Mushaf Page 449
صفحة ٤٤٩
- Ghunnah
- Qalqalah
- Ikhfa (Haqiqi)
- Ikhfa Shafawi
- Idgham with Ghunnah
- Idgham without Ghunnah
- Idgham Shafawi (Mimi)
- Madd Lazim (6 counts)
- Madd Wajib Muttasil (4-5 counts)
- Madd Jaiz Munfasil (2, 4, 6 counts)
Each word’s meaning appears right below it; the transliteration follows below the words.
Surah as-saffat
- وَجَعَلْنَا ذُرِّيَّتَهُ هُمُ الْبَاقِينَMuka sanya zurriyarsa sunã mãsu wanzuwa.0 Views
- وَتَرَكْنَا عَلَيْهِ فِي الْآخِرِينَKuma Muka bar masa (yabo) a cikin jama'ar ƙarshe.0 Views
- سَلَامٌ عَلَىٰ نُوحٍ فِي الْعَالَمِينَAminci ya tabbata ga Nũhu, a cikin halittu.0 Views
- إِنَّا كَذَٰلِكَ نَجْزِي الْمُحْسِنِينَLalle Mũ kamar haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa.0 Views
- إِنَّهُ مِنْ عِبَادِنَا الْمُؤْمِنِينَLalle shi, yanã daga bãyinMu mũminai.0 Views
- ثُمَّ أَغْرَقْنَا الْآخَرِينَSã'an nan Muka nutsar da waɗansunsu.0 Views
- ۞ وَإِنَّ مِن شِيعَتِهِ لَإِبْرَاهِيمَKuma lalle daga ƙungiyarsa, haƙĩƙa, Ibrahĩm yake.0 Views
- إِذْ جَاءَ رَبَّهُ بِقَلْبٍ سَلِيمٍA lõkacin da ya je wa dangijinsa da zũciya kuɓutacciya.0 Views
- إِذْ قَالَ لِأَبِيهِ وَقَوْمِهِ مَاذَا تَعْبُدُونَA lõkacin da ya ce wa ubansa da mutãnensa, "Mẽne ne kuke bautãwa?"0 Views
- أَئِفْكًا آلِهَةً دُونَ اللَّهِ تُرِيدُونَ"Shin, ƙiren ƙarya (wãtau) gumãka, wanin Allah, kuke bautãwa?"0 Views
- فَمَا ظَنُّكُم بِرَبِّ الْعَالَمِينَ"To, mẽne ne zatonku game da Ubangijin halittu?"0 Views
- فَنَظَرَ نَظْرَةً فِي النُّجُومِSai ya yi dũbi, dũba ta sõsai, a cikin taurãri.0 Views
- فَقَالَ إِنِّي سَقِيمٌSã'an nan ya ce: "Nĩ mai rashin lãfiya ne."0 Views
- فَتَوَلَّوْا عَنْهُ مُدْبِرِينَSai suka jũya ga barinsa, sunã mãsu jũyãwa da bãya.0 Views
- فَرَاغَ إِلَىٰ آلِهَتِهِمْ فَقَالَ أَلَا تَأْكُلُونَSai ya karkata zuwa ga gumãkansu, sa'an nan ya ce: "Ashe bã zã ku ci ba?0 Views
- مَا لَكُمْ لَا تَنطِقُونَ"Me ya sãme ku, bã ku magana?"0 Views
- فَرَاغَ عَلَيْهِمْ ضَرْبًا بِالْيَمِينِSai ya zuba dũka a kansu da hannun dãma.0 Views
- فَأَقْبَلُوا إِلَيْهِ يَزِفُّونَSai suka fuskanto zuwa gare shi, sunã gaggãwa.0 Views
- قَالَ أَتَعْبُدُونَ مَا تَنْحِتُونَYa ce, "Kunã bauta wa abin da kuke sassaƙawa,0 Views
- وَاللَّهُ خَلَقَكُمْ وَمَا تَعْمَلُونَ"Alhãli, Allah ne Ya halitta ku game da abin da kuke aikatãwa?"0 Views
- قَالُوا ابْنُوا لَهُ بُنْيَانًا فَأَلْقُوهُ فِي الْجَحِيمِSuka ce: "Ku gina wani gini sabõda shi, sa'an nan ku jẽfa shi a cikin Jahĩm."0 Views
- فَأَرَادُوا بِهِ كَيْدًا فَجَعَلْنَاهُمُ الْأَسْفَلِينَSabõda haka suka yi nufin makĩda game da shi. Sai Muka sanya su, sũ ne mafi ƙasƙanci.0 Views
- وَقَالَ إِنِّي ذَاهِبٌ إِلَىٰ رَبِّي سَيَهْدِينِKuma (Ibrahĩm] ya ce: "Lalle, nĩ mai tafiya ne zuwa ga Ubangijĩna, zai shiryar da ni."0 Views
- رَبِّ هَبْ لِي مِنَ الصَّالِحِينَ"Ya Ubangijĩna! Ka bã ni (abõkin zama) daga sãlihan mutãne."0 Views
- فَبَشَّرْنَاهُ بِغُلَامٍ حَلِيمٍSai Muka yi masa bushãra da wani yãro mai haƙuri.0 Views
- فَلَمَّا بَلَغَ مَعَهُ السَّعْيَ قَالَ يَا بُنَيَّ إِنِّي أَرَىٰ فِي الْمَنَامِ أَنِّي أَذْبَحُكَ فَانظُرْ مَاذَا تَرَىٰ ۚ قَالَ يَا أَبَتِ افْعَلْ مَا تُؤْمَرُ ۖ سَتَجِدُنِي إِن شَاءَ اللَّهُ مِنَ الصَّابِرِينَTo, a lõkacin da ya isa aiki tãre da shi, ya ce: "Ya ƙaramin ɗãna! Lalle ne inã gani, a ciki barci, lalle inã yanka ka. To, ka dũba mẽ ka gani?" (Yãron) ya ce: "Ya, Bãbãna! Ka aikata abin da aka umurce ka, zã ka sãme ni, in Allah Ya so, daga mãsu haƙuri."0 Views