãsu shimfiɗãwa, Mũ,0 Views
- وَمِن كُلِّ شَيْءٍ خَلَقْنَا زَوْجَيْنِ لَعَلَّكُمْ تَذَكَّرُونَKuma daga kõme Mun halitta nau'i biyu, watakila zã ku yi tunãni.0 Views
- فَفِرُّوا إِلَى اللَّهِ ۖ إِنِّي لَكُم مِّنْهُ نَذِيرٌ مُّبِينٌSabõda haka ku gudu zuwa ga Allah, lalle nĩ mai gargaɗi kawai ne a gare ku, mai bayyanannen gargaɗi.0 Views
- وَلَا تَجْعَلُوا مَعَ اللَّهِ إِلَـٰهًا آخَرَ ۖ إِنِّي لَكُم مِّنْهُ نَذِيرٌ مُّبِينٌKuma kada ku sanya, tãre da Allah wani abin bautãwa na dabam, lalle nĩ, mai gargaɗi kawai ne a gare ku, mai bayyanannen gargaɗi.0 Views
- كَذَٰلِكَ مَا أَتَى الَّذِينَ مِن قَبْلِهِم مِّن رَّسُولٍ إِلَّا قَالُوا سَاحِرٌ أَوْ مَجْنُونٌKamar haka dai wani Manzo bai jẽ wa waɗanda ke gabãninsu ba fãce sun ce: "Mai sihiri ne kõ mahaukaci."0 Views
- أَتَوَاصَوْا بِهِ ۚ بَلْ هُمْ قَوْمٌ طَاغُونَshin, sunã yi wa jũna wasiyya da shi ne? Ã'a, sũ dai mutãne ne mãsu girman kai.0 Views
- فَتَوَلَّ عَنْهُمْ فَمَا أَنتَ بِمَلُومٍSai ka jũya daga barinsu, kuma kai ba abin zargi ba ne.0 Views
- وَذَكِّرْ فَإِنَّ الذِّكْرَىٰ تَنفَعُ الْمُؤْمِنِينَKuma ka tunãtar, dõmin tunãtarwa tanã amfãnin mũminai.0 Views
- وَمَا خَلَقْتُ الْجِنَّ وَالْإِنسَ إِلَّا لِيَعْبُدُونِKuma Ban halitta aljannu da mutãne ba sai dõmin su bauta Mini.0 Views
- مَا أُرِيدُ مِنْهُم مِّن رِّزْقٍ وَمَا أُرِيدُ أَن يُطْعِمُونِBã Ni nufln (sãmun) wani arziki daga gare su, Bã Ni nufin su (yi Mini hidimar) ciyar da Ni.0 Views
- إِنَّ اللَّهَ هُوَ الرَّزَّاقُ ذُو الْقُوَّةِ الْمَتِينُLalle Allah, Shĩ ne Mai azurtãwa, Mai ĩkon yi, Mai cikakken ƙarfi.0 Views
- فَإِنَّ لِلَّذِينَ ظَلَمُوا ذَنُوبًا مِّثْلَ ذَنُوبِ أَصْحَابِهِمْ فَلَا يَسْتَعْجِلُونِTo, lalle waɗanda suka yi zãlunci sunã da masaki (na ɗĩban zunubi) kamar masakin abõkansu, sabõda haka kada su yi Mini gaggãwa.0 Views
- فَوَيْلٌ لِّلَّذِينَ كَفَرُوا مِن يَوْمِهِمُ الَّذِي يُوعَدُونَSabõda haka, bone ya tabbata ga waɗanda suka kãfirta, daga rãnar su wadda aka yi musu alkawari.0 Views
Surah at-tur
Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
- وَالطُّورِInã rantsuwa da ¦ũr (Dũtsen Mũsã).0 Views
- وَكِتَابٍ مَّسْطُورٍDa wani littãfi rubũtacce.0 Views
- فِي رَقٍّ مَّنشُورٍA cikin wata takardar fãta shimfiɗaɗɗa.0 Views
- وَالْبَيْتِ الْمَعْمُورِDa Gidan da aka rãyar da shi (da ibãda).0 Views
- وَالسَّقْفِ الْمَرْفُوعِDa rufin nan da aka ɗaukaka.0 Views
- وَالْبَحْرِ الْمَسْجُورِDa tẽkun nan da aka cika (da ruwa).0 Views
- إِنَّ عَذَابَ رَبِّكَ لَوَاقِعٌLalle, azãbar Ubangijinka, haƙĩƙa, mai aukuwa ce.0 Views
- مَّا لَهُ مِن دَافِعٍBã ta da mai tunkuɗẽwa.0 Views
- يَوْمَ تَمُورُ السَّمَاءُ مَوْرًاRãnar da samã ke yin mõtsi tanã kai kãwo.0 Views
- وَتَسِيرُ الْجِبَالُ سَيْرًاKuma duwãtsu nã tafiya sunã shũɗẽwa.0 Views
- فَوَيْلٌ يَوْمَئِذٍ لِّلْمُكَذِّبِينَTo, bone yã tabbata a rãnar nan ga mãsu ƙaryatãwa.0 Views
- الَّذِينَ هُمْ فِي خَوْضٍ يَلْعَبُونَWaɗanda suke a cikin kududdufi sunã wãsã.0 Views
- يَوْمَ يُدَعُّونَ إِلَىٰ نَارِ جَهَنَّمَ دَعًّاRãnar da zã a tunkuɗa su zuwa wutar Jahannama, tunkuɗãwa.0 Views
- هَـٰذِهِ النَّارُ الَّتِي كُنتُم بِهَا تُكَذِّبُونَ(A ce musu): "Wannan ita ce wutar da kuka kasance kunã ƙaryatãwa game da ita."0 Views
- أَفَسِحْرٌ هَـٰذَا أَمْ أَنتُمْ لَا تُبْصِرُونَ"To, shin wannan sihiri ne kõ kuwa kũ ne bã ku gani?"0 Views
- اصْلَوْهَا فَاصْبِرُوا أَوْ لَا تَصْبِرُوا سَوَاءٌ عَلَيْكُمْ ۖ إِنَّمَا تُجْزَوْنَ مَا كُنتُمْ تَعْمَلُونَ"Ku shigẽ ta. To, ku yi haƙuri ko kuma kada ku yi haƙuri, dai dai ne a kanku, kawai anã yi muku sakamakon abin da kuka kasance kunã aikatãwa."0 Views
- إِنَّ الْمُتَّقِينَ فِي جَنَّاتٍ وَنَعِيمٍLalle, mãsu taƙawa, sunã a cikin gidãjen Aljanna da wata ni'ima.0 Views
- فَاكِهِينَ بِمَا آتَاهُمْ رَبُّهُمْ وَوَقَاهُمْ رَبُّهُمْ عَذَابَ الْجَحِيمِSunã mãsu jin dãɗi da abin da Ubangijinsu Ya ba su, kuma Ubangijinsu Ya tsãre musu azãbar Jahĩm.0 Views
- كُلُوا وَاشْرَبُوا هَنِيئًا بِمَا كُنتُمْ تَعْمَلُونَ(A ce musu): "Ku ci, ku sha, da ni'ima, dõmin abin da kuka kasance kunã aikatãwa."0 Views
- مُتَّكِئِينَ عَلَىٰ سُرُرٍ مَّصْفُوفَةٍ ۖ وَزَوَّجْنَاهُم بِحُورٍ عِينٍSunã kishingiɗe a kan karagu waɗanda ke cikin sahu, kuma Muka aurar da su waɗansu mãtã mãsu farin idãnu, mãsu girmansu.0 Views
- وَالَّذِينَ آمَنُوا وَاتَّبَعَتْهُمْ ذُرِّيَّتُهُم بِإِيمَانٍ أَلْحَقْنَا بِهِمْ ذُرِّيَّتَهُمْ وَمَا أَلَتْنَاهُم مِّنْ عَمَلِهِم مِّن شَيْءٍ ۚ كُلُّ امْرِئٍ بِمَا كَسَبَ رَهِينٌKuma waɗanda suka yi ĩmãni kuma zũriyarsu suka bĩ su ga ĩmãnin, Mun riskar da zũriyarsu da su, alhãli kuwa bã da Mun rage musu kõme ba daga aikinsu, kõwane mutum jingina ne ga abin da ya sana'anta.0 Views
- وَأَمْدَدْنَاهُم بِفَاكِهَةٍ وَلَحْمٍ مِّمَّا يَشْتَهُونَKuma Muka yalwata musu 'ya'yan itãce da nãma irin wanda suke marmari.0 Views
- يَتَنَازَعُونَ فِيهَا كَأْسًا لَّا لَغْوٌ فِيهَا وَلَا تَأْثِيمٌSunã mĩƙa wa jũnansu a cikinta hinjãlan giya, wadda bãbu yãsassar magana a cikinta, kuma bãbu jin nauyin zunubi.0 Views
- ۞ وَيَطُوفُ عَلَيْهِمْ غِلْمَانٌ لَّهُمْ كَأَنَّهُمْ لُؤْلُؤٌ مَّكْنُونٌKuma waɗansu samãri nã gẽwayãwa a kansu, kamar dai sũ lu'ulu'u ne wanda ke kulle.0 Views
- وَأَقْبَلَ بَعْضُهُمْ عَلَىٰ بَعْضٍ يَتَسَاءَلُونَWaɗansunsu suka fuskanta zuwa ga waɗansu, sunã tambayar jũna.0 Views
- قَالُوا إِنَّا كُنَّا قَبْلُ فِي أَهْلِنَا مُشْفِقِينَSuka ce: "Lalle mũ mun kasance a gabãnin wannan (a dũniya) a cikin iyãlanmu munã jin tsõro."0 Views
- فَمَنَّ اللَّهُ عَلَيْنَا وَوَقَانَا عَذَابَ السَّمُومِ"To, Allah Yã yi mana kyautar falala, kuma Yã tsare mana azãbar iskar zãfi."0 Views
- إِنَّا كُنَّا مِن قَبْلُ نَدْعُوهُ ۖ إِنَّهُ هُوَ الْبَرُّ الرَّحِيمُ"Lalle mũ mun kasance, a gãbanin haka, munã kiran sa. Lalle Shĩ, Shĩ ne Mai kyautatãwa, Mai rahama."0 Views
- فَذَكِّرْ فَمَا أَنتَ بِنِعْمَتِ رَبِّكَ بِكَاهِنٍ وَلَا مَجْنُونٍTo, ka tunãtar kai fa sabõda ni'imar Ubangjinka, bã bõka kake ba, kuma bã mahaukaci ba.0 Views
- أَمْ يَقُولُونَ شَاعِرٌ نَّتَرَبَّصُ بِهِ رَيْبَ الْمَنُونِShin zã su ce: "Mawãƙi ne, munã jiran, masĩfun mutuwa game da shĩ"?0 Views
- قُلْ تَرَبَّصُوا فَإِنِّي مَعَكُم مِّنَ الْمُتَرَبِّصِينَKa ce: "Ku yi jira, domin nĩ ma lalle inã a cikin mãsu jira tãre da ku."0 Views
- أَمْ تَأْمُرُهُمْ أَحْلَامُهُم بِهَـٰذَا ۚ أَمْ هُمْ قَوْمٌ طَاغُونَShin, hankulansu ne ke umarin su da wannan, kõ kuwa sũ wasu mutãne ne mãsu ƙetare haddi?0 Views
- أَمْ يَقُولُونَ تَقَوَّلَهُ ۚ بَل لَّا يُؤْمِنُونَShin, cẽwa suke yi: "Shi ne ke ƙãga faɗarsa"? Ã'a ba su dai yi ĩmãni ba.0 Views
- فَلْيَأْتُوا بِحَدِيثٍ مِّثْلِهِ إِن كَانُوا صَادِقِينَSai su zõ da wani lãbãri mai misãlinsa idan sun kasance sũmãsu gaskiya ne.0 Views
- أَمْ خُلِقُوا مِنْ غَيْرِ شَيْءٍ أَمْ هُمُ الْخَالِقُونَShin, an halitta su ne bã daga kõme ba, kõ kuwa sũ ne mãsu yin halitta?0 Views
- أَمْ خَلَقُوا السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضَ ۚ بَل لَّا يُوقِنُونَShin, sun halitta sammai da ƙasa ne? Ã'a ba su dai yi ĩmãnin yaƙĩni ba.0 Views
- أَمْ عِندَهُمْ خَزَائِنُ رَبِّكَ أَمْ هُمُ الْمُصَيْطِرُونَShin, taskõkin Ubangijinka, sunã a wurinsu ne? Kõ kuwa sũ ne mãsu rinjãya?0 Views
