37. as-saffat
الصافات
Read Surah as-saffat in full: surah 37, 182 verses, Meccan, Juz 23. Arabic text with Hausa translation.
- Ghunnah
- Qalqalah
- Ikhfa (Haqiqi)
- Ikhfa Shafawi
- Idgham with Ghunnah
- Idgham without Ghunnah
- Idgham Shafawi (Mimi)
- Madd Lazim (6 counts)
- Madd Wajib Muttasil (4-5 counts)
- Madd Jaiz Munfasil (2, 4, 6 counts)
Each word’s meaning appears right below it; the transliteration follows below the words.
Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
- وَالصَّافَّاتِ صَفًّاInã rantsuwa da mãsu yin sahu-sahu (a cikin salla kõ yãƙi).0 Views
- فَالزَّاجِرَاتِ زَجْرًاSa'an nan mãsu yin tsãwa dõmin gargaɗi.0 Views
- فَالتَّالِيَاتِ ذِكْرًاSa'an nan da mãsu karãtun abin tunãtarwa.0 Views
- إِنَّ إِلَـٰهَكُمْ لَوَاحِدٌLalle Abin bautawarku haƙĩƙa ¦aya ne.0 Views
- رَّبُّ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ وَمَا بَيْنَهُمَا وَرَبُّ الْمَشَارِقِUbangijin sammai da ƙasã da abin da ke tsakãninsu, kuma Ubangijin wurãren fitar rãnã.0 Views
- إِنَّا زَيَّنَّا السَّمَاءَ الدُّنْيَا بِزِينَةٍ الْكَوَاكِبِLalle Mũ, Mun ƙãwatãr da sama ta kusa da wata ƙawa, watau taurãri.0 Views
- وَحِفْظًا مِّن كُلِّ شَيْطَانٍ مَّارِدٍKuma sunã tsari daga dukan Shaiɗan mai tsaurin kai.0 Views
- لَّا يَسَّمَّعُونَ إِلَى الْمَلَإِ الْأَعْلَىٰ وَيُقْذَفُونَ مِن كُلِّ جَانِبٍBã zã su iya saurãre zuwa ga jama'a mafi ɗaukaka (Malã'iku) ba, kuma anã jĩfar su daga kõwane gẽfe.0 Views
- دُحُورًا ۖ وَلَهُمْ عَذَابٌ وَاصِبٌDõmin tunkuɗẽwa kuma sunã da wata azãba tabbatacciya.0 Views
- إِلَّا مَنْ خَطِفَ الْخَطْفَةَ فَأَتْبَعَهُ شِهَابٌ ثَاقِبٌFãce wanda ya fizgi wata kalma, sai yũla mai haske ta bĩ shi.0 Views
- فَاسْتَفْتِهِمْ أَهُمْ أَشَدُّ خَلْقًا أَم مَّنْ خَلَقْنَا ۚ إِنَّا خَلَقْنَاهُم مِّن طِينٍ لَّازِبٍKa tambaye su: "Shin sũ ne mafi wuya ga halittawa, kõ, kuwa waɗanda Muka halitta?" Lalle Mũ, Mun halitta su daga lãkã mai ɗauri.0 Views
- بَلْ عَجِبْتَ وَيَسْخَرُونَÃ'a, kã yi mãmãki, alhãli kuwa sunã ta yin izgili.0 Views
- وَإِذَا ذُكِّرُوا لَا يَذْكُرُونَKuma idan aka tunãtar da su, bã su tunãwa.0 Views
- وَإِذَا رَأَوْا آيَةً يَسْتَسْخِرُونَIdan suka ga wata ãyã, sai su dinga yin izgili.0 Views
- وَقَالُوا إِنْ هَـٰذَا إِلَّا سِحْرٌ مُّبِينٌKuma su ce, "Wannnan bã kõme ba, fãce sihiri, ne bayyananne."0 Views
- أَإِذَا مِتْنَا وَكُنَّا تُرَابًا وَعِظَامًا أَإِنَّا لَمَبْعُوثُونَ"Shin, idan mun mutu, kuma muka kasance turɓaya da kasũsuwa, ashe, lalle mũ tabbas waɗandaake tãyarwa ne?0 Views
- أَوَآبَاؤُنَا الْأَوَّلُونَ"Ashe kõ da ubanninmu na farko?"0 Views
- قُلْ نَعَمْ وَأَنتُمْ دَاخِرُونَKa ce: "Na'am alhãli kuwa kunã ƙasƙantattu."0 Views
