Mushaf Page 447
صفحة ٤٤٧
- Ghunnah
- Qalqalah
- Ikhfa (Haqiqi)
- Ikhfa Shafawi
- Idgham with Ghunnah
- Idgham without Ghunnah
- Idgham Shafawi (Mimi)
- Madd Lazim (6 counts)
- Madd Wajib Muttasil (4-5 counts)
- Madd Jaiz Munfasil (2, 4, 6 counts)
Each word’s meaning appears right below it; the transliteration follows below the words.
Surah as-saffat
- مَا لَكُمْ لَا تَنَاصَرُونَMe ya sãme ku, bã ku taimakon jũna?0 Views
- بَلْ هُمُ الْيَوْمَ مُسْتَسْلِمُونَÃ'a, sũ a yau, mãsu sallamãwa ne.0 Views
- وَأَقْبَلَ بَعْضُهُمْ عَلَىٰ بَعْضٍ يَتَسَاءَلُونَKuma sãshensu ya fuskanta ga sãshe, sunã tambayar jũna.0 Views
- قَالُوا إِنَّكُمْ كُنتُمْ تَأْتُونَنَا عَنِ الْيَمِينِSuka ce: "Lalle kũ, kun kasance kunã jẽ mana daga wajen dãma (inda muka amince)."0 Views
- قَالُوا بَل لَّمْ تَكُونُوا مُؤْمِنِينَSuka ce: "Ã'a, ba ku kasance mũminai ba.0 Views
- وَمَا كَانَ لَنَا عَلَيْكُم مِّن سُلْطَانٍ ۖ بَلْ كُنتُمْ قَوْمًا طَاغِينَ"Kuma wani dalĩli bai kasance ba gare mu a kanku. Ã'a, kun kasance mutãne ne mãsu kẽtare iyãka."0 Views
- فَحَقَّ عَلَيْنَا قَوْلُ رَبِّنَا ۖ إِنَّا لَذَائِقُونَ"Sabõda haka maganar Ubangijinmu ta wajaba a kanmu. Lalle mũ, mãsu ɗanɗanãwa ne."0 Views
- فَأَغْوَيْنَاكُمْ إِنَّا كُنَّا غَاوِينَ"Sabõda haka muka ɓatar da ku. Lalle mũ, mun kasance ɓatattu."0 Views
- فَإِنَّهُمْ يَوْمَئِذٍ فِي الْعَذَابِ مُشْتَرِكُونَTo lalle sũ a rãnar nan, mãsu tãrayya ne a cikin azãbar.0 Views
- إِنَّا كَذَٰلِكَ نَفْعَلُ بِالْمُجْرِمِينَLalle Mũ, kamar haka Muke aikatãwa game, da mãsu laifi.0 Views
- إِنَّهُمْ كَانُوا إِذَا قِيلَ لَهُمْ لَا إِلَـٰهَ إِلَّا اللَّهُ يَسْتَكْبِرُونَLalle sũ, sun kasance idan an ce musu: "Bãbu abin bautãwa, fãce Allah," sai su dõra girman kai.0 Views
- وَيَقُولُونَ أَئِنَّا لَتَارِكُو آلِهَتِنَا لِشَاعِرٍ مَّجْنُونٍKuma sunã cẽwa, "Shin, mũ lalle mãsu barin gumãkanmu ne, sabõda maganar wani mawãƙi mahaukaci?0 Views
- بَلْ جَاءَ بِالْحَقِّ وَصَدَّقَ الْمُرْسَلِينَÃ'a, yã zo da gaskiya kuma ya gaskata Manzanni.0 Views
- إِنَّكُمْ لَذَائِقُو الْعَذَابِ الْأَلِيمِLalle kũ, haƙĩƙa mãsu ɗanɗana azãba mai raɗaɗi ne.0 Views
- وَمَا تُجْزَوْنَ إِلَّا مَا كُنتُمْ تَعْمَلُونَKuma bã zã a sãka muku ba fãce da abin da kuka kasance kunã aikatãwa.0 Views
- إِلَّا عِبَادَ اللَّهِ الْمُخْلَصِينَFãce bãyin Allah waɗanda aka tsarkake.0 Views
- أُولَـٰئِكَ لَهُمْ رِزْقٌ مَّعْلُومٌWaɗannan sunã da abinci sananne.0 Views
- فَوَاكِهُ ۖ وَهُم مُّكْرَمُونَ'Ya'yan itãcen marmari, kuma sunã waɗanda ake girmamãwa.0 Views
- فِي جَنَّاتِ النَّعِيمِA cikin gidãjen Aljannar ni'ima.0 Views
- عَلَىٰ سُرُرٍ مُّتَقَابِلِينَA kan karagu, sunã mãsu fuskantar jũna.0 Views
- يُطَافُ عَلَيْهِم بِكَأْسٍ مِّن مَّعِينٍAnã kẽwayãwa a kansu da hinjãlan giya, ta daga waɗansu marẽmari.0 Views
- بَيْضَاءَ لَذَّةٍ لِّلشَّارِبِينَFarã mai dãɗi ga mashãyan.0 Views
- لَا فِيهَا غَوْلٌ وَلَا هُمْ عَنْهَا يُنزَفُونَA cikinta bãbu jirĩ kuma ba su zama mãsu mãye daga gare ta ba,0 Views
- وَعِندَهُمْ قَاصِرَاتُ الطَّرْفِ عِينٌKuma a wurinsu, akwai mãtan aure mãsu taƙaita kallonsu, mãsu manyan idãnu.0 Views
- كَأَنَّهُنَّ بَيْضٌ مَّكْنُونٌKamar dai su ƙwai ne ɓõyayye.0 Views
- فَأَقْبَلَ بَعْضُهُمْ عَلَىٰ بَعْضٍ يَتَسَاءَلُونَSai sãshensu ya fuskanta a kan sãshe, sunã tambayar jũna.0 Views
- قَالَ قَائِلٌ مِّنْهُمْ إِنِّي كَانَ لِي قَرِينٌWani mai magana daga cikinsu ya ce: "Lalle ni wani abõki ya kasance a gare ni (a dũniya)."0 Views