- أَمْ لَهُمْ سُلَّمٌ يَسْتَمِعُونَ فِيهِ ۖ فَلْيَأْتِ مُسْتَمِعُهُم بِسُلْطَانٍ مُّبِينٍShin, sunã da wani tsãni ne wanda suke (hawa sunã) saurãron (lãbãrin samã) a cikinsa? Sai mai saurarõnsu ya zo da wani dalĩli bayyananne.0 Views
- أَمْ لَهُ الْبَنَاتُ وَلَكُمُ الْبَنُونَShin, Yanã da 'ya'ya mãtã ne kuma kũ, kunã da ɗiya maza ne?0 Views
- أَمْ تَسْأَلُهُمْ أَجْرًا فَهُم مِّن مَّغْرَمٍ مُّثْقَلُونَShin, kanã tambayar su wata ijãra ne, sabõda haka suka zama mãsu jin nauyin biyan tãrar?0 Views
- أَمْ عِندَهُمُ الْغَيْبُ فَهُمْ يَكْتُبُونَShin, a wurinsu akwai ilmin gaibi, sabõda haka sunã rubũtãwa?0 Views
- أَمْ يُرِيدُونَ كَيْدًا ۖ فَالَّذِينَ كَفَرُوا هُمُ الْمَكِيدُونَShin, sunã nufin wani kaidi ne? To, waɗanda suka kãfirta sũ ne waɗanda ake yi wa kaidi.0 Views
- أَمْ لَهُمْ إِلَـٰهٌ غَيْرُ اللَّهِ ۚ سُبْحَانَ اللَّهِ عَمَّا يُشْرِكُونَShin, sunã da wani abin bautãwa ne wanda bã Allah ba? Tsarki ya tabbata ga Allah daga abin da suke yi na shirki!0 Views
- وَإِن يَرَوْا كِسْفًا مِّنَ السَّمَاءِ سَاقِطًا يَقُولُوا سَحَابٌ مَّرْكُومٌKuma idan sun ga wani ɓaɓɓake daga samã yãnã fãɗuwa, sai su ce wani girgije ne, mai hauhawar jũna.0 Views
- فَذَرْهُمْ حَتَّىٰ يُلَاقُوا يَوْمَهُمُ الَّذِي فِيهِ يُصْعَقُونَTo, ka bar su, sai sun haɗu da yinin nan da za a sũmar da su a cikinsa.0 Views
- يَوْمَ لَا يُغْنِي عَنْهُمْ كَيْدُهُمْ شَيْئًا وَلَا هُمْ يُنصَرُونَRãnar da kaidinsu bã ya wadãtar masu da kõme, kuma bã a taimakon su.0 Views
- وَإِنَّ لِلَّذِينَ ظَلَمُوا عَذَابًا دُونَ ذَٰلِكَ وَلَـٰكِنَّ أَكْثَرَهُمْ لَا يَعْلَمُونَKuma lalle, waɗannan da suka yi zãluncin, sunã da azãba (a nan dũniya) banda waccan, kuma mafi yawansu ba su sani ba.0 Views
- وَاصْبِرْ لِحُكْمِ رَبِّكَ فَإِنَّكَ بِأَعْيُنِنَا ۖ وَسَبِّحْ بِحَمْدِ رَبِّكَ حِينَ تَقُومُSai ka yi hakuri da hukuncin Ubangijinka, lalle kai fa kanã idãnunMu, kuma ka tsarkake Ubangijinka da (tasbĩhi) game da gõde Masa a lõkacin da kake tãshi tsaye (dõmin salla kõ wani abu).0 Views
- وَمِنَ اللَّيْلِ فَسَبِّحْهُ وَإِدْبَارَ النُّجُومِKuma daga dare, sai ka tsarkake Shi (da tasbĩhin) dalõkacin jũyãwar taurãri.0 Views
Surah an-najm
Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
- وَالنَّجْمِ إِذَا هَوَىٰInã rantsuwa da taurãron, a lõkacin da ya faku.4 Views
- مَا ضَلَّ صَاحِبُكُمْ وَمَا غَوَىٰMa'abũcinku bai ɓata ba, kuma bai ƙẽtare haddi ba.4 Views
- وَمَا يَنطِقُ عَنِ الْهَوَىٰKuma bã ya yin magana daga son zuciyarsa.4 Views
- إِنْ هُوَ إِلَّا وَحْيٌ يُوحَىٰ(Maganarsa) ba ta zamo ba, fãce wahayi ne da ake aikõwa.4 Views
- عَلَّمَهُ شَدِيدُ الْقُوَىٰ(Malã'ika) mai tsananin ƙarfi ya sanar da shi.4 Views
- ذُو مِرَّةٍ فَاسْتَوَىٰMa'abũcin ƙarfi da kwarjini, sa'an nan ya daidaita.4 Views
- وَهُوَ بِالْأُفُقِ الْأَعْلَىٰAlhãli kuwa yanã a sararin samã mafi aukaka.4 Views
- ثُمَّ دَنَا فَتَدَلَّىٰSa'an nan ya kusanta, kuma ya matsa zurõwa.4 Views
- فَكَانَ قَابَ قَوْسَيْنِ أَوْ أَدْنَىٰHar ya kasance gwargwadon zirã'i biyu, kõ kuma abin da ya fi kusa.4 Views
- فَأَوْحَىٰ إِلَىٰ عَبْدِهِ مَا أَوْحَىٰSa'an nan ya yi wahayi zuwa ga bãwan Allah (Muhammadu) da abin da ya faɗa (masa).4 Views
- مَا كَذَبَ الْفُؤَادُ مَا رَأَىٰZũciyar (Annabi) bata ƙaryata abin da ya gani ba.4 Views
- أَفَتُمَارُونَهُ عَلَىٰ مَا يَرَىٰShin, zã ku yi masa musu a kan abin da yake gani?4 Views
- وَلَقَدْ رَآهُ نَزْلَةً أُخْرَىٰKuma lalle ya gan shi, haƙĩƙatan, a wani lõkacin saukarsa.4 Views
- عِندَ سِدْرَةِ الْمُنتَهَىٰA wurin da magaryar tuƙẽwa take.4 Views
- عِندَهَا جَنَّةُ الْمَأْوَىٰA inda taken, nan Aljannar makoma take.4 Views
- إِذْ يَغْشَى السِّدْرَةَ مَا يَغْشَىٰLõkacin da abin da yake rufe magaryar tuƙẽwa ya rufe ta.4 Views
- مَا زَاغَ الْبَصَرُ وَمَا طَغَىٰGaninsa bai karkata ba, kuma bai ƙetare haddi ba.4 Views
- لَقَدْ رَأَىٰ مِنْ آيَاتِ رَبِّهِ الْكُبْرَىٰLalle, tabbas, (Annabinku) ya ga waɗanda suka fi girma daga ãyõyin Ubangijinsa.4 Views
- أَفَرَأَيْتُمُ اللَّاتَ وَالْعُزَّىٰShin, kun ga Lãta da uzza?4 Views
- وَمَنَاةَ الثَّالِثَةَ الْأُخْرَىٰDa (wani gunki wai shi) Manãta, na ukunsu?4 Views
- أَلَكُمُ الذَّكَرُ وَلَهُ الْأُنثَىٰAshe, kũ ne da ɗa namiji Shĩ (Allah) kuma da ɗiya mace?4 Views
- تِلْكَ إِذًا قِسْمَةٌ ضِيزَىٰWannan fa ya zama rabo naƙasasshe.4 Views
- إِنْ هِيَ إِلَّا أَسْمَاءٌ سَمَّيْتُمُوهَا أَنتُمْ وَآبَاؤُكُم مَّا أَنزَلَ اللَّهُ بِهَا مِن سُلْطَانٍ ۚ إِن يَتَّبِعُونَ إِلَّا الظَّنَّ وَمَا تَهْوَى الْأَنفُسُ ۖ وَلَقَدْ جَاءَهُم مِّن رَّبِّهِمُ الْهُدَىٰWaɗannan bã kõme ba ne fãce sũnãye, waɗanda kuka ambace su da su, kũ da uwãyenku. Allah bai saukar da wani dalĩli game da su ba. (Kãfirai) bã su biyar kõme fãce zato da abin da rãyukansu ke so, Alhãli kuwa shiriyar ta daga wajen Ubangijinsu, ta jẽ musu (sai suka bar ta suka kõma wa zaton).4 Views
- أَمْ لِلْإِنسَانِ مَا تَمَنَّىٰKo (an fai cẽwa) mutum zai sãmi abin da yake gũri?4 Views
- فَلِلَّهِ الْآخِرَةُ وَالْأُولَىٰTo, Lãhira da dũniya na Allah kawai ne (wanda ya nẽme su daga wani, yã yi kuskure).4 Views
- ۞ وَكَم مِّن مَّلَكٍ فِي السَّمَاوَاتِ لَا تُغْنِي شَفَاعَتُهُمْ شَيْئًا إِلَّا مِن بَعْدِ أَن يَأْذَنَ اللَّهُ لِمَن يَشَاءُ وَيَرْضَىٰAkwai malã'iku da yawa a cikin sammai cẽtonsu bã ya wadãtar da kõme fãce bãyan Allah Yã yi izni (da shi) ga wanda Yake so, kuma Yake yarda.4 Views
- إِنَّ الَّذِينَ لَا يُؤْمِنُونَ بِالْآخِرَةِ لَيُسَمُّونَ الْمَلَائِكَةَ تَسْمِيَةَ الْأُنثَىٰLalle waɗannan da bã su yin ĩmãni da Lãhira, haƙĩƙa sunã kiran malã'iku da sũnan mace.4 Views
- وَمَا لَهُم بِهِ مِنْ عِلْمٍ ۖ إِن يَتَّبِعُونَ إِلَّا الظَّنَّ ۖ وَإِنَّ الظَّنَّ لَا يُغْنِي مِنَ الْحَقِّ شَيْئًاKuma bã su da wani ilmi game da shi, bã su bin kõme fãce zato alhãli kuwa lalle zato bã ya amfãnar da kõme daga gaskiya.4 Views
- فَأَعْرِضْ عَن مَّن تَوَلَّىٰ عَن ذِكْرِنَا وَلَمْ يُرِدْ إِلَّا الْحَيَاةَ الدُّنْيَاSabõda haka sai ka kau da kai daga wanda ya jũya bãya daga ambatonMu kuma bai yi nufin kõme ba fãce rãyuwar kusa (dũniya).4 Views
- ذَٰلِكَ مَبْلَغُهُم مِّنَ الْعِلْمِ ۚ إِنَّ رَبَّكَ هُوَ أَعْلَمُ بِمَن ضَلَّ عَن سَبِيلِهِ وَهُوَ أَعْلَمُ بِمَنِ اهْتَدَىٰWannan ita ce iyãkar abin da suke iya kai gare shi na ilmi. lalle Ubangijinka Shĩ ne Mafi sanin wanda ya ɓace daga hanyarSa, kuma Shi ne Mafi sani ga wanda ya nẽmi shiriya.4 Views
- وَلِلَّهِ مَا فِي السَّمَاوَاتِ وَمَا فِي الْأَرْضِ لِيَجْزِيَ الَّذِينَ أَسَاءُوا بِمَا عَمِلُوا وَيَجْزِيَ الَّذِينَ أَحْسَنُوا بِالْحُسْنَىKuma abin da ke cikin sammai da abin da yake a cikin ƙasã na Allah kawai ne, dõmin Yã sãka wa waɗanda suka mũnana da abin da suka aikata, kuma Ya sãka wa waɗanda suki kyautata da sakamakon da ya fi kyau.4 Views
- الَّذِينَ يَجْتَنِبُونَ كَبَائِرَ الْإِثْمِ وَالْفَوَاحِشَ إِلَّا اللَّمَمَ ۚ إِنَّ رَبَّكَ وَاسِعُ الْمَغْفِرَةِ ۚ هُوَ أَعْلَمُ بِكُمْ إِذْ أَنشَأَكُم مِّنَ الْأَرْضِ وَإِذْ أَنتُمْ أَجِنَّةٌ فِي بُطُونِ أُمَّهَاتِكُمْ ۖ فَلَا تُزَكُّوا أَنفُسَكُمْ ۖ هُوَ أَعْلَمُ بِمَنِ اتَّقَىٰWaɗanda ke nĩsantar manyan zunubai da abũbuwan alfãsha, fãce ƙanãnan laifuffuka, lalle Ubangijinka Mai yalwatattar gãfara ne, Shĩ ne Ya fi sani ga abinda ke gare ku a lõkacin da Ya ƙãga halittarku daga ƙasa, kuma a lõkacin da kuke tãyuna a cikin cikannan uwãyenku. Sabõda haka, kada ku tsarkake kanku, Shĩ ne Mafi sani ga wanda ya yi taƙawa.4 Views