- فَإِنَّمَا هِيَ زَجْرَةٌ وَاحِدَةٌ فَإِذَا هُمْ يَنظُرُونَTsãwa guda kawai ce, sai gã su, sunã dũbi.0 Views
- وَقَالُوا يَا وَيْلَنَا هَـٰذَا يَوْمُ الدِّينِKuma su ce: "Yã bonenmu! Wannan ita ce rãnar sakamako."0 Views
- هَـٰذَا يَوْمُ الْفَصْلِ الَّذِي كُنتُم بِهِ تُكَذِّبُونَWannan ita ce rãnar rarrabẽwa wadda kuka kasance kuna ƙaryatãwa.0 Views
- ۞ احْشُرُوا الَّذِينَ ظَلَمُوا وَأَزْوَاجَهُمْ وَمَا كَانُوا يَعْبُدُونَKu tãra waɗanda suka yi zãlunci, da abõkan haɗinsu, da abin da suka kasance sunã bautãwa.0 Views
- مِن دُونِ اللَّهِ فَاهْدُوهُمْ إِلَىٰ صِرَاطِ الْجَحِيمِWanin Allah, sabõda haka ku shiryar da su zuwa ga hanyar Jahĩm.0 Views
- وَقِفُوهُمْ ۖ إِنَّهُم مَّسْئُولُونَKuma ku tsayar da su, lalle su, waɗanda ake yi wa tambaya ne.0 Views
- مَا لَكُمْ لَا تَنَاصَرُونَMe ya sãme ku, bã ku taimakon jũna?0 Views
- بَلْ هُمُ الْيَوْمَ مُسْتَسْلِمُونَÃ'a, sũ a yau, mãsu sallamãwa ne.0 Views
- وَأَقْبَلَ بَعْضُهُمْ عَلَىٰ بَعْضٍ يَتَسَاءَلُونَKuma sãshensu ya fuskanta ga sãshe, sunã tambayar jũna.0 Views
- قَالُوا إِنَّكُمْ كُنتُمْ تَأْتُونَنَا عَنِ الْيَمِينِSuka ce: "Lalle kũ, kun kasance kunã jẽ mana daga wajen dãma (inda muka amince)."0 Views
- قَالُوا بَل لَّمْ تَكُونُوا مُؤْمِنِينَSuka ce: "Ã'a, ba ku kasance mũminai ba.0 Views
- وَمَا كَانَ لَنَا عَلَيْكُم مِّن سُلْطَانٍ ۖ بَلْ كُنتُمْ قَوْمًا طَاغِينَ"Kuma wani dalĩli bai kasance ba gare mu a kanku. Ã'a, kun kasance mutãne ne mãsu kẽtare iyãka."0 Views
- فَحَقَّ عَلَيْنَا قَوْلُ رَبِّنَا ۖ إِنَّا لَذَائِقُونَ"Sabõda haka maganar Ubangijinmu ta wajaba a kanmu. Lalle mũ, mãsu ɗanɗanãwa ne."0 Views
- فَأَغْوَيْنَاكُمْ إِنَّا كُنَّا غَاوِينَ"Sabõda haka muka ɓatar da ku. Lalle mũ, mun kasance ɓatattu."0 Views
- فَإِنَّهُمْ يَوْمَئِذٍ فِي الْعَذَابِ مُشْتَرِكُونَTo lalle sũ a rãnar nan, mãsu tãrayya ne a cikin azãbar.0 Views
- إِنَّا كَذَٰلِكَ نَفْعَلُ بِالْمُجْرِمِينَLalle Mũ, kamar haka Muke aikatãwa game, da mãsu laifi.0 Views
- إِنَّهُمْ كَانُوا إِذَا قِيلَ لَهُمْ لَا إِلَـٰهَ إِلَّا اللَّهُ يَسْتَكْبِرُونَLalle sũ, sun kasance idan an ce musu: "Bãbu abin bautãwa, fãce Allah," sai su dõra girman kai.0 Views
- وَيَقُولُونَ أَئِنَّا لَتَارِكُو آلِهَتِنَا لِشَاعِرٍ مَّجْنُونٍKuma sunã cẽwa, "Shin, mũ lalle mãsu barin gumãkanmu ne, sabõda maganar wani mawãƙi mahaukaci?0 Views
- بَلْ جَاءَ بِالْحَقِّ وَصَدَّقَ الْمُرْسَلِينَÃ'a, yã zo da gaskiya kuma ya gaskata Manzanni.0 Views
- إِنَّكُمْ لَذَائِقُو الْعَذَابِ الْأَلِيمِLalle kũ, haƙĩƙa mãsu ɗanɗana azãba mai raɗaɗi ne.0 Views
- وَمَا تُجْزَوْنَ إِلَّا مَا كُنتُمْ تَعْمَلُونَKuma bã zã a sãka muku ba fãce da abin da kuka kasance kunã aikatãwa.0 Views
