74. al-muddaththir
المدثر
Read Surah al-muddaththir in full: surah 74, 56 verses, Meccan, Juz 29. Arabic text with Hausa translation.
- Ghunnah
- Qalqalah
- Ikhfa (Haqiqi)
- Ikhfa Shafawi
- Idgham with Ghunnah
- Idgham without Ghunnah
- Idgham Shafawi (Mimi)
- Madd Lazim (6 counts)
- Madd Wajib Muttasil (4-5 counts)
- Madd Jaiz Munfasil (2, 4, 6 counts)
Each word’s meaning appears right below it; the transliteration follows below the words.
Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
- يَا أَيُّهَا الْمُدَّثِّرُYã wanda ya lulluɓa da mayãfi.3 Views
- قُمْ فَأَنذِرْKa tãshi dõmin ka yi gargaɗi3 Views
- وَرَبَّكَ فَكَبِّرْKuma Ubangijinka, sai ka girmama Shi,3 Views
- وَثِيَابَكَ فَطَهِّرْKuma tutãfinka, sai ka tsarkake su,3 Views
- وَالرُّجْزَ فَاهْجُرْKuma gumãka, sai ka ƙaurace musu.3 Views
- وَلَا تَمْنُن تَسْتَكْثِرُKada ka yi kyauta kana nẽman ƙãri3 Views
- وَلِرَبِّكَ فَاصْبِرْKuma sabõda Ubangijinka? Sai ka yi haƙure3 Views
- فَإِذَا نُقِرَ فِي النَّاقُورِTo, idan aka yi bũsa a cikin ƙaho.0 Views
- فَذَٰلِكَ يَوْمَئِذٍ يَوْمٌ عَسِيرٌTo, wannan, a rãnar nan, yini ne mai wuya0 Views
- عَلَى الْكَافِرِينَ غَيْرُ يَسِيرٍA kan kãfirai, bã mai sauƙi ba ne.0 Views
- ذَرْنِي وَمَنْ خَلَقْتُ وَحِيدًاKa bar Ni da wanda Na halitta, yana shi kaɗai,0 Views
- وَجَعَلْتُ لَهُ مَالًا مَّمْدُودًاKuma Na sanya masa dũkiya shimfiɗaɗɗiya0 Views
- وَبَنِينَ شُهُودًاDa ɗiyã halartattu,0 Views
- وَمَهَّدتُّ لَهُ تَمْهِيدًاKuma Na shimfiɗa? masa kõme shimfiɗãwa.0 Views
- ثُمَّ يَطْمَعُ أَنْ أَزِيدَSa'an nan, yanã kwaɗayin in yi masa ƙãri!0 Views
- كَلَّا ۖ إِنَّهُ كَانَ لِآيَاتِنَا عَنِيدًاFaufau! Lalle ne, shĩ yã kasance, ga ãyõyinMu, mai tsaurin kai.0 Views
- سَأُرْهِقُهُ صَعُودًاZã Ni kallafa masa wahala mai hauhawa.0 Views
- إِنَّهُ فَكَّرَ وَقَدَّرَLalle ne, Shi, yã yi tunãni, kuma yã ƙaddara (abin da zai faɗã game da Alƙur'ãni)0 Views
- فَقُتِلَ كَيْفَ قَدَّرَSabõda haka, aka la'ane shi, kamar yadda ya ƙaddara.0 Views
- ثُمَّ قُتِلَ كَيْفَ قَدَّرَSa'an nan, aka la'ane shi kamar yadda ya ƙaddara.0 Views
- ثُمَّ نَظَرَSa'an nan, ya yi tunãni0 Views
- ثُمَّ عَبَسَ وَبَسَرَSa'an nan, ya gintse huska? kuma ya yi murtuk.0 Views
- ثُمَّ أَدْبَرَ وَاسْتَكْبَرَSa'an nan, ya jũya bãya, kuma ya bunƙãsa,0 Views
- فَقَالَ إِنْ هَـٰذَا إِلَّا سِحْرٌ يُؤْثَرُSai ya ce: "Wannan abu dai bã kõme ba ne fãce wani sihiri, wanda aka ruwaito."0 Views
- إِنْ هَـٰذَا إِلَّا قَوْلُ الْبَشَرِ"Wannan maganar mutum dai ce."0 Views
- سَأُصْلِيهِ سَقَرَZã Ni ƙõna shi da Saƙar.0 Views
- وَمَا أَدْرَاكَ مَا سَقَرُKuma mẽ ya sanar da kai abin da akẽ cẽwa Saƙar!0 Views
- لَا تُبْقِي وَلَا تَذَرُBã ta ragẽwa, kuma bã ta bari.0 Views
- لَوَّاحَةٌ لِّلْبَشَرِMai nãcẽwa ga jiki ce (da (ƙũna).0 Views
- عَلَيْهَا تِسْعَةَ عَشَرَA kanta akwai (matsara) gõma shã tara.0 Views