- أَفَرَأَيْتَ الَّذِي تَوَلَّىٰShin, ka ga wannan da ya jũya baya?4 Views
- وَأَعْطَىٰ قَلِيلًا وَأَكْدَىٰYa yi kyauta kaɗan, kuma ya yi rowa?4 Views
- أَعِندَهُ عِلْمُ الْغَيْبِ فَهُوَ يَرَىٰShin, akwai ilmin gaibi a wurinsa, Sabõda haka yanã ganin gaibin?4 Views
- أَمْ لَمْ يُنَبَّأْ بِمَا فِي صُحُفِ مُوسَىٰKo kuwa ba a ba shi lãbãri ba ga abin da yake a cikin Littafan Mũsã?4 Views
- وَإِبْرَاهِيمَ الَّذِي وَفَّىٰDa Ibrãhĩm wanda ya cika alkawari?4 Views
- أَلَّا تَزِرُ وَازِرَةٌ وِزْرَ أُخْرَىٰCẽwa wani rai mai kãyan laifi bã ya ɗaukar kãyan laifin wani.4 Views
- وَأَن لَّيْسَ لِلْإِنسَانِ إِلَّا مَا سَعَىٰKuma mutum bã shi da kõme fãce abin da ya aikata.4 Views
- وَأَنَّ سَعْيَهُ سَوْفَ يُرَىٰKuma lalle, aikinsa zã a gan shi.4 Views
- ثُمَّ يُجْزَاهُ الْجَزَاءَ الْأَوْفَىٰSa'an nan a sãka masa da sakamako wanda yake mafi cikar ma'auni?4 Views
- وَأَنَّ إِلَىٰ رَبِّكَ الْمُنتَهَىٰKuma lalle, makõmar zuwa Ubangijinka kawai take?4 Views
- وَأَنَّهُ هُوَ أَضْحَكَ وَأَبْكَىٰKuma lalle, Shĩ, Shĩ ne Ya sanya dariya, kuma Ya sanya kũka.4 Views
- وَأَنَّهُ هُوَ أَمَاتَ وَأَحْيَاKuma lalle, Shĩ, Shĩ ne Ya kashe, kuma Ya rãyar.4 Views
- وَأَنَّهُ خَلَقَ الزَّوْجَيْنِ الذَّكَرَ وَالْأُنثَىٰKuma lalle Shĩ ne Ya yi halitta nau'i-nau'i, namiji da mace.4 Views
- مِن نُّطْفَةٍ إِذَا تُمْنَىٰDaga wani ɗigon ruwa guda a lõkacin da ake jẽfa shi a cikin mahaifa.4 Views
- وَأَنَّ عَلَيْهِ النَّشْأَةَ الْأُخْرَىٰKuma a kansa ne ƙãga halitta ta biyu take.4 Views
- وَأَنَّهُ هُوَ أَغْنَىٰ وَأَقْنَىٰKuma lalle, Shĩ, Shĩ ne Ya azurta, kuma Ya wadãtar.4 Views
- وَأَنَّهُ هُوَ رَبُّ الشِّعْرَىٰKuma lalle, Shĩ, Shi ne Ubangijin Shi'ira.4 Views
- وَأَنَّهُ أَهْلَكَ عَادًا الْأُولَىٰKuma lalle, Shĩ, Shĩ ne Ya halaka Ãdãwa na farko.4 Views
- وَثَمُودَ فَمَا أَبْقَىٰDa Samũdãwa, sa'an nan bai rage su ba.4 Views
- وَقَوْمَ نُوحٍ مِّن قَبْلُ ۖ إِنَّهُمْ كَانُوا هُمْ أَظْلَمَ وَأَطْغَىٰDa mutãnen Nũhu a gabãnin haka, lalle sũ sun kasance mafi zãlunci kuma mafi girman kai.4 Views
- وَالْمُؤْتَفِكَةَ أَهْوَىٰDa waɗanda aka birkice ƙasarsu, Ya kãyar da su.4 Views
- فَغَشَّاهَا مَا غَشَّىٰSa'an nan abin da ya rufe su, ya rufe su.4 Views
- فَبِأَيِّ آلَاءِ رَبِّكَ تَتَمَارَىٰTo, da wace daga ni'imõmin Ubangijinka kake yin shakka?4 Views
- هَـٰذَا نَذِيرٌ مِّنَ النُّذُرِ الْأُولَىٰwannan (Muhammadu) mai gargaɗi ne kamar irin mãsu gargaɗi na farko.4 Views
- أَزِفَتِ الْآزِفَةُMakusanciya fa, tã yi kusa.4 Views
- لَيْسَ لَهَا مِن دُونِ اللَّهِ كَاشِفَةٌBãbu wani rai, banda Allah, mai iya bãyani gare ta.4 Views
- أَفَمِنْ هَـٰذَا الْحَدِيثِ تَعْجَبُونَShin, kuma daga wannan lãbãri kuke mãmãki?4 Views
- وَتَضْحَكُونَ وَلَا تَبْكُونَKuma kunã yin dãriya, kuma bã ku yin kũka?4 Views
- وَأَنتُمْ سَامِدُونَAlhãli kunã mãsu wãsã?4 Views
- 53:62۩ Sajdahفَاسْجُدُوا لِلَّهِ وَاعْبُدُوا ۩To, ku yi tawãli'u ga Allah, kuma ku bauta (masa).4 Views
Surah al-qamar
Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
- اقْتَرَبَتِ السَّاعَةُ وَانشَقَّ الْقَمَرُSã'a ta yi kusa, kuma wata ya tsãge.0 Views
- وَإِن يَرَوْا آيَةً يُعْرِضُوا وَيَقُولُوا سِحْرٌ مُّسْتَمِرٌّKuma idan sun ga wata ãyã, sai su juya baya su ce: "Sihiri ne mai dõgẽwa!"0 Views
- وَكَذَّبُوا وَاتَّبَعُوا أَهْوَاءَهُمْ ۚ وَكُلُّ أَمْرٍ مُّسْتَقِرٌّKuma suka ƙaryata, kuma suka bi son zũciyarsu, alhãli kuwa kõwane al'amari (wanda suke son su tũre daga Annabi) an tabbatar da shi.0 Views
- وَلَقَدْ جَاءَهُم مِّنَ الْأَنبَاءِ مَا فِيهِ مُزْدَجَرٌKuma lalle, abin da yake akwai tsãwatarwa a cikinsa na lãbãraiya zo musu.0 Views
- حِكْمَةٌ بَالِغَةٌ ۖ فَمَا تُغْنِ النُّذُرُHikima cikakka! Sai dai abũbuwan gargaɗi bã su amfãni.0 Views
- فَتَوَلَّ عَنْهُمْ ۘ يَوْمَ يَدْعُ الدَّاعِ إِلَىٰ شَيْءٍ نُّكُرٍSabõda haka, ka bar su! Rãnar da mai kiran zai yi kira zuwa ga wani abu abin ƙyama.0 Views
- خُشَّعًا أَبْصَارُهُمْ يَخْرُجُونَ مِنَ الْأَجْدَاثِ كَأَنَّهُمْ جَرَادٌ مُّنتَشِرٌ¡asƙantattu ga idanunsu zã su fito daga kaburburansu, kamar dai sũ fãri ne waɗandasuka wãtse.0 Views
- مُّهْطِعِينَ إِلَى الدَّاعِ ۖ يَقُولُ الْكَافِرُونَ هَـٰذَا يَوْمٌ عَسِرٌSunã gaggãwar tafiya zuwa ga mai kiran, kãfirai na cẽwa, "Wannan yini ne mai wuya!"0 Views
- ۞ كَذَّبَتْ قَبْلَهُمْ قَوْمُ نُوحٍ فَكَذَّبُوا عَبْدَنَا وَقَالُوا مَجْنُونٌ وَازْدُجِرَMutãnen Nũhu sun ƙaryata, a gabãninsu, sai suka ƙaryata BawanMu, kuma suka ce: "Shi mahaukaci ne." Kuma aka tsãwace shi.0 Views
- فَدَعَا رَبَّهُ أَنِّي مَغْلُوبٌ فَانتَصِرْSabõda haka, ya kira Ubangijinsa (ya ce), "Lalle nĩ, an rinjãye ni, sai Ka yi taimako."0 Views
- فَفَتَحْنَا أَبْوَابَ السَّمَاءِ بِمَاءٍ مُّنْهَمِرٍSai Muka bũɗe kõfõfin sama da ruwa mai zuba.0 Views
- وَفَجَّرْنَا الْأَرْضَ عُيُونًا فَالْتَقَى الْمَاءُ عَلَىٰ أَمْرٍ قَدْ قُدِرَKuma Muka ɓuɓɓugar da ƙasã ta zama idãnun ruwa, daɗa ruwa ya haɗu a kan wani umurni da aka riga aka ƙaddara shi.0 Views
- وَحَمَلْنَاهُ عَلَىٰ ذَاتِ أَلْوَاحٍ وَدُسُرٍKuma Muka ɗauke Nũhu a kan (jirgi) na alluna da ƙũsõshi.0 Views
- تَجْرِي بِأَعْيُنِنَا جَزَاءً لِّمَن كَانَ كُفِرَTanã gudãna, a kan idãnunMu, dõmin sakamako ga wanda aka yi wa kãfircin.0 Views
- وَلَقَد تَّرَكْنَاهَا آيَةً فَهَلْ مِن مُّدَّكِرٍKuma lalle, Mun bar ta ta zama ãyã. To, Shin, akwai mai tunãni0 Views
- فَكَيْفَ كَانَ عَذَابِي وَنُذُرِTo, yãyã azãbãTa take da gargaɗiNa?2 Views
- وَلَقَدْ يَسَّرْنَا الْقُرْآنَ لِلذِّكْرِ فَهَلْ مِن مُّدَّكِرٍKuma lalle ne, haƙĩkƙa, Mun sauƙaƙe Alƙur'ãni, dõmin tunãwa. To, shin, akwai mai tunãwa?1 Views
- كَذَّبَتْ عَادٌ فَكَيْفَ كَانَ عَذَابِي وَنُذُرِÃdãwa sun ƙaryata, to, yãya azãbãTa take, da gargaɗiNa?0 Views
- إِنَّا أَرْسَلْنَا عَلَيْهِمْ رِيحًا صَرْصَرًا فِي يَوْمِ نَحْسٍ مُّسْتَمِرٍّLalle Mũ, Mun aika da iska mai tsananin sauti a kansu, a cikin wani yinin nahĩsa mai dõgẽwa.0 Views
- تَنزِعُ النَّاسَ كَأَنَّهُمْ أَعْجَازُ نَخْلٍ مُّنقَعِرٍTanã fizgar mutãne kamar dai sũ kututturan dabĩno tumɓukakku ne.0 Views
- فَكَيْفَ كَانَ عَذَابِي وَنُذُرِTo, yãya azãbãTa take da gargaɗiNa?2 Views
- وَلَقَدْ يَسَّرْنَا الْقُرْآنَ لِلذِّكْرِ فَهَلْ مِن مُّدَّكِرٍKuma lalle ne, haƙiƙa Mun sauƙaƙe Alƙur'ani, dõmin tunãwa. To, shin, akwai mai tunãwa?1 Views
- كَذَّبَتْ ثَمُودُ بِالنُّذُرِSamũdãwa sun ƙaryata game da gargaɗin.2 Views
- فَقَالُوا أَبَشَرًا مِّنَّا وَاحِدًا نَّتَّبِعُهُ إِنَّا إِذًا لَّفِي ضَلَالٍ وَسُعُرٍSai suka ce: "Wani mutum daga cikinmu, shi kaɗai, wai mu bĩ shi! Lalle mũ a lõkacin, haƙĩƙa mun shiga wata ɓata da haukã.0 Views
- أَأُلْقِيَ الذِّكْرُ عَلَيْهِ مِن بَيْنِنَا بَلْ هُوَ كَذَّابٌ أَشِرٌ"Shin, an jẽfa masa Manzancin ne, a tsakãninmu? Ã'a, shĩ dai gawurtaccen maƙaryaci ne mai girman kai!"0 Views
- سَيَعْلَمُونَ غَدًا مَّنِ الْكَذَّابُ الْأَشِرُZã su sani a gõbe, wãne ne gawurtaccen mai ƙaryar, mai girman kan?0 Views
- إِنَّا مُرْسِلُو النَّاقَةِ فِتْنَةً لَّهُمْ فَارْتَقِبْهُمْ وَاصْطَبِرْLalle Mũ, mãsu aikãwa da rãƙumar ne, ta zame musu fitina, sai ka tsare su da kallo, kuma ka yi haƙuri.0 Views