- إِلَّا عِبَادَ اللَّهِ الْمُخْلَصِينَFãce bãyin Allah waɗanda aka tsarkake.0 Views
- أُولَـٰئِكَ لَهُمْ رِزْقٌ مَّعْلُومٌWaɗannan sunã da abinci sananne.0 Views
- فَوَاكِهُ ۖ وَهُم مُّكْرَمُونَ'Ya'yan itãcen marmari, kuma sunã waɗanda ake girmamãwa.0 Views
- فِي جَنَّاتِ النَّعِيمِA cikin gidãjen Aljannar ni'ima.0 Views
- عَلَىٰ سُرُرٍ مُّتَقَابِلِينَA kan karagu, sunã mãsu fuskantar jũna.0 Views
- يُطَافُ عَلَيْهِم بِكَأْسٍ مِّن مَّعِينٍAnã kẽwayãwa a kansu da hinjãlan giya, ta daga waɗansu marẽmari.0 Views
- بَيْضَاءَ لَذَّةٍ لِّلشَّارِبِينَFarã mai dãɗi ga mashãyan.0 Views
- لَا فِيهَا غَوْلٌ وَلَا هُمْ عَنْهَا يُنزَفُونَA cikinta bãbu jirĩ kuma ba su zama mãsu mãye daga gare ta ba,0 Views
- وَعِندَهُمْ قَاصِرَاتُ الطَّرْفِ عِينٌKuma a wurinsu, akwai mãtan aure mãsu taƙaita kallonsu, mãsu manyan idãnu.0 Views
- كَأَنَّهُنَّ بَيْضٌ مَّكْنُونٌKamar dai su ƙwai ne ɓõyayye.0 Views
- فَأَقْبَلَ بَعْضُهُمْ عَلَىٰ بَعْضٍ يَتَسَاءَلُونَSai sãshensu ya fuskanta a kan sãshe, sunã tambayar jũna.0 Views
- قَالَ قَائِلٌ مِّنْهُمْ إِنِّي كَانَ لِي قَرِينٌWani mai magana daga cikinsu ya ce: "Lalle ni wani abõki ya kasance a gare ni (a dũniya)."0 Views
- يَقُولُ أَإِنَّكَ لَمِنَ الْمُصَدِّقِينَYanã cewa, "Shin, kai lalle, kanã daga mãsu gaskatãwa ne?"0 Views
- أَإِذَا مِتْنَا وَكُنَّا تُرَابًا وَعِظَامًا أَإِنَّا لَمَدِينُونَ"Ashe, idan muka mutu, kuma muka, kasance turɓaya da kasũsuwa, ashe, lalle, mũ tabbas waɗanda ake sãka wa ne?"0 Views
- قَالَ هَلْ أَنتُم مُّطَّلِعُونَ(Mai maganar) ya ce: "Shin, kõ ku, mãsu tsinkãya ne (mu gan shi)?"0 Views
- فَاطَّلَعَ فَرَآهُ فِي سَوَاءِ الْجَحِيمِSai ya tsinkãya, sai ya gan shi a cikin tsakar Jahim.0 Views
- قَالَ تَاللَّهِ إِن كِدتَّ لَتُرْدِينِYa ce (masa), "Wallahi, lalle, kã yi kusa, haƙĩƙã, ka halakãni."0 Views
- وَلَوْلَا نِعْمَةُ رَبِّي لَكُنتُ مِنَ الْمُحْضَرِينَ"Kuma bã dõmin ni'imar Ubangijĩna ba, lalle, dã na kasance daga waɗanda ake halartarwa (tãre da kai a cikin wutã)."0 Views
- أَفَمَا نَحْنُ بِمَيِّتِينَ"Shin fa, ba mu zama mãsu mutuwa ba."0 Views
- إِلَّا مَوْتَتَنَا الْأُولَىٰ وَمَا نَحْنُ بِمُعَذَّبِينَ"Sai mutuwarmu ta farko, kuma ba mu zama waɗanda ake azabtarwa ba?"0 Views
- إِنَّ هَـٰذَا لَهُوَ الْفَوْزُ الْعَظِيمُLalle, wannan shĩ ne babban rabo mai girma.0 Views
- لِمِثْلِ هَـٰذَا فَلْيَعْمَلِ الْعَامِلُونَSabõda irin wannan, sai mãsu aiki su yi ta aikatãwa.0 Views
- أَذَٰلِكَ خَيْرٌ نُّزُلًا أَمْ شَجَرَةُ الزَّقُّومِShin wancan shĩ ne mafi zama alhẽri ga liyafa kõ itãciyar zaƙƙũm?0 Views
- إِنَّا جَعَلْنَاهَا فِتْنَةً لِّلظَّالِمِينَLalle, Mũ, Mun sanya ta fitina ga. azzãlumai.0 Views
- إِنَّهَا شَجَرَةٌ تَخْرُجُ فِي أَصْلِ الْجَحِيمِLalle ita wata itãciya ce wadda take fita daga asalin Jahĩm.0 Views
