Mushaf Page 574
صفحة ٥٧٤
- Ghunnah
- Qalqalah
- Ikhfa (Haqiqi)
- Ikhfa Shafawi
- Idgham with Ghunnah
- Idgham without Ghunnah
- Idgham Shafawi (Mimi)
- Madd Lazim (6 counts)
- Madd Wajib Muttasil (4-5 counts)
- Madd Jaiz Munfasil (2, 4, 6 counts)
Each word’s meaning appears right below it; the transliteration follows below the words.
Surah al-muzzammil
Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
- يَا أَيُّهَا الْمُزَّمِّلُYã wanda ya lulluɓe!0 Views
- قُمِ اللَّيْلَ إِلَّا قَلِيلًاKa tsayu domin yin salla a cikin dare (duka) fãce kaɗan.0 Views
- نِّصْفَهُ أَوِ انقُصْ مِنْهُ قَلِيلًاRabinsa, ko ka rage abu kaɗan daga gare shi.0 Views
- أَوْ زِدْ عَلَيْهِ وَرَتِّلِ الْقُرْآنَ تَرْتِيلًاKo ka ƙara kansa kuma ka kyautata karanta Alƙu'ãni, daki daki.0 Views
- إِنَّا سَنُلْقِي عَلَيْكَ قَوْلًا ثَقِيلًاLalle ne, Mũ, zã Mu jẽfa maka magana mai nauyi.0 Views
- إِنَّ نَاشِئَةَ اللَّيْلِ هِيَ أَشَدُّ وَطْئًا وَأَقْوَمُ قِيلًاLalle ne, tashin dare shi ne mafi tsananin natsuwa, kuma mafi daidaituwa ga magana.0 Views
- إِنَّ لَكَ فِي النَّهَارِ سَبْحًا طَوِيلًاLalle ne, kanã da, a cikin yini, wani tasĩhi mai tsawo.0 Views
- وَاذْكُرِ اسْمَ رَبِّكَ وَتَبَتَّلْ إِلَيْهِ تَبْتِيلًاKuma ka ambaci sũnan Ubangijinka, kuma ka yanke (ƙauna daga kowa ka koma) zuwa gare Shi, yankewa.0 Views
- رَّبُّ الْمَشْرِقِ وَالْمَغْرِبِ لَا إِلَـٰهَ إِلَّا هُوَ فَاتَّخِذْهُ وَكِيلًاShi ne Ubangijin mafitar rãnã da mafãɗarta, bãbu abin bautawa fãce Shi. Sabõda haka ka riƙe Shi wakili.0 Views
- وَاصْبِرْ عَلَىٰ مَا يَقُولُونَ وَاهْجُرْهُمْ هَجْرًا جَمِيلًاKuma ka yi haƙuri ga abin da suke faɗã, kuma ka ƙaurace musu, ƙauracẽwa mai kyãwo.3 Views
- وَذَرْنِي وَالْمُكَذِّبِينَ أُولِي النَّعْمَةِ وَمَهِّلْهُمْ قَلِيلًاKuma ka bar Ni da mãsu ƙaryatãwa, mawadãta, kuma ka jinkirta musu kaɗan.3 Views
- إِنَّ لَدَيْنَا أَنكَالًا وَجَحِيمًاLalle ne, a wurinMu, akwai wasu marũruwa mãsu nauyi da Jahĩm.0 Views
- وَطَعَامًا ذَا غُصَّةٍ وَعَذَابًا أَلِيمًاDa wani abinci mai mãƙara da azãba mai raɗaɗi.0 Views
- يَوْمَ تَرْجُفُ الْأَرْضُ وَالْجِبَالُ وَكَانَتِ الْجِبَالُ كَثِيبًا مَّهِيلًاRãnar da ƙasa ke raurawa, da duwãtsu kuma duwãtsu su kasance tudun rairayi mai malãlã.0 Views
- إِنَّا أَرْسَلْنَا إِلَيْكُمْ رَسُولًا شَاهِدًا عَلَيْكُمْ كَمَا أَرْسَلْنَا إِلَىٰ فِرْعَوْنَ رَسُولًاLalle ne, Mũ. Mun aika zuwa gare ku, wani Manzo mai shaida a kanku, kamar yadda Muka aika wani Manzo zuwaga Fir'auna,0 Views
- فَعَصَىٰ فِرْعَوْنُ الرَّسُولَ فَأَخَذْنَاهُ أَخْذًا وَبِيلًاSai Fir'auna ya saɓa wa Manzon, saboda haka Muka kãma shi kãmu mai tsanani.0 Views
- فَكَيْفَ تَتَّقُونَ إِن كَفَرْتُمْ يَوْمًا يَجْعَلُ الْوِلْدَانَ شِيبًاTo, yãya, idan kun kãfirta, zã ku kãre (azabar) wani yini mai mayar da yãra (tsofaffi) mãsu hurhura.0 Views
- السَّمَاءُ مُنفَطِرٌ بِهِ ۚ كَانَ وَعْدُهُ مَفْعُولًاSama za ta tsãge a cikinsa, wa'adinsa yã kasance mai aukuwa.0 Views
- إِنَّ هَـٰذِهِ تَذْكِرَةٌ ۖ فَمَن شَاءَ اتَّخَذَ إِلَىٰ رَبِّهِ سَبِيلًاLalle ne, wannan wata tunãtarwa ce, sai dai wanda ya so, ya kãma hanyar ƙwarai zuwa ga Ubangijinsa.0 Views