- وَنَبِّئْهُمْ أَنَّ الْمَاءَ قِسْمَةٌ بَيْنَهُمْ ۖ كُلُّ شِرْبٍ مُّحْتَضَرٌKuma ka bã su lãbãri cẽwa ruwa rababbe ne a tsakãninsu (da rãƙumar), kõwane sha, mai shi yanã halartar sa.0 Views
- فَنَادَوْا صَاحِبَهُمْ فَتَعَاطَىٰ فَعَقَرَSai suka kira abokinsu, sai ya karɓa, sa'an nan ya sõke ta,0 Views
- فَكَيْفَ كَانَ عَذَابِي وَنُذُرِTo, yãya azãbaTa take da gargaɗiNa?2 Views
- إِنَّا أَرْسَلْنَا عَلَيْهِمْ صَيْحَةً وَاحِدَةً فَكَانُوا كَهَشِيمِ الْمُحْتَظِرِLalle Mũ, Mun aika tsãwa guda a kansu, sai suka kasance kamar yãyin mai shinge.0 Views
- وَلَقَدْ يَسَّرْنَا الْقُرْآنَ لِلذِّكْرِ فَهَلْ مِن مُّدَّكِرٍKuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun sauƙaƙe Alƙur'ani, dõmin tunãwa. To, shin, akwai mai tunãwa?1 Views
- كَذَّبَتْ قَوْمُ لُوطٍ بِالنُّذُرِMutãnen Lũɗu sun ƙaryata, game da gargaɗi.2 Views
- إِنَّا أَرْسَلْنَا عَلَيْهِمْ حَاصِبًا إِلَّا آلَ لُوطٍ ۖ نَّجَّيْنَاهُم بِسَحَرٍLalle Mun aika iskar tsakuwa a kansu, fãce mabiyan Lũɗu, Mun tsirar da su a lõkacin asuba.0 Views
- نِّعْمَةً مِّنْ عِندِنَا ۚ كَذَٰلِكَ نَجْزِي مَن شَكَرَSabõda wata ni'ima ta daga gare Mu. Kamar haka Muke sãka wa wanda ya gõde.0 Views
- وَلَقَدْ أَنذَرَهُم بَطْشَتَنَا فَتَمَارَوْا بِالنُّذُرِKuma lalle, haƙĩƙa, ya yi musu gargaɗin damƙarMu, sai suka yi musu game da gargaɗin.2 Views
- وَلَقَدْ رَاوَدُوهُ عَن ضَيْفِهِ فَطَمَسْنَا أَعْيُنَهُمْ فَذُوقُوا عَذَابِي وَنُذُرِKuma lalle haƙĩƙa, su, sun nẽme shi ta wajen bãƙinsa, sai Muka shãfe idãnunsu. "To, ku ɗanɗani azãbaTa da gargaɗĩNa."0 Views
- وَلَقَدْ صَبَّحَهُم بُكْرَةً عَذَابٌ مُّسْتَقِرٌّKuma lalle, haƙĩƙa, wata azãba matabbaciya tã wãye musu gari da yãƙi, tun da sãfe.0 Views
- فَذُوقُوا عَذَابِي وَنُذُرِTo, ku ɗanɗani azãbãTa da gargaɗĩNa.2 Views
- وَلَقَدْ يَسَّرْنَا الْقُرْآنَ لِلذِّكْرِ فَهَلْ مِن مُّدَّكِرٍKuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun sauƙaƙe Alƙur, ani dõmin tunãwa. To, shin, akwai mai tunãwa?1 Views
- وَلَقَدْ جَاءَ آلَ فِرْعَوْنَ النُّذُرُKuma lalle, haƙĩƙa, gargaɗin ya jẽ wa mabiyan Fir'auna.2 Views
- كَذَّبُوا بِآيَاتِنَا كُلِّهَا فَأَخَذْنَاهُمْ أَخْذَ عَزِيزٍ مُّقْتَدِرٍSun ƙaryata game da ãyõyinMu, dukansu sai Muka kãma su, irin kãmun Mabuwãyi, Mai ĩkon yi.0 Views
- أَكُفَّارُكُمْ خَيْرٌ مِّنْ أُولَـٰئِكُمْ أَمْ لَكُم بَرَاءَةٌ فِي الزُّبُرِShin, kãfiranku ne mafi alhẽri daga waɗancan, ko kuwa kunã da wata barã'a a cikin littattafai?0 Views
- أَمْ يَقُولُونَ نَحْنُ جَمِيعٌ مُّنتَصِرٌKõ zã su ce: "Mũ duka mãsu haɗa ƙarfi ne dõmin cin nasara?"0 Views
- سَيُهْزَمُ الْجَمْعُ وَيُوَلُّونَ الدُّبُرَZã a karya tãron, kuma su jũya bãya dõmin gudu.0 Views
- بَلِ السَّاعَةُ مَوْعِدُهُمْ وَالسَّاعَةُ أَدْهَىٰ وَأَمَرُّÃ'a, Sã'a ita cẽ lõkacin wa'adinsu, kuma Sã'ar tã fi tsananin masĩfa, kuma ta fiɗãci.0 Views
- إِنَّ الْمُجْرِمِينَ فِي ضَلَالٍ وَسُعُرٍLalle ne, mãsu laifi sunã a cikin ɓata da hauka.0 Views
- يَوْمَ يُسْحَبُونَ فِي النَّارِ عَلَىٰ وُجُوهِهِمْ ذُوقُوا مَسَّ سَقَرَRãnar da zã a jã su a cikin wuta a kan fuskõkinsu. "Ku ɗanɗani shãfar wutar Saƙar."0 Views
- إِنَّا كُلَّ شَيْءٍ خَلَقْنَاهُ بِقَدَرٍLalle Mũ, kõwane irin abu Mun halitta shi a kan tsãri.0 Views
- وَمَا أَمْرُنَا إِلَّا وَاحِدَةٌ كَلَمْحٍ بِالْبَصَرِKuma umurninMu bai zamo ba fãce da kalma ɗaya, kamar walƙãwar ido.0 Views
- وَلَقَدْ أَهْلَكْنَا أَشْيَاعَكُمْ فَهَلْ مِن مُّدَّكِرٍKuma lalle ne haƙĩƙa, Mun halaka irin gayyarku. To, shin, akwai mai tunãni?0 Views
- وَكُلُّ شَيْءٍ فَعَلُوهُ فِي الزُّبُرِKuma kõwane abu, da suka aikata shi, yanã a cikin littattafai.0 Views
- وَكُلُّ صَغِيرٍ وَكَبِيرٍ مُّسْتَطَرٌKuma dukkan ƙarami da babba, rubutacce ne.0 Views
- إِنَّ الْمُتَّقِينَ فِي جَنَّاتٍ وَنَهَرٍLalle mãsu taƙawa sunã a cikin gidãjen Aljanna da kõguna.0 Views
- فِي مَقْعَدِ صِدْقٍ عِندَ مَلِيكٍ مُّقْتَدِرٍA cikin mazaunin gaskiya, wurin Mai ikon yi, Mai iya zartaswa.0 Views
Surah ar-rahman
Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
- الرَّحْمَـٰنُ(Allah) Mai rahama.0 Views
- عَلَّمَ الْقُرْآنَYã sanar da Alƙur'ani.0 Views
- خَلَقَ الْإِنسَانَYã halitta mutum.0 Views
- عَلَّمَهُ الْبَيَانَYã sanar da shi bayãni (magana).0 Views
- الشَّمْسُ وَالْقَمَرُ بِحُسْبَانٍRãnã da watã a kan lissãfi suke.0 Views
- وَالنَّجْمُ وَالشَّجَرُ يَسْجُدَانِKuma tsirrai mãsu yãɗo da itãce sunã tawãlu'i.0 Views
- وَالسَّمَاءَ رَفَعَهَا وَوَضَعَ الْمِيزَانَKuma samã Ya ɗaukaka ta, Kuma Yã aza sikẽli.0 Views
- أَلَّا تَطْغَوْا فِي الْمِيزَانِDõmin kada ku karkatar da sikẽlin.0 Views
- وَأَقِيمُوا الْوَزْنَ بِالْقِسْطِ وَلَا تُخْسِرُوا الْمِيزَانَKuma ku daidaita awo da ãdalci, kuma kada ku rage sikẽlin.0 Views
- وَالْأَرْضَ وَضَعَهَا لِلْأَنَامِKuma ƙasã Yã aza ta dõmin tãlikai.0 Views
- فِيهَا فَاكِهَةٌ وَالنَّخْلُ ذَاتُ الْأَكْمَامِA cikinta akwai 'ya'yan itãcen marmari da dabĩno mai kwasfa.0 Views
- وَالْحَبُّ ذُو الْعَصْفِ وَالرَّيْحَانُDa ƙwãya mai sõshiya da ƙamshi.0 Views
- فَبِأَيِّ آلَاءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِTo, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangjinku kuke ƙaryatãwa?0 Views
- خَلَقَ الْإِنسَانَ مِن صَلْصَالٍ كَالْفَخَّارِYã halitta mutum daga ƙẽkasasshen yumɓu kumar kasko.0 Views
- وَخَلَقَ الْجَانَّ مِن مَّارِجٍ مِّن نَّارٍKuma ya halitta aljani daga bira daga wutã.0 Views
- فَبِأَيِّ آلَاءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِTo, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?0 Views
- رَبُّ الْمَشْرِقَيْنِ وَرَبُّ الْمَغْرِبَيْنِUbangjin mafita biyu na rãnã, kuma Ubangijin mafãɗã biyu na rãnã.0 Views
- فَبِأَيِّ آلَاءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِTo, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?0 Views
- مَرَجَ الْبَحْرَيْنِ يَلْتَقِيَانِYã garwaya tẽku biyu (ruwan dãɗi da na zartsi) sunã haɗuwa.0 Views
- بَيْنَهُمَا بَرْزَخٌ لَّا يَبْغِيَانِA tsakãninsu akwai shãmaki, bã za su ƙetare haddi ba.0 Views
- فَبِأَيِّ آلَاءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِTo, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?0 Views
- يَخْرُجُ مِنْهُمَا اللُّؤْلُؤُ وَالْمَرْجَانُLu'ulu'u da murjãni na fita daga gare su.0 Views
- فَبِأَيِّ آلَاءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِTo, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?0 Views
- وَلَهُ الْجَوَارِ الْمُنشَآتُ فِي الْبَحْرِ كَالْأَعْلَامِKuma Yanã da manyan jirãge, waɗanda ake ƙãgãwa a cikin tẽku kamar manyan duwãtsu.0 Views
- فَبِأَيِّ آلَاءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِTo, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?0 Views
- كُلُّ مَنْ عَلَيْهَا فَانٍDukkan wanda ke kanta mai ƙãrẽwa ne.0 Views
- وَيَبْقَىٰ وَجْهُ رَبِّكَ ذُو الْجَلَالِ وَالْإِكْرَامِKuma Fuskarar Ubangijinka, Mai girman Jalala da karimci, ita ce take wanzuwa.0 Views
- فَبِأَيِّ آلَاءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِTo, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?0 Views
- يَسْأَلُهُ مَن فِي السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ ۚ كُلَّ يَوْمٍ هُوَ فِي شَأْنٍwanda ke a cikin sammai da ƙasã yanã rõƙon Sa (Allah), a kullum Allah na a cikin wani sha'ani.0 Views