- طَلْعُهَا كَأَنَّهُ رُءُوسُ الشَّيَاطِينِGundarta, kamar dai shi kãnun Shaiɗan ne.0 Views
- فَإِنَّهُمْ لَآكِلُونَ مِنْهَا فَمَالِئُونَ مِنْهَا الْبُطُونَTo, lalle sũ haƙĩƙa mãsu ci ne daga gare ta. Sa'an nan mãsu cika cikuna ne daga gare ta.0 Views
- ثُمَّ إِنَّ لَهُمْ عَلَيْهَا لَشَوْبًا مِّنْ حَمِيمٍSa'an nan lalle sunã da wani garwaye a kanta, daga ruwan zãfi.0 Views
- ثُمَّ إِنَّ مَرْجِعَهُمْ لَإِلَى الْجَحِيمِSa'an nan lalle makomarsu, haƙĩƙa, zuwa ga Jãhĩm take.0 Views
- إِنَّهُمْ أَلْفَوْا آبَاءَهُمْ ضَالِّينَLalle sũ, sun iske ubanninsu batattu.0 Views
- فَهُمْ عَلَىٰ آثَارِهِمْ يُهْرَعُونَSabõda haka sũ, a kan gurãbunsu, suke gaggãwa.0 Views
- وَلَقَدْ ضَلَّ قَبْلَهُمْ أَكْثَرُ الْأَوَّلِينَKuma tabbas haƙĩƙa mafi yawan mutãnen farko sun ɓace a gabãninsu.0 Views
- وَلَقَدْ أَرْسَلْنَا فِيهِم مُّنذِرِينَKuma tabbas haƙĩƙa, Mun aika mãsu gargaɗi a cikinsu.0 Views
- فَانظُرْ كَيْفَ كَانَ عَاقِبَةُ الْمُنذَرِينَSai ka dũba yadda ãƙibar waɗanda aka yi wa gargaɗi ta kasance.0 Views
- إِلَّا عِبَادَ اللَّهِ الْمُخْلَصِينَFãce bãyin Allah waɗanda aka tsarkake.0 Views
- وَلَقَدْ نَادَانَا نُوحٌ فَلَنِعْمَ الْمُجِيبُونَKuma lalle, haƙĩƙa' Nũhu ya kira Mu. To, madalla da mãsu karɓãwa, Mu.0 Views
- وَنَجَّيْنَاهُ وَأَهْلَهُ مِنَ الْكَرْبِ الْعَظِيمِKuma Mun tsĩrar da shi da mutãnensa daga bakin ciki babba.0 Views
- وَجَعَلْنَا ذُرِّيَّتَهُ هُمُ الْبَاقِينَMuka sanya zurriyarsa sunã mãsu wanzuwa.0 Views
- وَتَرَكْنَا عَلَيْهِ فِي الْآخِرِينَKuma Muka bar masa (yabo) a cikin jama'ar ƙarshe.0 Views
- سَلَامٌ عَلَىٰ نُوحٍ فِي الْعَالَمِينَAminci ya tabbata ga Nũhu, a cikin halittu.0 Views
- إِنَّا كَذَٰلِكَ نَجْزِي الْمُحْسِنِينَLalle Mũ kamar haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa.0 Views
- إِنَّهُ مِنْ عِبَادِنَا الْمُؤْمِنِينَLalle shi, yanã daga bãyinMu mũminai.0 Views
- ثُمَّ أَغْرَقْنَا الْآخَرِينَSã'an nan Muka nutsar da waɗansunsu.0 Views
- ۞ وَإِنَّ مِن شِيعَتِهِ لَإِبْرَاهِيمَKuma lalle daga ƙungiyarsa, haƙĩƙa, Ibrahĩm yake.0 Views
- إِذْ جَاءَ رَبَّهُ بِقَلْبٍ سَلِيمٍA lõkacin da ya je wa dangijinsa da zũciya kuɓutacciya.0 Views
- إِذْ قَالَ لِأَبِيهِ وَقَوْمِهِ مَاذَا تَعْبُدُونَA lõkacin da ya ce wa ubansa da mutãnensa, "Mẽne ne kuke bautãwa?"0 Views
- أَئِفْكًا آلِهَةً دُونَ اللَّهِ تُرِيدُونَ"Shin, ƙiren ƙarya (wãtau) gumãka, wanin Allah, kuke bautãwa?"0 Views
- فَمَا ظَنُّكُم بِرَبِّ الْعَالَمِينَ"To, mẽne ne zatonku game da Ubangijin halittu?"0 Views
- فَنَظَرَ نَظْرَةً فِي النُّجُومِSai ya yi dũbi, dũba ta sõsai, a cikin taurãri.0 Views
- فَقَالَ إِنِّي سَقِيمٌSã'an nan ya ce: "Nĩ mai rashin lãfiya ne."0 Views
