Mushaf Page 575
صفحة ٥٧٥
- Ghunnah
- Qalqalah
- Ikhfa (Haqiqi)
- Ikhfa Shafawi
- Idgham with Ghunnah
- Idgham without Ghunnah
- Idgham Shafawi (Mimi)
- Madd Lazim (6 counts)
- Madd Wajib Muttasil (4-5 counts)
- Madd Jaiz Munfasil (2, 4, 6 counts)
Each word’s meaning appears right below it; the transliteration follows below the words.
Surah al-muzzammil
- ۞ إِنَّ رَبَّكَ يَعْلَمُ أَنَّكَ تَقُومُ أَدْنَىٰ مِن ثُلُثَيِ اللَّيْلِ وَنِصْفَهُ وَثُلُثَهُ وَطَائِفَةٌ مِّنَ الَّذِينَ مَعَكَ ۚ وَاللَّهُ يُقَدِّرُ اللَّيْلَ وَالنَّهَارَ ۚ عَلِمَ أَن لَّن تُحْصُوهُ فَتَابَ عَلَيْكُمْ ۖ فَاقْرَءُوا مَا تَيَسَّرَ مِنَ الْقُرْآنِ ۚ عَلِمَ أَن سَيَكُونُ مِنكُم مَّرْضَىٰ ۙ وَآخَرُونَ يَضْرِبُونَ فِي الْأَرْضِ يَبْتَغُونَ مِن فَضْلِ اللَّهِ ۙ وَآخَرُونَ يُقَاتِلُونَ فِي سَبِيلِ اللَّهِ ۖ فَاقْرَءُوا مَا تَيَسَّرَ مِنْهُ ۚ وَأَقِيمُوا الصَّلَاةَ وَآتُوا الزَّكَاةَ وَأَقْرِضُوا اللَّهَ قَرْضًا حَسَنًا ۚ وَمَا تُقَدِّمُوا لِأَنفُسِكُم مِّنْ خَيْرٍ تَجِدُوهُ عِندَ اللَّهِ هُوَ خَيْرًا وَأَعْظَمَ أَجْرًا ۚ وَاسْتَغْفِرُوا اللَّهَ ۖ إِنَّ اللَّهَ غَفُورٌ رَّحِيمٌLalle ne, Ubangijinka Yã sani cẽwa, kai kana tsayuwa a kusan kashi biyu daga uku na dare, da rabinsa, da sulusinsa, tãre da wani ɓangare na waɗanda ke tãre da kai. Allah Yake iya ƙaddara dare da yini, Ya san bã zã ku iya lissafa shi ba, sabõda haka Ya karɓi tubarku sai, ku karanta abin da ya sauƙaƙa na Alƙur'ãni. Ya san wasu daga cikinku, zã su yi cĩwo, kuma wasu zã su yi tafiya cikin ƙasa suna nẽman falalar Allah da fatauci, kuma wasu zã su yi yãƙi a cikin banyar Allah. Sabõda haka ku karanta abin da ya sauƙaƙa daga gare shi, kuma ku tsai da salla kuma ku bãyar da zakka, kumaa ku bai wa Allah rance, rance mai kyãwo. Kuma abin da kuka gabatar dõmin kanku, na alhẽri, zã ku sãme shi a wurin Allah zai kasance mafifici (daga wanda kuka ajiye) kuma zai fi girma ga sakamako, kuma ku rõƙi Allah gãfara; lalle ne Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙai.2 Views
Surah al-muddaththir
Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
- يَا أَيُّهَا الْمُدَّثِّرُYã wanda ya lulluɓa da mayãfi.3 Views
- قُمْ فَأَنذِرْKa tãshi dõmin ka yi gargaɗi3 Views
- وَرَبَّكَ فَكَبِّرْKuma Ubangijinka, sai ka girmama Shi,3 Views
- وَثِيَابَكَ فَطَهِّرْKuma tutãfinka, sai ka tsarkake su,3 Views
- وَالرُّجْزَ فَاهْجُرْKuma gumãka, sai ka ƙaurace musu.3 Views
- وَلَا تَمْنُن تَسْتَكْثِرُKada ka yi kyauta kana nẽman ƙãri3 Views
- وَلِرَبِّكَ فَاصْبِرْKuma sabõda Ubangijinka? Sai ka yi haƙure3 Views
- فَإِذَا نُقِرَ فِي النَّاقُورِTo, idan aka yi bũsa a cikin ƙaho.0 Views
- فَذَٰلِكَ يَوْمَئِذٍ يَوْمٌ عَسِيرٌTo, wannan, a rãnar nan, yini ne mai wuya0 Views
- عَلَى الْكَافِرِينَ غَيْرُ يَسِيرٍA kan kãfirai, bã mai sauƙi ba ne.0 Views
- ذَرْنِي وَمَنْ خَلَقْتُ وَحِيدًاKa bar Ni da wanda Na halitta, yana shi kaɗai,0 Views
- وَجَعَلْتُ لَهُ مَالًا مَّمْدُودًاKuma Na sanya masa dũkiya shimfiɗaɗɗiya0 Views
- وَبَنِينَ شُهُودًاDa ɗiyã halartattu,0 Views
- وَمَهَّدتُّ لَهُ تَمْهِيدًاKuma Na shimfiɗa? masa kõme shimfiɗãwa.0 Views
- ثُمَّ يَطْمَعُ أَنْ أَزِيدَSa'an nan, yanã kwaɗayin in yi masa ƙãri!0 Views
- كَلَّا ۖ إِنَّهُ كَانَ لِآيَاتِنَا عَنِيدًاFaufau! Lalle ne, shĩ yã kasance, ga ãyõyinMu, mai tsaurin kai.0 Views
- سَأُرْهِقُهُ صَعُودًاZã Ni kallafa masa wahala mai hauhawa.0 Views