- فَبِأَيِّ آلَاءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِTo, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?0 Views
- سَنَفْرُغُ لَكُمْ أَيُّهَ الثَّقَلَانِZã mu ɗauki lõkaci sabõda ku, yã kũ mãsu nauyin halitta biyu!0 Views
- فَبِأَيِّ آلَاءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِTo, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?0 Views
- يَا مَعْشَرَ الْجِنِّ وَالْإِنسِ إِنِ اسْتَطَعْتُمْ أَن تَنفُذُوا مِنْ أَقْطَارِ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ فَانفُذُوا ۚ لَا تَنفُذُونَ إِلَّا بِسُلْطَانٍYa jama'ar aljannu da mutãne! Idan kunã iya zarcẽwa daga sãsannin sammai da ƙasã to ku zarce. Bã za ku iya zarcẽwaba fãce da wani dalĩli.0 Views
- فَبِأَيِّ آلَاءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِTo, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?0 Views
- يُرْسَلُ عَلَيْكُمَا شُوَاظٌ مِّن نَّارٍ وَنُحَاسٌ فَلَا تَنتَصِرَانِAnã sako wani harshe daga wata wutã a kanku, da narkakkiyar tagulla. To, bã zã ku nẽmi taimako ba?0 Views
- فَبِأَيِّ آلَاءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِTo, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?0 Views
- فَإِذَا انشَقَّتِ السَّمَاءُ فَكَانَتْ وَرْدَةً كَالدِّهَانِSa'an nan idan sama ta tsãge kuma ta zama jã kamar jar fãta.0 Views
- فَبِأَيِّ آلَاءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِTo, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?0 Views
- فَيَوْمَئِذٍ لَّا يُسْأَلُ عَن ذَنبِهِ إِنسٌ وَلَا جَانٌّTo, a ran nan bã zã a tambayi wani mutum laifinsa ba, kuma haka aljani.0 Views
- فَبِأَيِّ آلَاءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِTo, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?0 Views
- يُعْرَفُ الْمُجْرِمُونَ بِسِيمَاهُمْ فَيُؤْخَذُ بِالنَّوَاصِي وَالْأَقْدَامِzã a iya sanin mãsu laifi da alãmarsu, sabõda haka sai a kãma kwarkaɗarsu da sãwãyensu.0 Views
- فَبِأَيِّ آلَاءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِTo, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?0 Views
- هَـٰذِهِ جَهَنَّمُ الَّتِي يُكَذِّبُ بِهَا الْمُجْرِمُونَWannan Jahannama ce wadda mãsu laifi ke ƙaryatãwa game da ita.0 Views
- يَطُوفُونَ بَيْنَهَا وَبَيْنَ حَمِيمٍ آنٍSunã kẽwaya a tsakaninta da ruwan ɗimi mai tsananin tafasa.0 Views
- فَبِأَيِّ آلَاءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِTo, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?0 Views
- وَلِمَنْ خَافَ مَقَامَ رَبِّهِ جَنَّتَانِKuma wanda ya ji tsõron tsayãwa a gaba ga Ubangijinsa yanã da Aljanna biyu.0 Views
- فَبِأَيِّ آلَاءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِTo, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?0 Views
- ذَوَاتَا أَفْنَانٍMãsu rassan itãce.0 Views
- فَبِأَيِّ آلَاءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِTo, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?0 Views
- فِيهِمَا عَيْنَانِ تَجْرِيَانِA cikinsu akwai marẽmari biyu sunã gudãna.0 Views
- فَبِأَيِّ آلَاءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِTo, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?0 Views
- فِيهِمَا مِن كُلِّ فَاكِهَةٍ زَوْجَانِA cikinsu akwai nau'i biyu daga kõwane 'ya'yan itãcen marmari.0 Views
- فَبِأَيِّ آلَاءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِTo, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?0 Views
- مُتَّكِئِينَ عَلَىٰ فُرُشٍ بَطَائِنُهَا مِنْ إِسْتَبْرَقٍ ۚ وَجَنَى الْجَنَّتَيْنِ دَانٍSunã gincire a kan waɗansu shimfiɗu cikinsu tufãfin alharĩni mai kauri ne kuma nũnannun 'yã'yan itãcen Aljannar biyu kusakusa suke.0 Views
- فَبِأَيِّ آلَاءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِTo, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?0 Views
- فِيهِنَّ قَاصِرَاتُ الطَّرْفِ لَمْ يَطْمِثْهُنَّ إِنسٌ قَبْلَهُمْ وَلَا جَانٌّA cikinsu akwai mãtã mãsu taƙaita ganinsu, wani mutum, gabanin mazajensu bai ɗebe budurcinsu ba kuma haka wani aljani.0 Views
- فَبِأَيِّ آلَاءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِTo, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?0 Views
- كَأَنَّهُنَّ الْيَاقُوتُ وَالْمَرْجَانُKamar dai su yaƙũtu ne da murjãni.0 Views
- فَبِأَيِّ آلَاءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِTo, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?0 Views
- هَلْ جَزَاءُ الْإِحْسَانِ إِلَّا الْإِحْسَانُShin, kyautatãwa nã da wani sakamako? (Ã'aha) fãce kyautatãwa.0 Views
- فَبِأَيِّ آلَاءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِTo, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?0 Views
- وَمِن دُونِهِمَا جَنَّتَانِKuma baicinsu akwai waɗansu gidãjen Aljanna biyu.0 Views
- فَبِأَيِّ آلَاءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِTo, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?0 Views
- مُدْهَامَّتَانِMãsu duhun inuwa.0 Views
- فَبِأَيِّ آلَاءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِTo, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?0 Views
- فِيهِمَا عَيْنَانِ نَضَّاخَتَانِA cikinsu akwai marẽmari biyu masu kwarãrar ruwa.0 Views
- فَبِأَيِّ آلَاءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِTo, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?0 Views
- فِيهِمَا فَاكِهَةٌ وَنَخْلٌ وَرُمَّانٌA cikinsu akwai 'ya'yan itãcen marmari da dabĩno darummãni.0 Views
- فَبِأَيِّ آلَاءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِTo, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?0 Views
- فِيهِنَّ خَيْرَاتٌ حِسَانٌA cikinsu, akwai wasu mãtã mãsu kyaun hãlãye, mãsu kyaun halitta.0 Views
- فَبِأَيِّ آلَاءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِTo, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?0 Views
- حُورٌ مَّقْصُورَاتٌ فِي الْخِيَامِMãsu farin idãnu da baƙinsu waɗanda aka tsare a cikin haimõmi.0 Views
- فَبِأَيِّ آلَاءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِTo, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?0 Views
- لَمْ يَطْمِثْهُنَّ إِنسٌ قَبْلَهُمْ وَلَا جَانٌّWani mutum, gabanin mazajensu bai ɗẽbe budurcinsu ba, kuma haka wani aljani.0 Views
- فَبِأَيِّ آلَاءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِTo, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?0 Views
- مُتَّكِئِينَ عَلَىٰ رَفْرَفٍ خُضْرٍ وَعَبْقَرِيٍّ حِسَانٍSunã gincire a kan wasu matãsai mãsu kõren launi da katĩfun Abkara kyãwãwa.0 Views
- فَبِأَيِّ آلَاءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِTo, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?0 Views
- تَبَارَكَ اسْمُ رَبِّكَ ذِي الْجَلَالِ وَالْإِكْرَامِSũnan Ubangjinka, Mai girman Jalãla da Karimci, ya tsarkaka.0 Views
Surah al-waqiah
Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
- إِذَا وَقَعَتِ الْوَاقِعَةُIdan mai aukuwa ta auku.0 Views
- لَيْسَ لِوَقْعَتِهَا كَاذِبَةٌBãbu wani (rai) mai ƙaryatãwa ga aukuwarta.0 Views
- خَافِضَةٌ رَّافِعَةٌ(Ita) mai ƙasƙantãwa ce, mai ɗaukakãwa.0 Views
- إِذَا رُجَّتِ الْأَرْضُ رَجًّاIdan aka girgiza ƙasã girgizwa.0 Views
- وَبُسَّتِ الْجِبَالُ بَسًّاKuma aka niƙe duwãtsu, niƙẽwa.0 Views