- فَتَوَلَّوْا عَنْهُ مُدْبِرِينَSai suka jũya ga barinsa, sunã mãsu jũyãwa da bãya.0 Views
- فَرَاغَ إِلَىٰ آلِهَتِهِمْ فَقَالَ أَلَا تَأْكُلُونَSai ya karkata zuwa ga gumãkansu, sa'an nan ya ce: "Ashe bã zã ku ci ba?0 Views
- مَا لَكُمْ لَا تَنطِقُونَ"Me ya sãme ku, bã ku magana?"0 Views
- فَرَاغَ عَلَيْهِمْ ضَرْبًا بِالْيَمِينِSai ya zuba dũka a kansu da hannun dãma.0 Views
- فَأَقْبَلُوا إِلَيْهِ يَزِفُّونَSai suka fuskanto zuwa gare shi, sunã gaggãwa.0 Views
- قَالَ أَتَعْبُدُونَ مَا تَنْحِتُونَYa ce, "Kunã bauta wa abin da kuke sassaƙawa,0 Views
- وَاللَّهُ خَلَقَكُمْ وَمَا تَعْمَلُونَ"Alhãli, Allah ne Ya halitta ku game da abin da kuke aikatãwa?"0 Views
- قَالُوا ابْنُوا لَهُ بُنْيَانًا فَأَلْقُوهُ فِي الْجَحِيمِSuka ce: "Ku gina wani gini sabõda shi, sa'an nan ku jẽfa shi a cikin Jahĩm."0 Views
- فَأَرَادُوا بِهِ كَيْدًا فَجَعَلْنَاهُمُ الْأَسْفَلِينَSabõda haka suka yi nufin makĩda game da shi. Sai Muka sanya su, sũ ne mafi ƙasƙanci.0 Views
- وَقَالَ إِنِّي ذَاهِبٌ إِلَىٰ رَبِّي سَيَهْدِينِKuma (Ibrahĩm] ya ce: "Lalle, nĩ mai tafiya ne zuwa ga Ubangijĩna, zai shiryar da ni."0 Views
- رَبِّ هَبْ لِي مِنَ الصَّالِحِينَ"Ya Ubangijĩna! Ka bã ni (abõkin zama) daga sãlihan mutãne."0 Views
- فَبَشَّرْنَاهُ بِغُلَامٍ حَلِيمٍSai Muka yi masa bushãra da wani yãro mai haƙuri.0 Views
- فَلَمَّا بَلَغَ مَعَهُ السَّعْيَ قَالَ يَا بُنَيَّ إِنِّي أَرَىٰ فِي الْمَنَامِ أَنِّي أَذْبَحُكَ فَانظُرْ مَاذَا تَرَىٰ ۚ قَالَ يَا أَبَتِ افْعَلْ مَا تُؤْمَرُ ۖ سَتَجِدُنِي إِن شَاءَ اللَّهُ مِنَ الصَّابِرِينَTo, a lõkacin da ya isa aiki tãre da shi, ya ce: "Ya ƙaramin ɗãna! Lalle ne inã gani, a ciki barci, lalle inã yanka ka. To, ka dũba mẽ ka gani?" (Yãron) ya ce: "Ya, Bãbãna! Ka aikata abin da aka umurce ka, zã ka sãme ni, in Allah Ya so, daga mãsu haƙuri."0 Views
- فَلَمَّا أَسْلَمَا وَتَلَّهُ لِلْجَبِينِTo, a lõkacin da suka yi sallama, (Ibrahĩm) ya kãyar da shi ga gẽfen gõshinsa.0 Views
- وَنَادَيْنَاهُ أَن يَا إِبْرَاهِيمُKuma Muka kira shi cẽwa "Ya Ibrahĩm!"0 Views
- قَدْ صَدَّقْتَ الرُّؤْيَا ۚ إِنَّا كَذَٰلِكَ نَجْزِي الْمُحْسِنِينَ"Haƙĩƙa kã gaskata mafarkin." Lalle kamar haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa.0 Views
- إِنَّ هَـٰذَا لَهُوَ الْبَلَاءُ الْمُبِينُLalle wannan ita ce jarrabãwa bayyananna.0 Views
- وَفَدَيْنَاهُ بِذِبْحٍ عَظِيمٍKuma Muka yi fansar yãron da wani abin yanka, mai girma.0 Views
- وَتَرَكْنَا عَلَيْهِ فِي الْآخِرِينَKuma Muka bar (yabo) a kansa a cikin mutãnen ƙarshe.0 Views
- سَلَامٌ عَلَىٰ إِبْرَاهِيمَAminci ya tabbata ga Ibrãhĩm.0 Views
- كَذَٰلِكَ نَجْزِي الْمُحْسِنِينَKamar haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa.0 Views
