Mushaf Page 264
صفحة ٢٦٤
- Ghunnah
- Qalqalah
- Ikhfa (Haqiqi)
- Ikhfa Shafawi
- Idgham with Ghunnah
- Idgham without Ghunnah
- Idgham Shafawi (Mimi)
- Madd Lazim (6 counts)
- Madd Wajib Muttasil (4-5 counts)
- Madd Jaiz Munfasil (2, 4, 6 counts)
Each word’s meaning appears right below it; the transliteration follows below the words.
Surah al-hijr
- قَالَ يَا إِبْلِيسُ مَا لَكَ أَلَّا تَكُونَ مَعَ السَّاجِدِينَYa ce: "Yã Iblĩs mẽne ne a gare ka, ba ka kasance tãre da mãsu yin sujuda ba?"2 Views
- قَالَ لَمْ أَكُن لِّأَسْجُدَ لِبَشَرٍ خَلَقْتَهُ مِن صَلْصَالٍ مِّنْ حَمَإٍ مَّسْنُونٍYa ce: "Ban kasance inã yin sujada ba ga mutum wanda Ka halicce shi daga bũsasshen yumɓun lãka wadda ta canja."2 Views
- قَالَ فَاخْرُجْ مِنْهَا فَإِنَّكَ رَجِيمٌYa ce: "To, ka fita daga gare ta, dõmin lalle kai abin jĩfa ne."2 Views
- وَإِنَّ عَلَيْكَ اللَّعْنَةَ إِلَىٰ يَوْمِ الدِّينِ"Kuma lalle ne akwai la'ana a kanka har ya zuwa rãnar sakamako."2 Views
- قَالَ رَبِّ فَأَنظِرْنِي إِلَىٰ يَوْمِ يُبْعَثُونَYa ce: "Yã Ubangjĩna! Sai Ka yi mini jinkiri zuwa rãnar da ake tãshin su."2 Views
- قَالَ فَإِنَّكَ مِنَ الْمُنظَرِينَYa ce: "To, lalle ne kanã daga waɗanda ake yi wa jinkiri."2 Views
- إِلَىٰ يَوْمِ الْوَقْتِ الْمَعْلُومِ"Zuwa ga Yinin Lõkacin nan sananne."2 Views
- قَالَ رَبِّ بِمَا أَغْوَيْتَنِي لَأُزَيِّنَنَّ لَهُمْ فِي الْأَرْضِ وَلَأُغْوِيَنَّهُمْ أَجْمَعِينَYa ce: "Yã Ubangijina! Inã rantsuwa da abin da Ka ɓatar da ni da shi, haƙĩƙa inã ƙawãta musu (rãyuwa) a cikin ƙasã kuma haƙĩƙa inã ɓatar da su gabã ɗaya."2 Views
- إِلَّا عِبَادَكَ مِنْهُمُ الْمُخْلَصِينَ"Fãce bãyinKa daga gare su, waɗanda Ka tsarkake."2 Views
- قَالَ هَـٰذَا صِرَاطٌ عَلَيَّ مُسْتَقِيمٌYa ce: "Wannan tafarki ne a gare Ni, madaidaici."2 Views
- إِنَّ عِبَادِي لَيْسَ لَكَ عَلَيْهِمْ سُلْطَانٌ إِلَّا مَنِ اتَّبَعَكَ مِنَ الْغَاوِينَ"Lalle ne bãyĩNa, bã ka da ĩkõ a kansu, fãce wanda ya bĩ ka daga ɓatattu."2 Views
- وَإِنَّ جَهَنَّمَ لَمَوْعِدُهُمْ أَجْمَعِينَKuma lalle Jahannama ce haƙĩƙa, ma'a1kawartarsu gabã ɗaya.2 Views
- لَهَا سَبْعَةُ أَبْوَابٍ لِّكُلِّ بَابٍ مِّنْهُمْ جُزْءٌ مَّقْسُومٌTanã da ƙõfõfi bakwai, ga kõwace ƙõfa akwai wani juz'i daga gare su rababbe.2 Views
- إِنَّ الْمُتَّقِينَ فِي جَنَّاتٍ وَعُيُونٍLalle mãsu taƙawa sunã a cikin gidãjen Aljanna mai idandunan ruwa.2 Views
- ادْخُلُوهَا بِسَلَامٍ آمِنِينَ"Ku shigẽ ta da aminci, kunã amintattu."2 Views
- وَنَزَعْنَا مَا فِي صُدُورِهِم مِّنْ غِلٍّ إِخْوَانًا عَلَىٰ سُرُرٍ مُّتَقَابِلِينَKuma Muka ɗẽbe abinda ke a cikin zukãtansu na daga ƙullin zũci, suka zama 'yan'uwa a kan gadãje, sunã mãsu fuskantar junã.2 Views
- لَا يَمَسُّهُمْ فِيهَا نَصَبٌ وَمَا هُم مِّنْهَا بِمُخْرَجِينَWata wahala bã zã ta shãfe su bã a cikinta kuma ba su zama mãsu fita daga, cikinta ba.2 Views
- ۞ نَبِّئْ عِبَادِي أَنِّي أَنَا الْغَفُورُ الرَّحِيمُKa bai wa bãyiNa lãbari cẽwa lalle ne Ni, Mai gãfarane, Mai jin ƙai.2 Views
- وَأَنَّ عَذَابِي هُوَ الْعَذَابُ الْأَلِيمُKuma azãbãTa ita ce azãba mai raɗaɗi.2 Views
- وَنَبِّئْهُمْ عَن ضَيْفِ إِبْرَاهِيمَKuma ka bã su lãbãrin bãƙin Ibrãhĩm.2 Views