Mushaf Page 374
صفحة ٣٧٤
- Ghunnah
- Qalqalah
- Ikhfa (Haqiqi)
- Ikhfa Shafawi
- Idgham with Ghunnah
- Idgham without Ghunnah
- Idgham Shafawi (Mimi)
- Madd Lazim (6 counts)
- Madd Wajib Muttasil (4-5 counts)
- Madd Jaiz Munfasil (2, 4, 6 counts)
Each word’s meaning appears right below it; the transliteration follows below the words.
Surah ash-shuara
- كَذَّبَتْ قَوْمُ لُوطٍ الْمُرْسَلِينَMutãnen Lũɗu sun ƙaryata Manzanni.0 Views
- إِذْ قَالَ لَهُمْ أَخُوهُمْ لُوطٌ أَلَا تَتَّقُونَA lõkacin da ɗan'uwansu, Lũɗu ya ce musu, "Bã zã ku yi taƙawa ba?"0 Views
- إِنِّي لَكُمْ رَسُولٌ أَمِينٌ"Lalle ne nĩ, zuwa gare ku, Manzõ ne, amintacce."0 Views
- فَاتَّقُوا اللَّهَ وَأَطِيعُونِ"Sabõda haka ku bi Allah da taƙawa, kuma ku yi mini ɗã'ã."0 Views
- وَمَا أَسْأَلُكُمْ عَلَيْهِ مِنْ أَجْرٍ ۖ إِنْ أَجْرِيَ إِلَّا عَلَىٰ رَبِّ الْعَالَمِينَ"Kuma bã ni tambayar ku wata ijãra, Ijãrãta ba ta zama ba fãce daga Ubangijin halittu."0 Views
- أَتَأْتُونَ الذُّكْرَانَ مِنَ الْعَالَمِينَ"Shin kunã jẽ wa maza daga cikin talikai?"0 Views
- وَتَذَرُونَ مَا خَلَقَ لَكُمْ رَبُّكُم مِّنْ أَزْوَاجِكُم ۚ بَلْ أَنتُمْ قَوْمٌ عَادُونَ"Kuma kunã barin abin da Ubangijinku Ya halitta muku daga mãtanku? Ã'a, ku mutãne ne mãsu ƙẽtarẽwa!"0 Views
- قَالُوا لَئِن لَّمْ تَنتَهِ يَا لُوطُ لَتَكُونَنَّ مِنَ الْمُخْرَجِينَSuka ce: "Lalle ne haƙĩƙa idan ba ka hanu ba, yã Lũɗu! Tĩlas ne kanã kasancẽwa daga waɗanda ake fitarwa (daga gari)."0 Views
- قَالَ إِنِّي لِعَمَلِكُم مِّنَ الْقَالِينَYa ce: "Lalle ne ga aikinku, haƙĩƙa, inã daga mãsu ƙinsa."2 Views
- رَبِّ نَجِّنِي وَأَهْلِي مِمَّا يَعْمَلُونَ"Ya Ubangijina! Ka tsĩrar da ni da iyãlĩna daga abin da suke aikatãwa."0 Views
- فَنَجَّيْنَاهُ وَأَهْلَهُ أَجْمَعِينَSabõda haka Muka tsĩrar da shi, Shi da mutãnensa gabã ɗaya.0 Views
- إِلَّا عَجُوزًا فِي الْغَابِرِينَFãce wata tsõhuwa a cikin mãsu wanzuwa.0 Views
- ثُمَّ دَمَّرْنَا الْآخَرِينَSa'an nan kuma Muka darkãke wasu.0 Views
- وَأَمْطَرْنَا عَلَيْهِم مَّطَرًا ۖ فَسَاءَ مَطَرُ الْمُنذَرِينَKuma Muka yi ruwan sama a kansu ruwa, sai dai ruwan waɗanda ake yi wa gargaɗi ya mũnana.0 Views
- إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَآيَةً ۖ وَمَا كَانَ أَكْثَرُهُم مُّؤْمِنِينَLalle ne ga wannan, akwai ãyã, kuma mafi yawansu bã su kasance mãsu ĩmãni ba.0 Views
- وَإِنَّ رَبَّكَ لَهُوَ الْعَزِيزُ الرَّحِيمُKuma lalle ne Ubangijinka, haƙĩƙa, Shĩ ne Mabuwãyi, Mai jin ƙai.0 Views
- كَذَّبَ أَصْحَابُ الْأَيْكَةِ الْمُرْسَلِينَMa'abũta ƙunci sun ƙaryata Manzanni.0 Views
- إِذْ قَالَ لَهُمْ شُعَيْبٌ أَلَا تَتَّقُونَA lõkacin da Shu'aibu ya ce musu, "Bã zã ku yi taƙawa ba?"0 Views
- إِنِّي لَكُمْ رَسُولٌ أَمِينٌ"Lalle ne ni, zuwa gare ku, Manzo ne, amintacce."0 Views
- فَاتَّقُوا اللَّهَ وَأَطِيعُونِ"Sabõda haka ku bi Allah da taƙawa kuma ku yi mini ɗã'ã."0 Views
- وَمَا أَسْأَلُكُمْ عَلَيْهِ مِنْ أَجْرٍ ۖ إِنْ أَجْرِيَ إِلَّا عَلَىٰ رَبِّ الْعَالَمِينَ"Kuma ba ni tambayar ku wata ijãra a kansa. Ijãrata ba ta zama ba fãce daga Ubangijin halittu."0 Views
- ۞ أَوْفُوا الْكَيْلَ وَلَا تَكُونُوا مِنَ الْمُخْسِرِينَ"Ku cika mũdu, kuma kada ku kasance daga mãsu sanyãwar hasãra (ga mutãne)."0 Views
- وَزِنُوا بِالْقِسْطَاسِ الْمُسْتَقِيمِ"Kuma ku yi awo da sikẽli daidaitacce."0 Views
- وَلَا تَبْخَسُوا النَّاسَ أَشْيَاءَهُمْ وَلَا تَعْثَوْا فِي الْأَرْضِ مُفْسِدِينَ"Kuma kada ku nakasa wa mutãne abũbuwansu kuma kada ku yi fasãdi a cikin ƙasa kuna mãsu ɓarna."0 Views