- إِنَّهُ مِنْ عِبَادِنَا الْمُؤْمِنِينَLalle shĩ, yanã daga bãyinMu mũminai.0 Views
- وَبَشَّرْنَاهُ بِإِسْحَاقَ نَبِيًّا مِّنَ الصَّالِحِينَKuma Muka yi masa bushãra Da Is'hãƙa ya zama Annabi daga sãlihan mutãne.0 Views
- وَبَارَكْنَا عَلَيْهِ وَعَلَىٰ إِسْحَاقَ ۚ وَمِن ذُرِّيَّتِهِمَا مُحْسِنٌ وَظَالِمٌ لِّنَفْسِهِ مُبِينٌKuma Muka yi albarka a gare shi, kuma ga Is'hãka. Kuma daga cikin zurriyarsu akwai mai kyautatãwa da kuma maizãlunci dõmin kansa, mai bayyanãwa (ga zãluncin).0 Views
- وَلَقَدْ مَنَنَّا عَلَىٰ مُوسَىٰ وَهَارُونَKuma lalle, Mun yi ni'ima ga Mũsã da Hãrũna.0 Views
- وَنَجَّيْنَاهُمَا وَقَوْمَهُمَا مِنَ الْكَرْبِ الْعَظِيمِKuma Muka tsĩrar da su da mutãnensu daga bakin ciki mai girma.0 Views
- وَنَصَرْنَاهُمْ فَكَانُوا هُمُ الْغَالِبِينَKuma Muka taimake su, sabõda haka suka kasance mãsu rinjãya.0 Views
- وَآتَيْنَاهُمَا الْكِتَابَ الْمُسْتَبِينَKuma Muka ba su Littãfi mai iyãkar bayãni.0 Views
- وَهَدَيْنَاهُمَا الصِّرَاطَ الْمُسْتَقِيمَKuma Muka shiryar da su ga hanya mĩƙaƙƙiya.0 Views
- وَتَرَكْنَا عَلَيْهِمَا فِي الْآخِرِينَKuma Muka bar (yabo) a gare su a cikin mutãnen karshe.0 Views
- سَلَامٌ عَلَىٰ مُوسَىٰ وَهَارُونَAminci ya tabbata ga Mũsã da Hãruna.0 Views
- إِنَّا كَذَٰلِكَ نَجْزِي الْمُحْسِنِينَLalle kamar haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa.0 Views
- إِنَّهُمَا مِنْ عِبَادِنَا الْمُؤْمِنِينَLalle, sunã daga bãyinMu mũminai.0 Views
- وَإِنَّ إِلْيَاسَ لَمِنَ الْمُرْسَلِينَKuma lalle Ilyãs, haƙĩƙa, yanã daga Manzanni.0 Views
- إِذْ قَالَ لِقَوْمِهِ أَلَا تَتَّقُونَA lõkacin da yake ce wa mutãnensa, "Ashe, bã zã ku yi taƙawa ba?"0 Views
- أَتَدْعُونَ بَعْلًا وَتَذَرُونَ أَحْسَنَ الْخَالِقِينَ"Shin, kunã bauta wa Ba'al ne, kuma kunã barin Mafi kyautatãwar mãsu halitta?"0 Views
- اللَّهَ رَبَّكُمْ وَرَبَّ آبَائِكُمُ الْأَوَّلِينَ"Allah Ubangijinku, kuma Ubangijin ubanninku farko?"0 Views
- فَكَذَّبُوهُ فَإِنَّهُمْ لَمُحْضَرُونَSai suka ƙaryata shi. Sabõda haka sũ lalle waɗanda zã a halartãwa ne (a wutã).1 Views
- إِلَّا عِبَادَ اللَّهِ الْمُخْلَصِينَSai bãyin Allah waɗanda aka tsarkake.1 Views
- وَتَرَكْنَا عَلَيْهِ فِي الْآخِرِينَKuma Muka bar (yabo) a gare shi, a cikin mutãnen ƙarshe.1 Views
- سَلَامٌ عَلَىٰ إِلْ يَاسِينَAminci ya tabbata ga Ilyãs.1 Views
- إِنَّا كَذَٰلِكَ نَجْزِي الْمُحْسِنِينَLalle Mũ kamar haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa.1 Views
- إِنَّهُ مِنْ عِبَادِنَا الْمُؤْمِنِينَLalle shĩ, yanã daga bãyinMu mũminai.1 Views
- وَإِنَّ لُوطًا لَّمِنَ الْمُرْسَلِينَKuma lalle Lũdu, haƙĩƙa, yanã daga Manzanni.1 Views
- إِذْ نَجَّيْنَاهُ وَأَهْلَهُ أَجْمَعِينَA lõkacin da Muka tsĩrar da shi, da mutãnensa gabã ɗaya.1 Views