- فَكَانَتْ هَبَاءً مُّنبَثًّاSai suka kasance ƙũra da ake wãtsarwa.0 Views
- وَكُنتُمْ أَزْوَاجًا ثَلَاثَةًKuma kun kasance nau'i uku.0 Views
- فَأَصْحَابُ الْمَيْمَنَةِ مَا أَصْحَابُ الْمَيْمَنَةِWatau mazõwa dãma. Mẽne ne mazõwa dãma?0 Views
- وَأَصْحَابُ الْمَشْأَمَةِ مَا أَصْحَابُ الْمَشْأَمَةِDa mazõwa hagu. Mẽne ne mazõwa hagu?0 Views
- وَالسَّابِقُونَ السَّابِقُونَDa waɗanda suka tsẽre. Sũ wɗanda suka tsẽren nan,0 Views
- أُولَـٰئِكَ الْمُقَرَّبُونَWaɗancan, sũ ne waɗanda aka kusantar.0 Views
- فِي جَنَّاتِ النَّعِيمِA ckin Aljannar ni'ima.0 Views
- ثُلَّةٌ مِّنَ الْأَوَّلِينَJama'a ne daga mutãnen farko.0 Views
- وَقَلِيلٌ مِّنَ الْآخِرِينَDa kaɗan daga mutãnen ƙarshe.0 Views
- عَلَىٰ سُرُرٍ مَّوْضُونَةٍ(Sunã) a kan wasu gadãje sãƙaƙƙuu.0 Views
- مُّتَّكِئِينَ عَلَيْهَا مُتَقَابِلِينَSunã gincire a kansu, sunã mãsu kallon jũna.0 Views
- يَطُوفُ عَلَيْهِمْ وِلْدَانٌ مُّخَلَّدُونَWasu yara samãri na dindindin gẽwaya a kansu.1 Views
- بِأَكْوَابٍ وَأَبَارِيقَ وَكَأْسٍ مِّن مَّعِينٍDa wasu kõfuna da shantula da hinjãlai daga (giya) mai ɓuɓɓuga.1 Views
- لَّا يُصَدَّعُونَ عَنْهَا وَلَا يُنزِفُونَBã a sanya musu cĩwon jirĩ sabõda ita, kuma bã su buguwa.1 Views
- وَفَاكِهَةٍ مِّمَّا يَتَخَيَّرُونَDa wasu 'ya'yan itãcen marmari daga irin waɗanda suke zãɓe.1 Views
- وَلَحْمِ طَيْرٍ مِّمَّا يَشْتَهُونَDa nãman tsuntsãye daga wanda suke ganin sha'awa.1 Views
- وَحُورٌ عِينٌDa wasu mãtã mãsu fararen idanu da girmansu.1 Views
- كَأَمْثَالِ اللُّؤْلُؤِ الْمَكْنُونِKamar misãlan lu'ulu'u wanda aka ɓõye.1 Views
- جَزَاءً بِمَا كَانُوا يَعْمَلُونَA kan sakamakon, dõmin abin da suka kasance sunã aikatãwa.1 Views
- لَا يَسْمَعُونَ فِيهَا لَغْوًا وَلَا تَأْثِيمًاBã su jin wata yãsassar magana a cikinta, kuma bã su jin sun yi laifi.1 Views
- إِلَّا قِيلًا سَلَامًا سَلَامًاSai dai wata magana (mai dãɗi): Salãmun, Salãmun.1 Views
- وَأَصْحَابُ الْيَمِينِ مَا أَصْحَابُ الْيَمِينِDa mazõwa dãma. Mẽne ne mazõwa dãma?1 Views
- فِي سِدْرٍ مَّخْضُودٍ(Sunã) a cikin itãcen magarya maras ƙaya.1 Views
- وَطَلْحٍ مَّنضُودٍDa wata ayaba mai yawan 'ya'ya.1 Views
- وَظِلٍّ مَّمْدُودٍDa wata inuwa mĩƙaƙƙiya.1 Views
- وَمَاءٍ مَّسْكُوبٍDa wani ruwa mai gudãna.1 Views
- وَفَاكِهَةٍ كَثِيرَةٍDa wasu 'ya'yan itacen marmari mãsu yawa.1 Views
- لَّا مَقْطُوعَةٍ وَلَا مَمْنُوعَةٍBã su yankẽwa kuma bã a hana su.1 Views
- وَفُرُشٍ مَّرْفُوعَةٍDa wasu shimfiɗu maɗaukaka.1 Views
- إِنَّا أَنشَأْنَاهُنَّ إِنشَاءًLalle Mũ, Mun ƙãga halittarsu ƙãgãwa.1 Views
- فَجَعَلْنَاهُنَّ أَبْكَارًاSa'an nan Muka sanya su budurwai.1 Views
- عُرُبًا أَتْرَابًاMãsu son mazansu, a cikin tsãrã ɗaya.1 Views
- لِّأَصْحَابِ الْيَمِينِGa mazõwa dãma.1 Views
- ثُلَّةٌ مِّنَ الْأَوَّلِينَWata ƙungiya ce daga mutãnen farko.1 Views
- وَثُلَّةٌ مِّنَ الْآخِرِينَDa wata ƙungiya daga mutãnen ƙarshe.1 Views
- وَأَصْحَابُ الشِّمَالِ مَا أَصْحَابُ الشِّمَالِMazõwa hagu, Mẽne ne mazõwa hagu?1 Views
- فِي سَمُومٍ وَحَمِيمٍSunã a cikin wata iskar zãfi da wani ruwan zãfi.1 Views
- وَظِلٍّ مِّن يَحْمُومٍDa wata inuwa ta hayãƙi mai baƙi.1 Views
- لَّا بَارِدٍ وَلَا كَرِيمٍBã mai sanyi ba, kuma bã mai wata ni'ima ba.1 Views
- إِنَّهُمْ كَانُوا قَبْلَ ذَٰلِكَ مُتْرَفِينَLalle sũ, sun kasance a gabãnin wannan waɗanda aka jiyar dãɗi.1 Views
- وَكَانُوا يُصِرُّونَ عَلَى الْحِنثِ الْعَظِيمِKuma sun kasance sunã dõgẽwa a kan mummũnan zunubi mai girma.1 Views
- وَكَانُوا يَقُولُونَ أَئِذَا مِتْنَا وَكُنَّا تُرَابًا وَعِظَامًا أَإِنَّا لَمَبْعُوثُونَKuma sun kasance sunã cẽwa: "Shin idan mun mutukuma muko kasance turɓãya da ƙasũsuwa shin lalle mũ waɗanda zã a kõma rãyarwa ne haƙĩƙatan?"1 Views
- أَوَآبَاؤُنَا الْأَوَّلُونَ"Shin, kuma da ubanninmu na farko?"1 Views
- قُلْ إِنَّ الْأَوَّلِينَ وَالْآخِرِينَKa ce: "Lalle mutãnen farko da na ƙarshe."1 Views
- لَمَجْمُوعُونَ إِلَىٰ مِيقَاتِ يَوْمٍ مَّعْلُومٍ"Tabbas, waɗanda ake tãrãwa ne a cikin wani yini sananne."1 Views
- ثُمَّ إِنَّكُمْ أَيُّهَا الضَّالُّونَ الْمُكَذِّبُونَ"Sa'an nan lalle ku, ya kũ ɓatattu, mãsu ƙaryatãwa!"0 Views
- لَآكِلُونَ مِن شَجَرٍ مِّن زَقُّومٍ"Lalle mãsu cĩ ne daga wata itãciya ta zaƙƙum (ɗanyen wutã)."0 Views
- فَمَالِئُونَ مِنْهَا الْبُطُونَ"Har za ku zama mãsu cika cikunna daga gare ta."0 Views
- فَشَارِبُونَ عَلَيْهِ مِنَ الْحَمِيمِ"Sa'an nan kuma mãsu shã ne, a kan wannan abin cin, daga ruwan zãfi."0 Views
- فَشَارِبُونَ شُرْبَ الْهِيمِ"Ku zama mãsu shã irin shan rãƙuma mãsu ƙishirwa."0 Views
- هَـٰذَا نُزُلُهُمْ يَوْمَ الدِّينِWannan ita ce liyãfarsu a rãnar sakamako.0 Views
- نَحْنُ خَلَقْنَاكُمْ فَلَوْلَا تُصَدِّقُونَMũ ne Muka halitta ku, to, don me bã zã ku gaskata ba?0 Views
- أَفَرَأَيْتُم مَّا تُمْنُونَShin kuma kun ga abin da kuke fitarwa na maniyyi?0 Views
- أَأَنتُمْ تَخْلُقُونَهُ أَمْ نَحْنُ الْخَالِقُونَShin kũ ne kuke halitta shi, kõ kuwa mũ ne Mãsu halittãwa?0 Views
- نَحْنُ قَدَّرْنَا بَيْنَكُمُ الْمَوْتَ وَمَا نَحْنُ بِمَسْبُوقِينَMũ ne Muka ƙaddara mutuwa a tsakãninku, kuma ba Mu zama Mãsu gajiyãwa ba,0 Views
- عَلَىٰ أَن نُّبَدِّلَ أَمْثَالَكُمْ وَنُنشِئَكُمْ فِي مَا لَا تَعْلَمُونَA kan Mu musanya waɗansu (mutãne) kamarku, kuma Mu mayar da ku a cikin wata halitta da ba ku sani ba.0 Views
- وَلَقَدْ عَلِمْتُمُ النَّشْأَةَ الْأُولَىٰ فَلَوْلَا تَذَكَّرُونَKuma lalle, ne haƙĩƙa, kun san halittar farko, to, don me ba zã ku yi tunãni ba?0 Views
- أَفَرَأَيْتُم مَّا تَحْرُثُونَShin, kuma kun ga abin da kũke nõmãwa?0 Views
- أَأَنتُمْ تَزْرَعُونَهُ أَمْ نَحْنُ الزَّارِعُونَShin, kũ ne ke tsirar da shi kõ kuwa Mũ ne Mãsu tsirarwa?0 Views
- لَوْ نَشَاءُ لَجَعَلْنَاهُ حُطَامًا فَظَلْتُمْ تَفَكَّهُونَDã Munã so lalle, da Mun sanya shi bũsasshiyar ciyãwa, sai ku yini kunã mãmãkin bãƙin ciki.0 Views
- إِنَّا لَمُغْرَمُونَ(Kunã cẽwa) "Lalle haƙĩƙa an azã mana tãra!"0 Views
- بَلْ نَحْنُ مَحْرُومُونَ"Ã'a, mun dai zama waɗanda aka hanã wa!"0 Views
- أَفَرَأَيْتُمُ الْمَاءَ الَّذِي تَشْرَبُونَShin, kuma kun ga ruwa wannan da kuke sha?0 Views
- أَأَنتُمْ أَنزَلْتُمُوهُ مِنَ الْمُزْنِ أَمْ نَحْنُ الْمُنزِلُونَShin, kũ ne kuke saukar da shi daga girgije, kõ kuwa Mũne Mãsu saukarwa?0 Views
- لَوْ نَشَاءُ جَعَلْنَاهُ أُجَاجًا فَلَوْلَا تَشْكُرُونَDã Mun so, dã Mun mayar da shi ruwan zartsi. To don me bã ku gõdẽwa?0 Views
- أَفَرَأَيْتُمُ النَّارَ الَّتِي تُورُونَShin, kuma kun ga wutã wannan da kuke ƙyastãwa?0 Views
- أَأَنتُمْ أَنشَأْتُمْ شَجَرَتَهَا أَمْ نَحْنُ الْمُنشِئُونَShin, kũ ne kuke ƙagã halittar itãciyarta, kõ kuwa Mũ ne Mãsu ƙãgãwa?0 Views
- نَحْنُ جَعَلْنَاهَا تَذْكِرَةً وَمَتَاعًا لِّلْمُقْوِينَMũ ne Muka sanya ta wata abar wa'azi da jin dãɗi ga matafiya a cikin jẽji.0 Views
- فَسَبِّحْ بِاسْمِ رَبِّكَ الْعَظِيمِSai ka tsarkake sũnan Ubangijinka Mai girma.0 Views
- ۞ فَلَا أُقْسِمُ بِمَوَاقِعِ النُّجُومِTo, bã sai Na yi rantsuwa ba da lõkutan fãɗuwar taurãri.0 Views
- وَإِنَّهُ لَقَسَمٌ لَّوْ تَعْلَمُونَ عَظِيمٌKuma lalle ne' haƙĩƙa, rantsuwa ce mai girma, dã kun sani.0 Views
- إِنَّهُ لَقُرْآنٌ كَرِيمٌLalle shi (wannan littãfi), haƙĩƙa, abin karantãwa ne mai daraja.0 Views
- فِي كِتَابٍ مَّكْنُونٍA cikin wani littafi tsararre.0 Views
