Mushaf Page 446
صفحة ٤٤٦
- Ghunnah
- Qalqalah
- Ikhfa (Haqiqi)
- Ikhfa Shafawi
- Idgham with Ghunnah
- Idgham without Ghunnah
- Idgham Shafawi (Mimi)
- Madd Lazim (6 counts)
- Madd Wajib Muttasil (4-5 counts)
- Madd Jaiz Munfasil (2, 4, 6 counts)
Each word’s meaning appears right below it; the transliteration follows below the words.
Surah as-saffat
Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
- وَالصَّافَّاتِ صَفًّاInã rantsuwa da mãsu yin sahu-sahu (a cikin salla kõ yãƙi).0 Views
- فَالزَّاجِرَاتِ زَجْرًاSa'an nan mãsu yin tsãwa dõmin gargaɗi.0 Views
- فَالتَّالِيَاتِ ذِكْرًاSa'an nan da mãsu karãtun abin tunãtarwa.0 Views
- إِنَّ إِلَـٰهَكُمْ لَوَاحِدٌLalle Abin bautawarku haƙĩƙa ¦aya ne.0 Views
- رَّبُّ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ وَمَا بَيْنَهُمَا وَرَبُّ الْمَشَارِقِUbangijin sammai da ƙasã da abin da ke tsakãninsu, kuma Ubangijin wurãren fitar rãnã.0 Views
- إِنَّا زَيَّنَّا السَّمَاءَ الدُّنْيَا بِزِينَةٍ الْكَوَاكِبِLalle Mũ, Mun ƙãwatãr da sama ta kusa da wata ƙawa, watau taurãri.0 Views
- وَحِفْظًا مِّن كُلِّ شَيْطَانٍ مَّارِدٍKuma sunã tsari daga dukan Shaiɗan mai tsaurin kai.0 Views
- لَّا يَسَّمَّعُونَ إِلَى الْمَلَإِ الْأَعْلَىٰ وَيُقْذَفُونَ مِن كُلِّ جَانِبٍBã zã su iya saurãre zuwa ga jama'a mafi ɗaukaka (Malã'iku) ba, kuma anã jĩfar su daga kõwane gẽfe.0 Views
- دُحُورًا ۖ وَلَهُمْ عَذَابٌ وَاصِبٌDõmin tunkuɗẽwa kuma sunã da wata azãba tabbatacciya.0 Views
- إِلَّا مَنْ خَطِفَ الْخَطْفَةَ فَأَتْبَعَهُ شِهَابٌ ثَاقِبٌFãce wanda ya fizgi wata kalma, sai yũla mai haske ta bĩ shi.0 Views
- فَاسْتَفْتِهِمْ أَهُمْ أَشَدُّ خَلْقًا أَم مَّنْ خَلَقْنَا ۚ إِنَّا خَلَقْنَاهُم مِّن طِينٍ لَّازِبٍKa tambaye su: "Shin sũ ne mafi wuya ga halittawa, kõ, kuwa waɗanda Muka halitta?" Lalle Mũ, Mun halitta su daga lãkã mai ɗauri.0 Views
- بَلْ عَجِبْتَ وَيَسْخَرُونَÃ'a, kã yi mãmãki, alhãli kuwa sunã ta yin izgili.0 Views
- وَإِذَا ذُكِّرُوا لَا يَذْكُرُونَKuma idan aka tunãtar da su, bã su tunãwa.0 Views
- وَإِذَا رَأَوْا آيَةً يَسْتَسْخِرُونَIdan suka ga wata ãyã, sai su dinga yin izgili.0 Views
- وَقَالُوا إِنْ هَـٰذَا إِلَّا سِحْرٌ مُّبِينٌKuma su ce, "Wannnan bã kõme ba, fãce sihiri, ne bayyananne."0 Views
- أَإِذَا مِتْنَا وَكُنَّا تُرَابًا وَعِظَامًا أَإِنَّا لَمَبْعُوثُونَ"Shin, idan mun mutu, kuma muka kasance turɓaya da kasũsuwa, ashe, lalle mũ tabbas waɗandaake tãyarwa ne?0 Views
- أَوَآبَاؤُنَا الْأَوَّلُونَ"Ashe kõ da ubanninmu na farko?"0 Views
- قُلْ نَعَمْ وَأَنتُمْ دَاخِرُونَKa ce: "Na'am alhãli kuwa kunã ƙasƙantattu."0 Views
- فَإِنَّمَا هِيَ زَجْرَةٌ وَاحِدَةٌ فَإِذَا هُمْ يَنظُرُونَTsãwa guda kawai ce, sai gã su, sunã dũbi.0 Views
- وَقَالُوا يَا وَيْلَنَا هَـٰذَا يَوْمُ الدِّينِKuma su ce: "Yã bonenmu! Wannan ita ce rãnar sakamako."0 Views
- هَـٰذَا يَوْمُ الْفَصْلِ الَّذِي كُنتُم بِهِ تُكَذِّبُونَWannan ita ce rãnar rarrabẽwa wadda kuka kasance kuna ƙaryatãwa.0 Views
- ۞ احْشُرُوا الَّذِينَ ظَلَمُوا وَأَزْوَاجَهُمْ وَمَا كَانُوا يَعْبُدُونَKu tãra waɗanda suka yi zãlunci, da abõkan haɗinsu, da abin da suka kasance sunã bautãwa.0 Views
- مِن دُونِ اللَّهِ فَاهْدُوهُمْ إِلَىٰ صِرَاطِ الْجَحِيمِWanin Allah, sabõda haka ku shiryar da su zuwa ga hanyar Jahĩm.0 Views
- وَقِفُوهُمْ ۖ إِنَّهُم مَّسْئُولُونَKuma ku tsayar da su, lalle su, waɗanda ake yi wa tambaya ne.0 Views