- إِلَّا عَجُوزًا فِي الْغَابِرِينَSai wata tsõhuwa tanã a cikin mãsu wanzuwa (a cikin azãba).1 Views
- ثُمَّ دَمَّرْنَا الْآخَرِينَSã'an nan Muka darkãke waɗansu mutãnen.1 Views
- وَإِنَّكُمْ لَتَمُرُّونَ عَلَيْهِم مُّصْبِحِينَKuma lalle kũ, haƙĩƙa, kunã shũɗewa a kansu, kunã mãsu asubanci.1 Views
- وَبِاللَّيْلِ ۗ أَفَلَا تَعْقِلُونَKuma da dare. Shin fa, bã zã ku hankalta ba?1 Views
- وَإِنَّ يُونُسَ لَمِنَ الْمُرْسَلِينَKuma lalle Yũnusa, haƙĩƙa, yanã daga Manzanni.1 Views
- إِذْ أَبَقَ إِلَى الْفُلْكِ الْمَشْحُونِA lõkacin da ya gudu zuwa ga jirgin ruwa wanda aka yi wa lõdi.1 Views
- فَسَاهَمَ فَكَانَ مِنَ الْمُدْحَضِينَSã'an nan ya yi ƙuri'a, sai ya kasance a cikin waɗanda aka rinjaya.1 Views
- فَالْتَقَمَهُ الْحُوتُ وَهُوَ مُلِيمٌSai kĩfi ya yi lõma da shi, alhãli kuwa yanã wanda ake zargi.1 Views
- فَلَوْلَا أَنَّهُ كَانَ مِنَ الْمُسَبِّحِينَTo, ba dõmin lalle shi ya kasance daga mãsu tasbĩhi ba,1 Views
- لَلَبِثَ فِي بَطْنِهِ إِلَىٰ يَوْمِ يُبْعَثُونَLalle dã ya zauna a cikin cikinsa har ya zuwa rãnar da zã a tãyar da su.1 Views
- ۞ فَنَبَذْنَاهُ بِالْعَرَاءِ وَهُوَ سَقِيمٌSai Muka jẽfa shi ga wani fĩli alhãli kuwa yanã mai raunin rashin lãfiya.1 Views
- وَأَنبَتْنَا عَلَيْهِ شَجَرَةً مِّن يَقْطِينٍKuma Muka tsirar da wata itãciya ta kankana a kusa da shi.1 Views
- وَأَرْسَلْنَاهُ إِلَىٰ مِائَةِ أَلْفٍ أَوْ يَزِيدُونَKuma Muka aika shi zuwa ga waɗansu mutãne dubuɗari, kõ sunã ƙaruwa (a kan haka).1 Views
- فَآمَنُوا فَمَتَّعْنَاهُمْ إِلَىٰ حِينٍSai suka yi ĩmãni sabõda haka Muka jiyar da su dãdi har wani lõkaci.1 Views
- فَاسْتَفْتِهِمْ أَلِرَبِّكَ الْبَنَاتُ وَلَهُمُ الْبَنُونَSabõda haka, ka tambaye su, "Shin, Ubangijinka ne da 'ya'ya mãtã, kuma su da ɗiya maza?"1 Views
- أَمْ خَلَقْنَا الْمَلَائِكَةَ إِنَاثًا وَهُمْ شَاهِدُونَKõ kuma Mun halitta malã'iku mãtã ne, alhãli kuwa sũ sunãhalarce?1 Views
- أَلَا إِنَّهُم مِّنْ إِفْكِهِمْ لَيَقُولُونَTo! Lalle sũ, daga ƙiren ƙaryarsu sunã cẽwa.1 Views
- وَلَدَ اللَّهُ وَإِنَّهُمْ لَكَاذِبُونَ"Allah Yã haihu," alhãli kuwa lalle sũ, haƙĩƙa maƙaryata ne.1 Views
- أَصْطَفَى الْبَنَاتِ عَلَى الْبَنِينَShin, Yã zãɓi 'yã'ya mãtã ne a kan ɗiya maza?1 Views
- مَا لَكُمْ كَيْفَ تَحْكُمُونَMẽ ya same ku? Yãya kuke hukuntãwa (wannanhukunci)?0 Views
- أَفَلَا تَذَكَّرُونَShin, bã ku tunãni?0 Views
- أَمْ لَكُمْ سُلْطَانٌ مُّبِينٌKo kuma kunã da wani dalĩli bayyananne ne?0 Views
- فَأْتُوا بِكِتَابِكُمْ إِن كُنتُمْ صَادِقِينَTo, ku zo da littãfinku idan kun kasance mãsu gaskiya.0 Views