- لَّا يَمَسُّهُ إِلَّا الْمُطَهَّرُونَBãbu mai shãfa shi fãce waɗanda aka tsarkake.0 Views
- تَنزِيلٌ مِّن رَّبِّ الْعَالَمِينَWanda aka saukar ne daga Ubangijin halitta.0 Views
- أَفَبِهَـٰذَا الْحَدِيثِ أَنتُم مُّدْهِنُونَShin, to, wannan lãbãrin ne kuke mãsu wulãkantãwa?0 Views
- وَتَجْعَلُونَ رِزْقَكُمْ أَنَّكُمْ تُكَذِّبُونَKuma kunã sanya arzikinku (game da shi) lalle kũ, ku ƙaryata (shi)?0 Views
- فَلَوْلَا إِذَا بَلَغَتِ الْحُلْقُومَTo, don me idan rai ya kai ga maƙõshi? (Kusa da mutuwa).0 Views
- وَأَنتُمْ حِينَئِذٍ تَنظُرُونَAlhãli kuwa kũ, a lõklcin nan, kunã kallo.0 Views
- وَنَحْنُ أَقْرَبُ إِلَيْهِ مِنكُمْ وَلَـٰكِن لَّا تُبْصِرُونَKuma Mũ ne mafi kusanta gare shi daga gare ku, to, amma kũ bã ku gani.0 Views
- فَلَوْلَا إِن كُنتُمْ غَيْرَ مَدِينِينَTo, don me in dai kun kasance bã waɗanda zã a yi wa sakamako ba?0 Views
- تَرْجِعُونَهَا إِن كُنتُمْ صَادِقِينَKu mayar da shi (cikin jikinsa) har idan kun kasance mãsu gaskiya.0 Views
- فَأَمَّا إِن كَانَ مِنَ الْمُقَرَّبِينَTo, amma idan (mai mutuwar) ya kasance daga makusanta,0 Views
- فَرَوْحٌ وَرَيْحَانٌ وَجَنَّتُ نَعِيمٍSai hũtawa da kyakkyawan abinci da Aljannar ni'ima.0 Views
- وَأَمَّا إِن كَانَ مِنْ أَصْحَابِ الْيَمِينِKuma amma idan ya kasance daga mazõwa dãma,0 Views
- فَسَلَامٌ لَّكَ مِنْ أَصْحَابِ الْيَمِينِSai (a ce masa) aminci ya tabbata a gare ka daga mazõwa dãma.0 Views
- وَأَمَّا إِن كَانَ مِنَ الْمُكَذِّبِينَ الضَّالِّينَKuma amma idan ya kasance daga mãsu ƙaryatãwar, ɓatattun,0 Views
- فَنُزُلٌ مِّنْ حَمِيمٍSai wata liyãfa ta ruwan zãfi.0 Views
- وَتَصْلِيَةُ جَحِيمٍDa ƙõnuwa da Jahĩm,0 Views
- إِنَّ هَـٰذَا لَهُوَ حَقُّ الْيَقِينِLalle wannan, haƙĩƙa, ita ce gaskiya ta yaƙĩni.0 Views
- فَسَبِّحْ بِاسْمِ رَبِّكَ الْعَظِيمِSabõda haka, ka tsarkake sũnan Ubangijinka, Mai karimci.0 Views
Surah al-hadid
Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
- سَبَّحَ لِلَّهِ مَا فِي السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ ۖ وَهُوَ الْعَزِيزُ الْحَكِيمُAbin da ke cikin sammai da ƙasa yã yi tasbĩhi ga Allah. Kuma Shĩ ne Mabuwãyi, Mai hikima.0 Views
- لَهُ مُلْكُ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ ۖ يُحْيِي وَيُمِيتُ ۖ وَهُوَ عَلَىٰ كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌShĩ ne da mulkin sammai da ƙasa: Yanã rãyarwa kuma Yanã kashẽwa, kuma Shĩ Mai ikon yi ne a kan kõme.0 Views
- هُوَ الْأَوَّلُ وَالْآخِرُ وَالظَّاهِرُ وَالْبَاطِنُ ۖ وَهُوَ بِكُلِّ شَيْءٍ عَلِيمٌShĩ ne Na farko, Na ƙarshe, Bayyananne, Bõyayye, kuma Shĩ Masani ne ga dukkan kõme.0 Views
- هُوَ الَّذِي خَلَقَ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضَ فِي سِتَّةِ أَيَّامٍ ثُمَّ اسْتَوَىٰ عَلَى الْعَرْشِ ۚ يَعْلَمُ مَا يَلِجُ فِي الْأَرْضِ وَمَا يَخْرُجُ مِنْهَا وَمَا يَنزِلُ مِنَ السَّمَاءِ وَمَا يَعْرُجُ فِيهَا ۖ وَهُوَ مَعَكُمْ أَيْنَ مَا كُنتُمْ ۚ وَاللَّهُ بِمَا تَعْمَلُونَ بَصِيرٌShĩ ne wanda Ya halitta sammai da ƙasa a cikin wasu kwãnuka shida, sa'an nan Ya daidaitu a kan Al'arshi, Yanã sanin abin da ke shiga cikin ƙasa da abin da ke fita daga gare ta, da abin da ke sauka daga sama da abin da ke hawa cikinta, kuma Shĩ yanã tareda ku duk inda kuka kasance. Kuma Allah Mai gani ne ga abin da kuke aikatãwa.0 Views
- لَّهُ مُلْكُ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ ۚ وَإِلَى اللَّهِ تُرْجَعُ الْأُمُورُShĩ ne da mulkin sammai da ƙasa, kuma zuwa gare Shĩ (Allah) kawai ake mayar da al'amura.0 Views
- يُولِجُ اللَّيْلَ فِي النَّهَارِ وَيُولِجُ النَّهَارَ فِي اللَّيْلِ ۚ وَهُوَ عَلِيمٌ بِذَاتِ الصُّدُورِYanã shigar da dare a cikin yini, kuma Yanã shigar da yini a cikin dare, kuma Shi Masani ne ga abin da yake a cikin ƙirãza.0 Views
- آمِنُوا بِاللَّهِ وَرَسُولِهِ وَأَنفِقُوا مِمَّا جَعَلَكُم مُّسْتَخْلَفِينَ فِيهِ ۖ فَالَّذِينَ آمَنُوا مِنكُمْ وَأَنفَقُوا لَهُمْ أَجْرٌ كَبِيرٌKu yi ĩmãni da Allah da ManzonSa, kuma ku ciyar daga abin da Allah Ya wakilta ku a cikinsa (na dũkiya). To, waɗannan da suka yi ĩmãni daga cikinku, kuma suka ciyar, sunã da wani sakamako mai girma.0 Views
- وَمَا لَكُمْ لَا تُؤْمِنُونَ بِاللَّهِ ۙ وَالرَّسُولُ يَدْعُوكُمْ لِتُؤْمِنُوا بِرَبِّكُمْ وَقَدْ أَخَذَ مِيثَاقَكُمْ إِن كُنتُم مُّؤْمِنِينَkuma me ya same ku, bã zã ku yi ĩmãni ba da Allah, alhãli kuwa manzonSa na kiran ku dõmin ku yi ĩmãni da Ubangijinku, kuma lalle Allah Ya karɓi alkawarinku (cẽwa zã ku bauta Masa)? (Ku bauta Masa) idan kun kasance mãsu ĩmãni.0 Views
- هُوَ الَّذِي يُنَزِّلُ عَلَىٰ عَبْدِهِ آيَاتٍ بَيِّنَاتٍ لِّيُخْرِجَكُم مِّنَ الظُّلُمَاتِ إِلَى النُّورِ ۚ وَإِنَّ اللَّهَ بِكُمْ لَرَءُوفٌ رَّحِيمٌShĩ ne wanda ke sassaukar da ãyõyi bayyanannu ga BãwanSa, dõmin Ya fitar da ku daga duffai zuwa ga haske, kuma lalle Allah haƙĩƙa Mai tausayi ne gare ku, Mai jin ƙai.0 Views
- وَمَا لَكُمْ أَلَّا تُنفِقُوا فِي سَبِيلِ اللَّهِ وَلِلَّهِ مِيرَاثُ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ ۚ لَا يَسْتَوِي مِنكُم مَّنْ أَنفَقَ مِن قَبْلِ الْفَتْحِ وَقَاتَلَ ۚ أُولَـٰئِكَ أَعْظَمُ دَرَجَةً مِّنَ الَّذِينَ أَنفَقُوا مِن بَعْدُ وَقَاتَلُوا ۚ وَكُلًّا وَعَدَ اللَّهُ الْحُسْنَىٰ ۚ وَاللَّهُ بِمَا تَعْمَلُونَ خَبِيرٌKuma me ya sãme ku, bã zã ku ciyar ba dõmin ɗaukaka kalmar Allah, alhãli kuwa gãdon sammai da ƙasã na Allah ne? Wanda ya ciyar a gabãnin cin nasara, kuma ya yi yãƙi daga cikinku, bã ya zama daidai (da wanda bai yi haka ba). waɗancan ne mafĩfĩta girman daraja bisa ga waɗanda suka ciyar daga bãya kuma suka yi yãƙi. Kuma dukansu Allah Ya yi musu wa'adi da (sakamako) mai kyau, kuma Allah Masani ne ga abin da kuke aikatãwa.0 Views
- مَّن ذَا الَّذِي يُقْرِضُ اللَّهَ قَرْضًا حَسَنًا فَيُضَاعِفَهُ لَهُ وَلَهُ أَجْرٌ كَرِيمٌWãne ne wanda zai ranta wa Allah rance mai kyau dõmin Allah Ya ninka masa shi (a dũniya) kuma Yanã da wani sakamako na karimci (a Lãhira)?0 Views
- يَوْمَ تَرَى الْمُؤْمِنِينَ وَالْمُؤْمِنَاتِ يَسْعَىٰ نُورُهُم بَيْنَ أَيْدِيهِمْ وَبِأَيْمَانِهِم بُشْرَاكُمُ الْيَوْمَ جَنَّاتٌ تَجْرِي مِن تَحْتِهَا الْأَنْهَارُ خَالِدِينَ فِيهَا ۚ ذَٰلِكَ هُوَ الْفَوْزُ الْعَظِيمُRãnar da zã ka ga mũminai maza da mũminai mãtã haskensu nã tafiya a gaba gare su, da kuma dãma gare su. (Anã ce musu) "Bushãrarku a yau, ita ce gidajen Aljanna." Ruwa na gudãna daga ƙarƙashinsu sunã mãsu dawwama a cikinsu. Wannan, shĩ ne babban rabo mai girma.0 Views
- يَوْمَ يَقُولُ الْمُنَافِقُونَ وَالْمُنَافِقَاتُ لِلَّذِينَ آمَنُوا انظُرُونَا نَقْتَبِسْ مِن نُّورِكُمْ قِيلَ ارْجِعُوا وَرَاءَكُمْ فَالْتَمِسُوا نُورًا فَضُرِبَ بَيْنَهُم بِسُورٍ لَّهُ بَابٌ بَاطِنُهُ فِيهِ الرَّحْمَةُ وَظَاهِرُهُ مِن قِبَلِهِ الْعَذَابُRãnar da munafikai maza da munãfikai mãtã ke cẽwa waɗanda suka yi ĩmãni: "Ku dũbẽ mu, mu yi makãmashi daga haskenku!" A ce (musu): "Ku kõma a bãyanku, dõmin ku nẽmo wani haske." Sai a danne a tsakãninsu da wani gãru yanã da wani ƙyaure, a cikinsa nan rahama take, kuma a bãyansa daga wajensa azaba take.0 Views
