Mushaf Page 536
صفحة ٥٣٦
- Ghunnah
- Qalqalah
- Ikhfa (Haqiqi)
- Ikhfa Shafawi
- Idgham with Ghunnah
- Idgham without Ghunnah
- Idgham Shafawi (Mimi)
- Madd Lazim (6 counts)
- Madd Wajib Muttasil (4-5 counts)
- Madd Jaiz Munfasil (2, 4, 6 counts)
Each word’s meaning appears right below it; the transliteration follows below the words.
Surah al-waqiah
- ثُمَّ إِنَّكُمْ أَيُّهَا الضَّالُّونَ الْمُكَذِّبُونَ"Sa'an nan lalle ku, ya kũ ɓatattu, mãsu ƙaryatãwa!"0 Views
- لَآكِلُونَ مِن شَجَرٍ مِّن زَقُّومٍ"Lalle mãsu cĩ ne daga wata itãciya ta zaƙƙum (ɗanyen wutã)."0 Views
- فَمَالِئُونَ مِنْهَا الْبُطُونَ"Har za ku zama mãsu cika cikunna daga gare ta."0 Views
- فَشَارِبُونَ عَلَيْهِ مِنَ الْحَمِيمِ"Sa'an nan kuma mãsu shã ne, a kan wannan abin cin, daga ruwan zãfi."0 Views
- فَشَارِبُونَ شُرْبَ الْهِيمِ"Ku zama mãsu shã irin shan rãƙuma mãsu ƙishirwa."0 Views
- هَـٰذَا نُزُلُهُمْ يَوْمَ الدِّينِWannan ita ce liyãfarsu a rãnar sakamako.0 Views
- نَحْنُ خَلَقْنَاكُمْ فَلَوْلَا تُصَدِّقُونَMũ ne Muka halitta ku, to, don me bã zã ku gaskata ba?0 Views
- أَفَرَأَيْتُم مَّا تُمْنُونَShin kuma kun ga abin da kuke fitarwa na maniyyi?0 Views
- أَأَنتُمْ تَخْلُقُونَهُ أَمْ نَحْنُ الْخَالِقُونَShin kũ ne kuke halitta shi, kõ kuwa mũ ne Mãsu halittãwa?0 Views
- نَحْنُ قَدَّرْنَا بَيْنَكُمُ الْمَوْتَ وَمَا نَحْنُ بِمَسْبُوقِينَMũ ne Muka ƙaddara mutuwa a tsakãninku, kuma ba Mu zama Mãsu gajiyãwa ba,0 Views
- عَلَىٰ أَن نُّبَدِّلَ أَمْثَالَكُمْ وَنُنشِئَكُمْ فِي مَا لَا تَعْلَمُونَA kan Mu musanya waɗansu (mutãne) kamarku, kuma Mu mayar da ku a cikin wata halitta da ba ku sani ba.0 Views
- وَلَقَدْ عَلِمْتُمُ النَّشْأَةَ الْأُولَىٰ فَلَوْلَا تَذَكَّرُونَKuma lalle, ne haƙĩƙa, kun san halittar farko, to, don me ba zã ku yi tunãni ba?0 Views
- أَفَرَأَيْتُم مَّا تَحْرُثُونَShin, kuma kun ga abin da kũke nõmãwa?0 Views
- أَأَنتُمْ تَزْرَعُونَهُ أَمْ نَحْنُ الزَّارِعُونَShin, kũ ne ke tsirar da shi kõ kuwa Mũ ne Mãsu tsirarwa?0 Views
- لَوْ نَشَاءُ لَجَعَلْنَاهُ حُطَامًا فَظَلْتُمْ تَفَكَّهُونَDã Munã so lalle, da Mun sanya shi bũsasshiyar ciyãwa, sai ku yini kunã mãmãkin bãƙin ciki.0 Views
- إِنَّا لَمُغْرَمُونَ(Kunã cẽwa) "Lalle haƙĩƙa an azã mana tãra!"0 Views
- بَلْ نَحْنُ مَحْرُومُونَ"Ã'a, mun dai zama waɗanda aka hanã wa!"0 Views
- أَفَرَأَيْتُمُ الْمَاءَ الَّذِي تَشْرَبُونَShin, kuma kun ga ruwa wannan da kuke sha?0 Views
- أَأَنتُمْ أَنزَلْتُمُوهُ مِنَ الْمُزْنِ أَمْ نَحْنُ الْمُنزِلُونَShin, kũ ne kuke saukar da shi daga girgije, kõ kuwa Mũne Mãsu saukarwa?0 Views
- لَوْ نَشَاءُ جَعَلْنَاهُ أُجَاجًا فَلَوْلَا تَشْكُرُونَDã Mun so, dã Mun mayar da shi ruwan zartsi. To don me bã ku gõdẽwa?0 Views
- أَفَرَأَيْتُمُ النَّارَ الَّتِي تُورُونَShin, kuma kun ga wutã wannan da kuke ƙyastãwa?0 Views
- أَأَنتُمْ أَنشَأْتُمْ شَجَرَتَهَا أَمْ نَحْنُ الْمُنشِئُونَShin, kũ ne kuke ƙagã halittar itãciyarta, kõ kuwa Mũ ne Mãsu ƙãgãwa?0 Views
- نَحْنُ جَعَلْنَاهَا تَذْكِرَةً وَمَتَاعًا لِّلْمُقْوِينَMũ ne Muka sanya ta wata abar wa'azi da jin dãɗi ga matafiya a cikin jẽji.0 Views
- فَسَبِّحْ بِاسْمِ رَبِّكَ الْعَظِيمِSai ka tsarkake sũnan Ubangijinka Mai girma.0 Views
- ۞ فَلَا أُقْسِمُ بِمَوَاقِعِ النُّجُومِTo, bã sai Na yi rantsuwa ba da lõkutan fãɗuwar taurãri.0 Views
- وَإِنَّهُ لَقَسَمٌ لَّوْ تَعْلَمُونَ عَظِيمٌKuma lalle ne' haƙĩƙa, rantsuwa ce mai girma, dã kun sani.0 Views