- وَجَعَلُوا بَيْنَهُ وَبَيْنَ الْجِنَّةِ نَسَبًا ۚ وَلَقَدْ عَلِمَتِ الْجِنَّةُ إِنَّهُمْ لَمُحْضَرُونَKuma suka sanya nasaba a tsakãninSa da tsakãnin aljannu. Alhãli kuwa Lalle aljannu sun sani, "Lalle sũ, haƙĩƙa waɗanda ake halartarwa ne (a cikin wutã.)"0 Views
- سُبْحَانَ اللَّهِ عَمَّا يَصِفُونَTsarki ya tabbata ga Allah daga abin da suke siffantãwa.0 Views
- إِلَّا عِبَادَ اللَّهِ الْمُخْلَصِينَSai bãyin Allah waɗanda aka tsarkake.0 Views
- فَإِنَّكُمْ وَمَا تَعْبُدُونَTo, lalle, ku da abin da kuke bautãwa,0 Views
- مَا أَنتُمْ عَلَيْهِ بِفَاتِنِينَBa ku zama mãsu buwãya ba a gare Shi.0 Views
- إِلَّا مَنْ هُوَ صَالِ الْجَحِيمِSai wanda yake mai shiga babbar wutã Jahĩm.0 Views
- وَمَا مِنَّا إِلَّا لَهُ مَقَامٌ مَّعْلُومٌ"Kuma bãbu kõwa daga cikinmu, fãce yanã da matsayi sananne."0 Views
- وَإِنَّا لَنَحْنُ الصَّافُّونَ"Kuma lalle mu, haƙĩƙa, mũ ne mãsu yin sahu-sahu (dõmin ibãda)."0 Views
- وَإِنَّا لَنَحْنُ الْمُسَبِّحُونَ"Kuma lalle mũ haƙĩƙa, mũ ne mãsu yin tasbĩhi."0 Views
- وَإِن كَانُوا لَيَقُولُونَKuma lalle sũ, sun kasance sunã cẽwa,0 Views
- لَوْ أَنَّ عِندَنَا ذِكْرًا مِّنَ الْأَوَّلِينَ"Dã lalle munã da wani littãfi irin na mutãnen farko."0 Views
- لَكُنَّا عِبَادَ اللَّهِ الْمُخْلَصِينَ"Lalle dã mun kasance bãyin Allah waɗanda aka tsarkake."0 Views
- فَكَفَرُوا بِهِ ۖ فَسَوْفَ يَعْلَمُونَSai suka kãfirta da shi. Sabõda haka zã su sani.0 Views
- وَلَقَدْ سَبَقَتْ كَلِمَتُنَا لِعِبَادِنَا الْمُرْسَلِينَKuma lalle, haƙĩƙa kalmarMu ta gabãta ga bãyinMu, Manzanni.0 Views
- إِنَّهُمْ لَهُمُ الْمَنصُورُونَLalle sũ, haƙĩƙa, sũ ne waɗanda ake taimako.0 Views
- وَإِنَّ جُندَنَا لَهُمُ الْغَالِبُونَKuma lalle rundunarMu, haƙĩƙa, sũ ne marinjaya.0 Views
- فَتَوَلَّ عَنْهُمْ حَتَّىٰ حِينٍSabõda haka juya daga barinsu, har a wani lõkaci.0 Views
- وَأَبْصِرْهُمْ فَسَوْفَ يُبْصِرُونَKa nũna musu (gaskiya), da haka zã su dinga gani.0 Views
- أَفَبِعَذَابِنَا يَسْتَعْجِلُونَShin fa, da azabarMu suke nẽman gaggãwa?0 Views
- فَإِذَا نَزَلَ بِسَاحَتِهِمْ فَسَاءَ صَبَاحُ الْمُنذَرِينَTo, idan ta sauka ga farfãjiyarsu, to, sãfiyar wadanda ake yi wa gargaɗi ta mũnana.0 Views
- وَتَوَلَّ عَنْهُمْ حَتَّىٰ حِينٍKuma ka jũya daga barinsu har a wani lõkaci.0 Views
- وَأَبْصِرْ فَسَوْفَ يُبْصِرُونَKa nũna (musu gaskiya), da haka zã su dinga nũnãwa.0 Views
- سُبْحَانَ رَبِّكَ رَبِّ الْعِزَّةِ عَمَّا يَصِفُونَTsarki ya tabbata ga Ubangijinka, Ubangijin rinjãye, daga barin abin da suke siffantãwa.0 Views
- وَسَلَامٌ عَلَى الْمُرْسَلِينَKuma aminci ya tabbata ga Manzanni.0 Views
- وَالْحَمْدُ لِلَّهِ رَبِّ الْعَالَمِينَKuma gõdiya ta tabbata ga Allah Ubangijin halittu.0 Views
Teks Al-Qur'an: Tanzil Project (https://tanzil.net), lisensi CC BY 3.0. · Abubakar Mahmoud Gumi (Tanzil Project, tanzil.net)