- يُنَادُونَهُمْ أَلَمْ نَكُن مَّعَكُمْ ۖ قَالُوا بَلَىٰ وَلَـٰكِنَّكُمْ فَتَنتُمْ أَنفُسَكُمْ وَتَرَبَّصْتُمْ وَارْتَبْتُمْ وَغَرَّتْكُمُ الْأَمَانِيُّ حَتَّىٰ جَاءَ أَمْرُ اللَّهِ وَغَرَّكُم بِاللَّهِ الْغَرُورُSunã kiran su, "Ashe, bã tãre muke da ku ba?" Su ce: "Ĩ, amma kũ, kun fitini kanku, kuma kun yi jiran wata masĩfa, kuma kunyi shakka, kuma waɗansu gũrace-gũrace sun rũɗe ku, har umurnin Allah ya jẽ muku, kumamarũɗi ya rũɗe ku game da Allah."0 Views
- فَالْيَوْمَ لَا يُؤْخَذُ مِنكُمْ فِدْيَةٌ وَلَا مِنَ الَّذِينَ كَفَرُوا ۚ مَأْوَاكُمُ النَّارُ ۖ هِيَ مَوْلَاكُمْ ۖ وَبِئْسَ الْمَصِيرُ"To, a yau bã zã a karɓi fansa daga gare ku ba. Kuma bã zã a karɓa daga waɗanda suka kãfirta ba. Makõmarku wutã ce, ita ce mai dacẽwa da ku, kuma makõmarku ɗin nan tã mũnana."0 Views
- ۞ أَلَمْ يَأْنِ لِلَّذِينَ آمَنُوا أَن تَخْشَعَ قُلُوبُهُمْ لِذِكْرِ اللَّهِ وَمَا نَزَلَ مِنَ الْحَقِّ وَلَا يَكُونُوا كَالَّذِينَ أُوتُوا الْكِتَابَ مِن قَبْلُ فَطَالَ عَلَيْهِمُ الْأَمَدُ فَقَسَتْ قُلُوبُهُمْ ۖ وَكَثِيرٌ مِّنْهُمْ فَاسِقُونَShin, lõkaci bai yi ba ga wa ɗanda suka yi ĩmãnĩ zukãtansu su yi tawãlu'i ga ambaton Allah da abin da ya sauka daga gaskiya? Kada su kasance kamar waɗanda aka bai wa littãfi a gabãnin haka, sai zãmani ya yi tsawo a kansu, sabõda haka zukãtansu suka ƙẽƙashe, kuma masu yawa daga cikinsu fãsiƙai ne.0 Views
- اعْلَمُوا أَنَّ اللَّهَ يُحْيِي الْأَرْضَ بَعْدَ مَوْتِهَا ۚ قَدْ بَيَّنَّا لَكُمُ الْآيَاتِ لَعَلَّكُمْ تَعْقِلُونَKu sani cẽwa Allah Yanã rãyar da ƙasã a bãyan mutuwarta. Lalle Mun bayyanamuku ãyõyi da fatan zã ku yi hankali.0 Views
- إِنَّ الْمُصَّدِّقِينَ وَالْمُصَّدِّقَاتِ وَأَقْرَضُوا اللَّهَ قَرْضًا حَسَنًا يُضَاعَفُ لَهُمْ وَلَهُمْ أَجْرٌ كَرِيمٌLalle mãsu gaskatãwa maza da mãsu gaskatãwa mãtã, kuma suka ranta wa Allah rance mai kyau, anã riɓanya musu, kuma suna da wani sakamako na karimci.0 Views
- وَالَّذِينَ آمَنُوا بِاللَّهِ وَرُسُلِهِ أُولَـٰئِكَ هُمُ الصِّدِّيقُونَ ۖ وَالشُّهَدَاءُ عِندَ رَبِّهِمْ لَهُمْ أَجْرُهُمْ وَنُورُهُمْ ۖ وَالَّذِينَ كَفَرُوا وَكَذَّبُوا بِآيَاتِنَا أُولَـٰئِكَ أَصْحَابُ الْجَحِيمِKuma waɗanda suka yi ĩmãni da Allah da MazanninSa waɗannan sũ ne kamãlar gaskatãwa kuma su ne mãsu shahãda awurin Ubangjinsu. sunã da sakamakonsu da haskensu. waɗanda suka kafirta kuma suka ƙaryata game da ãyõyinMu, waɗannan su ne'yan Jahĩm.0 Views
- اعْلَمُوا أَنَّمَا الْحَيَاةُ الدُّنْيَا لَعِبٌ وَلَهْوٌ وَزِينَةٌ وَتَفَاخُرٌ بَيْنَكُمْ وَتَكَاثُرٌ فِي الْأَمْوَالِ وَالْأَوْلَادِ ۖ كَمَثَلِ غَيْثٍ أَعْجَبَ الْكُفَّارَ نَبَاتُهُ ثُمَّ يَهِيجُ فَتَرَاهُ مُصْفَرًّا ثُمَّ يَكُونُ حُطَامًا ۖ وَفِي الْآخِرَةِ عَذَابٌ شَدِيدٌ وَمَغْفِرَةٌ مِّنَ اللَّهِ وَرِضْوَانٌ ۚ وَمَا الْحَيَاةُ الدُّنْيَا إِلَّا مَتَاعُ الْغُرُورِKu sani cẽwa rãyuwar dũniya wãsã ɗai ce da shagala da ƙawa da alafahri a tsakãninku da gãsar wadãta ta dũkiya da ɗiya, kamar misãlin shũka wadda yabanyarta ta bãyar da sha'awa ga manõma, sa'an nan ta ƙẽƙashe, har ka ganta tã zama rawaya sa'an nan ta kõma rauno. Kuma, alãmra akwai azãba mai tsanani da gãfara daga Allah da yarda. Kuma rãyuwar dũniya ba ta zama ba fãce ɗan jin dãɗin rũɗi kawai.0 Views
- سَابِقُوا إِلَىٰ مَغْفِرَةٍ مِّن رَّبِّكُمْ وَجَنَّةٍ عَرْضُهَا كَعَرْضِ السَّمَاءِ وَالْأَرْضِ أُعِدَّتْ لِلَّذِينَ آمَنُوا بِاللَّهِ وَرُسُلِهِ ۚ ذَٰلِكَ فَضْلُ اللَّهِ يُؤْتِيهِ مَن يَشَاءُ ۚ وَاللَّهُ ذُو الْفَضْلِ الْعَظِيمِKu yi tsẽre zuwa ga (nẽman) gãfara daga Ubangjinku, da Aljanna fãɗinta kamar fãɗin samã da ƙasã ne, an yi tattalinta dõmin waɗanda suka yi ĩmãni da Allah da ManzanninSa. Wannan falalar Allah ce, Yanã bãyar da ita ga wanda Ya so. Kuma Allah Mai falala ne Mai girma.0 Views
- مَا أَصَابَ مِن مُّصِيبَةٍ فِي الْأَرْضِ وَلَا فِي أَنفُسِكُمْ إِلَّا فِي كِتَابٍ مِّن قَبْلِ أَن نَّبْرَأَهَا ۚ إِنَّ ذَٰلِكَ عَلَى اللَّهِ يَسِيرٌWata masifa bã zã ta auku ba a cikin ƙasã kõ a cikin rayukanku fãce tanã a cikin littãfi a gabãnin Mu halitta ta. Lalle wannan, ga Allah, mai sauƙi ne.0 Views
- لِّكَيْلَا تَأْسَوْا عَلَىٰ مَا فَاتَكُمْ وَلَا تَفْرَحُوا بِمَا آتَاكُمْ ۗ وَاللَّهُ لَا يُحِبُّ كُلَّ مُخْتَالٍ فَخُورٍDõmin kada ku yi baƙin ciki a kan abin da ya kuɓuce muku, kuma kada ku yi mumar alfahari da abin da Ya bã ku. Kuma Allah bã Ya son dukkan mai tãƙama, mai alfahari.0 Views
- الَّذِينَ يَبْخَلُونَ وَيَأْمُرُونَ النَّاسَ بِالْبُخْلِ ۗ وَمَن يَتَوَلَّ فَإِنَّ اللَّهَ هُوَ الْغَنِيُّ الْحَمِيدُWatau, waɗanda ke yin rõwa, kuma sunã umumin mutãne da yin rõwa. Kuma wanda ya jũya bãya, to, lalle Allah, Shĩ ne kaɗai Mawadãci, Gõdadde.0 Views
- لَقَدْ أَرْسَلْنَا رُسُلَنَا بِالْبَيِّنَاتِ وَأَنزَلْنَا مَعَهُمُ الْكِتَابَ وَالْمِيزَانَ لِيَقُومَ النَّاسُ بِالْقِسْطِ ۖ وَأَنزَلْنَا الْحَدِيدَ فِيهِ بَأْسٌ شَدِيدٌ وَمَنَافِعُ لِلنَّاسِ وَلِيَعْلَمَ اللَّهُ مَن يَنصُرُهُ وَرُسُلَهُ بِالْغَيْبِ ۚ إِنَّ اللَّهَ قَوِيٌّ عَزِيزٌHaƙĩƙa, lalle Mun aiko ManzanninMu da hujjõji bayyanannu, kuma Muka saukar da Littãfi da sikẽli tãre da su dõmin mutãne su tsayu da ãdalci, kuma Mun saukar da baƙin ƙarfe, a cikinsa akwai cutarwa mai tsanani da amfãni ga mutãne, kuma dõmin Allah Ya san mai taimakonSa da ManzanninSa a fake. Lalle ne Allah Mai ƙarfi ne, Mabuwãyi.0 Views
- وَلَقَدْ أَرْسَلْنَا نُوحًا وَإِبْرَاهِيمَ وَجَعَلْنَا فِي ذُرِّيَّتِهِمَا النُّبُوَّةَ وَالْكِتَابَ ۖ فَمِنْهُم مُّهْتَدٍ ۖ وَكَثِيرٌ مِّنْهُمْ فَاسِقُونَKuma haƙĩƙa, lalle, Mun aiki Nũhu da Ibrahĩm, kuma Muka sanya Annabci da Littĩfi a cikin zuriyarsu; daga cikinsu akwai mai nẽman shiryuwa, kuma mãsu yawa daga cikinsu fasiƙai ne.0 Views
- ثُمَّ قَفَّيْنَا عَلَىٰ آثَارِهِم بِرُسُلِنَا وَقَفَّيْنَا بِعِيسَى ابْنِ مَرْيَمَ وَآتَيْنَاهُ الْإِنجِيلَ وَجَعَلْنَا فِي قُلُوبِ الَّذِينَ اتَّبَعُوهُ رَأْفَةً وَرَحْمَةً وَرَهْبَانِيَّةً ابْتَدَعُوهَا مَا كَتَبْنَاهَا عَلَيْهِمْ إِلَّا ابْتِغَاءَ رِضْوَانِ اللَّهِ فَمَا رَعَوْهَا حَقَّ رِعَايَتِهَا ۖ فَآتَيْنَا الَّذِينَ آمَنُوا مِنْهُمْ أَجْرَهُمْ ۖ وَكَثِيرٌ مِّنْهُمْ فَاسِقُونَSa'an nan Muka biyar a bãyansu da ManzanninMu; kuma Muka biyar da ĩsã ɗan Maryama, kuma Muka ba shi Linjila kuma Muka sanya tausayi da rahama a cikin zukãtan waɗanda suka bĩ shi, da ruhbãnanci wanda suka ƙãga, shi, ba Mu rubũta shi ba a kansu, fãce dai (Mun rubũta musu nẽman yardar Allah, sa'an nan ba su tsare shi haƙƙin tsarẽwarsa ba, sabõda haka Muka bai wa waɗanda suka yi ĩmãni daga cikinsu sakamakonsu kuma mãsu yawa daga cikinsu fãsiƙai ne.0 Views
- يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا اتَّقُوا اللَّهَ وَآمِنُوا بِرَسُولِهِ يُؤْتِكُمْ كِفْلَيْنِ مِن رَّحْمَتِهِ وَيَجْعَل لَّكُمْ نُورًا تَمْشُونَ بِهِ وَيَغْفِرْ لَكُمْ ۚ وَاللَّهُ غَفُورٌ رَّحِيمٌYã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku bi Allah da taƙawa, ku yi ĩmãni da ManzonSa Ya bã ku rabo biyu daga rahamarSa, kuma Ya sanya muku wani haske wanda kuke yin tafiya da shi, kuma Ya gãfarta muku. Kuma Allah Mai gãfara ne, Mai rahama.0 Views
- لِّئَلَّا يَعْلَمَ أَهْلُ الْكِتَابِ أَلَّا يَقْدِرُونَ عَلَىٰ شَيْءٍ مِّن فَضْلِ اللَّهِ ۙ وَأَنَّ الْفَضْلَ بِيَدِ اللَّهِ يُؤْتِيهِ مَن يَشَاءُ ۚ وَاللَّهُ ذُو الْفَضْلِ الْعَظِيمِDõmin kada mutãnen Littãfi su san cẽwa lalle bã su da ikon yi ga kõme na falalar Allah, kuma ita falalar ga hannun Allah kawai take, Yanã bãyar da ita ga wanda Ya so (wannan jãhilci yã hana su ĩmani). Kuma Al1ah Mai falala ne mai girma.0 Views