Mushaf Page 372
صفحة ٣٧٢
- Ghunnah
- Qalqalah
- Ikhfa (Haqiqi)
- Ikhfa Shafawi
- Idgham with Ghunnah
- Idgham without Ghunnah
- Idgham Shafawi (Mimi)
- Madd Lazim (6 counts)
- Madd Wajib Muttasil (4-5 counts)
- Madd Jaiz Munfasil (2, 4, 6 counts)
Each word’s meaning appears right below it; the transliteration follows below the words.
Surah ash-shuara
- قَالَ وَمَا عِلْمِي بِمَا كَانُوا يَعْمَلُونَYa ce: "Kuma bã ni da sani ga abin da suka kasance sanã aikatãwa."0 Views
- إِنْ حِسَابُهُمْ إِلَّا عَلَىٰ رَبِّي ۖ لَوْ تَشْعُرُونَ"Hisãbinsu bai zama ba fãce ga Ubangijina, dã kunã sansancẽwa."0 Views
- وَمَا أَنَا بِطَارِدِ الْمُؤْمِنِينَ"Ban zama mai kõre mũminai ba."0 Views
- إِنْ أَنَا إِلَّا نَذِيرٌ مُّبِينٌ"Nĩ ba kõwa ba ne sai mai gargaɗi mai bayyanãwa."0 Views
- قَالُوا لَئِن لَّمْ تَنتَهِ يَا نُوحُ لَتَكُونَنَّ مِنَ الْمَرْجُومِينَSuka ce: "Lalle ne, idan ba ka hanu ba, yã Nũhu, (daga maganarka,) haƙĩƙa, kanã kasancẽwa daga waɗanda ake jẽfewa"0 Views
- قَالَ رَبِّ إِنَّ قَوْمِي كَذَّبُونِYa ce: "Yã Ubangijĩna! Lalle ne mutãnena sun ƙaryatã ni."0 Views
- فَافْتَحْ بَيْنِي وَبَيْنَهُمْ فَتْحًا وَنَجِّنِي وَمَن مَّعِيَ مِنَ الْمُؤْمِنِينَ"Sai ka yi hukunci, a tsakãnĩna da tsakãninsu tabbataccen hukanci, kuma ka tsĩrar da ni, da waɗanda suke tãre da ni daga mũminai."0 Views
- فَأَنجَيْنَاهُ وَمَن مَّعَهُ فِي الْفُلْكِ الْمَشْحُونِSai Muka tsĩrar da shi, shi da waɗanda suke tãre da shi, a cikin jirgi wanda aka yi wa lõdi.0 Views
- ثُمَّ أَغْرَقْنَا بَعْدُ الْبَاقِينَSa'an nan Muka nutsar a bãyan haka, da sauran.0 Views
- إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَآيَةً ۖ وَمَا كَانَ أَكْثَرُهُم مُّؤْمِنِينَLalle ne a cikin wannan akwai ãyã, kuma mafi yawansu, ba su kasance mãsu ĩmãni ba.0 Views
- وَإِنَّ رَبَّكَ لَهُوَ الْعَزِيزُ الرَّحِيمُKuma Lalle ne, Ubangijinka, haƙĩƙa, Shĩ ne Mabuwãyi, Mai Rahama.0 Views
- كَذَّبَتْ عَادٌ الْمُرْسَلِينَÃdãwa sun ƙaryata Manzanni.0 Views
- إِذْ قَالَ لَهُمْ أَخُوهُمْ هُودٌ أَلَا تَتَّقُونَA lõkacin da ɗan'uwansu, Hũdu ya ce musu, "Bã zã ku yi taƙawa ba?"0 Views
- إِنِّي لَكُمْ رَسُولٌ أَمِينٌ"Lalle ne ni, zuwa gare ku, haƙĩƙa, Manzo ne, amintacce."0 Views
- فَاتَّقُوا اللَّهَ وَأَطِيعُونِ"Sabõda haka ku bi Allah da taƙawa, kuma ku yi mini ɗã'ã."0 Views
- وَمَا أَسْأَلُكُمْ عَلَيْهِ مِنْ أَجْرٍ ۖ إِنْ أَجْرِيَ إِلَّا عَلَىٰ رَبِّ الْعَالَمِينَ"Kuma bã ni tambayar wata ijãra a kansa. Ijãrãta ba ta zama ba, fãce daga Ubangijin halittu."0 Views
- أَتَبْنُونَ بِكُلِّ رِيعٍ آيَةً تَعْبَثُونَ"Shin, kunã yin ginin sitadiyo a kõwane tsauni ne, kunã yin wãsa?"0 Views
- وَتَتَّخِذُونَ مَصَانِعَ لَعَلَّكُمْ تَخْلُدُونَ"Kuma kunã riƙon matsãrar ruwa, tsammãninku, ku dawwama?"0 Views
- وَإِذَا بَطَشْتُم بَطَشْتُمْ جَبَّارِينَ"Kuma idan kun yi damƙa, sai ku yi damƙar kunã mãsu tanƙwasãwa."0 Views
- فَاتَّقُوا اللَّهَ وَأَطِيعُونِ"To ku bi Allah da taƙawa, kuma ku yi mini ɗã'ã."0 Views
- وَاتَّقُوا الَّذِي أَمَدَّكُم بِمَا تَعْلَمُونَ"Ku ji tsõron wanda Ya taimake ku da abin da kuka sani."0 Views
- أَمَدَّكُم بِأَنْعَامٍ وَبَنِينَ"Ya taimake ku da dabbõbin ni'ima da ɗiya."0 Views
- وَجَنَّاتٍ وَعُيُونٍ"Da gõnaki da marẽmari."0 Views
- إِنِّي أَخَافُ عَلَيْكُمْ عَذَابَ يَوْمٍ عَظِيمٍ"Lalle ne nĩ, inã ji muku tsõron azãbar wani yini mai girma."0 Views
- قَالُوا سَوَاءٌ عَلَيْنَا أَوَعَظْتَ أَمْ لَمْ تَكُن مِّنَ الْوَاعِظِينَSuka ce: "Daidai ne a kanmu: Kã yi wa'azi kõ ba ka kasance daga mãsu wa'azi ba."0 Views