Mushaf Page 451
صفحة ٤٥١
- Ghunnah
- Qalqalah
- Ikhfa (Haqiqi)
- Ikhfa Shafawi
- Idgham with Ghunnah
- Idgham without Ghunnah
- Idgham Shafawi (Mimi)
- Madd Lazim (6 counts)
- Madd Wajib Muttasil (4-5 counts)
- Madd Jaiz Munfasil (2, 4, 6 counts)
Each word’s meaning appears right below it; the transliteration follows below the words.
Surah as-saffat
- فَكَذَّبُوهُ فَإِنَّهُمْ لَمُحْضَرُونَSai suka ƙaryata shi. Sabõda haka sũ lalle waɗanda zã a halartãwa ne (a wutã).1 Views
- إِلَّا عِبَادَ اللَّهِ الْمُخْلَصِينَSai bãyin Allah waɗanda aka tsarkake.1 Views
- وَتَرَكْنَا عَلَيْهِ فِي الْآخِرِينَKuma Muka bar (yabo) a gare shi, a cikin mutãnen ƙarshe.1 Views
- سَلَامٌ عَلَىٰ إِلْ يَاسِينَAminci ya tabbata ga Ilyãs.1 Views
- إِنَّا كَذَٰلِكَ نَجْزِي الْمُحْسِنِينَLalle Mũ kamar haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa.1 Views
- إِنَّهُ مِنْ عِبَادِنَا الْمُؤْمِنِينَLalle shĩ, yanã daga bãyinMu mũminai.1 Views
- وَإِنَّ لُوطًا لَّمِنَ الْمُرْسَلِينَKuma lalle Lũdu, haƙĩƙa, yanã daga Manzanni.1 Views
- إِذْ نَجَّيْنَاهُ وَأَهْلَهُ أَجْمَعِينَA lõkacin da Muka tsĩrar da shi, da mutãnensa gabã ɗaya.1 Views
- إِلَّا عَجُوزًا فِي الْغَابِرِينَSai wata tsõhuwa tanã a cikin mãsu wanzuwa (a cikin azãba).1 Views
- ثُمَّ دَمَّرْنَا الْآخَرِينَSã'an nan Muka darkãke waɗansu mutãnen.1 Views
- وَإِنَّكُمْ لَتَمُرُّونَ عَلَيْهِم مُّصْبِحِينَKuma lalle kũ, haƙĩƙa, kunã shũɗewa a kansu, kunã mãsu asubanci.1 Views
- وَبِاللَّيْلِ ۗ أَفَلَا تَعْقِلُونَKuma da dare. Shin fa, bã zã ku hankalta ba?1 Views
- وَإِنَّ يُونُسَ لَمِنَ الْمُرْسَلِينَKuma lalle Yũnusa, haƙĩƙa, yanã daga Manzanni.1 Views
- إِذْ أَبَقَ إِلَى الْفُلْكِ الْمَشْحُونِA lõkacin da ya gudu zuwa ga jirgin ruwa wanda aka yi wa lõdi.1 Views
- فَسَاهَمَ فَكَانَ مِنَ الْمُدْحَضِينَSã'an nan ya yi ƙuri'a, sai ya kasance a cikin waɗanda aka rinjaya.1 Views
- فَالْتَقَمَهُ الْحُوتُ وَهُوَ مُلِيمٌSai kĩfi ya yi lõma da shi, alhãli kuwa yanã wanda ake zargi.1 Views
- فَلَوْلَا أَنَّهُ كَانَ مِنَ الْمُسَبِّحِينَTo, ba dõmin lalle shi ya kasance daga mãsu tasbĩhi ba,1 Views
- لَلَبِثَ فِي بَطْنِهِ إِلَىٰ يَوْمِ يُبْعَثُونَLalle dã ya zauna a cikin cikinsa har ya zuwa rãnar da zã a tãyar da su.1 Views
- ۞ فَنَبَذْنَاهُ بِالْعَرَاءِ وَهُوَ سَقِيمٌSai Muka jẽfa shi ga wani fĩli alhãli kuwa yanã mai raunin rashin lãfiya.1 Views
- وَأَنبَتْنَا عَلَيْهِ شَجَرَةً مِّن يَقْطِينٍKuma Muka tsirar da wata itãciya ta kankana a kusa da shi.1 Views
- وَأَرْسَلْنَاهُ إِلَىٰ مِائَةِ أَلْفٍ أَوْ يَزِيدُونَKuma Muka aika shi zuwa ga waɗansu mutãne dubuɗari, kõ sunã ƙaruwa (a kan haka).1 Views
- فَآمَنُوا فَمَتَّعْنَاهُمْ إِلَىٰ حِينٍSai suka yi ĩmãni sabõda haka Muka jiyar da su dãdi har wani lõkaci.1 Views
- فَاسْتَفْتِهِمْ أَلِرَبِّكَ الْبَنَاتُ وَلَهُمُ الْبَنُونَSabõda haka, ka tambaye su, "Shin, Ubangijinka ne da 'ya'ya mãtã, kuma su da ɗiya maza?"1 Views
- أَمْ خَلَقْنَا الْمَلَائِكَةَ إِنَاثًا وَهُمْ شَاهِدُونَKõ kuma Mun halitta malã'iku mãtã ne, alhãli kuwa sũ sunãhalarce?1 Views
- أَلَا إِنَّهُم مِّنْ إِفْكِهِمْ لَيَقُولُونَTo! Lalle sũ, daga ƙiren ƙaryarsu sunã cẽwa.1 Views
- وَلَدَ اللَّهُ وَإِنَّهُمْ لَكَاذِبُونَ"Allah Yã haihu," alhãli kuwa lalle sũ, haƙĩƙa maƙaryata ne.1 Views
- أَصْطَفَى الْبَنَاتِ عَلَى الْبَنِينَShin, Yã zãɓi 'yã'ya mãtã ne a kan ɗiya maza?1 Views