- وَمَا جَعَلْنَا أَصْحَابَ النَّارِ إِلَّا مَلَائِكَةً ۙ وَمَا جَعَلْنَا عِدَّتَهُمْ إِلَّا فِتْنَةً لِّلَّذِينَ كَفَرُوا لِيَسْتَيْقِنَ الَّذِينَ أُوتُوا الْكِتَابَ وَيَزْدَادَ الَّذِينَ آمَنُوا إِيمَانًا ۙ وَلَا يَرْتَابَ الَّذِينَ أُوتُوا الْكِتَابَ وَالْمُؤْمِنُونَ ۙ وَلِيَقُولَ الَّذِينَ فِي قُلُوبِهِم مَّرَضٌ وَالْكَافِرُونَ مَاذَا أَرَادَ اللَّهُ بِهَـٰذَا مَثَلًا ۚ كَذَٰلِكَ يُضِلُّ اللَّهُ مَن يَشَاءُ وَيَهْدِي مَن يَشَاءُ ۚ وَمَا يَعْلَمُ جُنُودَ رَبِّكَ إِلَّا هُوَ ۚ وَمَا هِيَ إِلَّا ذِكْرَىٰ لِلْبَشَرِKuma ba Mu sanya ma'abũta wutã (wãto matsaranta) ba, fãce malã'iku, kuma ba Mu sanya adadinsu (gõma sha tara) ba, fãce dõmin fitina ga waɗanda suka kãfirta domin waɗanda aka bai wa littãfi su sãmi yaƙĩni kuma waɗanda suka yi ĩmãni su ƙãra ĩmãni, kuma waɗanda aka bai wa littãfi da mũminai bã zã su yi shakka ba, kuma domin wa ɗanda a cikin zukatansu akwai wata cuta da kãfirai su ce: "Mẽ Allah Yake nufi da wannan, ya kasance misãli?" Haka dai Allah ke ɓatar da wanda Ya so, kuma Ya shiryar da wanda ya so. Kuma bãbu wanda ya san mayãƙan Ubangijinka fãce Shi, kuma ita (wutar) ba ta kasance ba fãce wata tunãtarwa ce ga mutum.0 Views
- كَلَّا وَالْقَمَرِA'aha! Ina rantsuwa da watã.0 Views
- وَاللَّيْلِ إِذْ أَدْبَرَDa dare a lõkacin da ya jũyar da baya.0 Views
- وَالصُّبْحِ إِذَا أَسْفَرَDa sãfiya idan ta wãye.0 Views
- إِنَّهَا لَإِحْدَى الْكُبَرِIta (wutar) ɗayan manyan masĩfũ? ce.0 Views
- نَذِيرًا لِّلْبَشَرِMai gargaɗĩ ce ga mutum.0 Views
- لِمَن شَاءَ مِنكُمْ أَن يَتَقَدَّمَ أَوْ يَتَأَخَّرَGa wanda ya so, daga cikinku, ya gabãta ko ya jinkirta.0 Views
- كُلُّ نَفْسٍ بِمَا كَسَبَتْ رَهِينَةٌKõwane rai ga abin da ya aikata jingina ce.0 Views
- إِلَّا أَصْحَابَ الْيَمِينِFãce mutãnen dãma.0 Views
- فِي جَنَّاتٍ يَتَسَاءَلُونَA cikin Aljanna suna tambayar jũna.0 Views
- عَنِ الْمُجْرِمِينَGame da mãsu laifi.0 Views
- مَا سَلَكَكُمْ فِي سَقَرَ(Su ce musu) "Me ya shigar da ku a cikin Saƙar?"0 Views
- قَالُوا لَمْ نَكُ مِنَ الْمُصَلِّينَSuka ce: "Ba mu kasance munã a cikin mãsu salla ba."0 Views
- وَلَمْ نَكُ نُطْعِمُ الْمِسْكِينَ"Kuma ba mu kasance muna ciyar da matalautã ba."0 Views
- وَكُنَّا نَخُوضُ مَعَ الْخَائِضِينَ"Kuma mun kasance muna kũtsãwa tãre da mãsu kũtsãwa."0 Views
- وَكُنَّا نُكَذِّبُ بِيَوْمِ الدِّينِ"Mun kasance munã ƙaryata rãnar sãkamako."0 Views
- حَتَّىٰ أَتَانَا الْيَقِينُ"Har gaskiya (wãto mutuwa) ta zo mana."0 Views
- فَمَا تَنفَعُهُمْ شَفَاعَةُ الشَّافِعِينَSabõda haka cẽton mãsu cẽto bã zai amfãne su ba.0 Views
- فَمَا لَهُمْ عَنِ التَّذْكِرَةِ مُعْرِضِينَHaba! Me ya same su, suka zama mãsu bijirewa daga wa'azin gaskiya.0 Views
- كَأَنَّهُمْ حُمُرٌ مُّسْتَنفِرَةٌKamar dai sũ, jãkuna firgitattu ne.0 Views
- فَرَّتْ مِن قَسْوَرَةٍSun gudu daga zãki.0 Views
- بَلْ يُرِيدُ كُلُّ امْرِئٍ مِّنْهُمْ أَن يُؤْتَىٰ صُحُفًا مُّنَشَّرَةًA'aha! Kõwãne mutum daga cikinsu yanã son a zo masa da takardu (da sũnansa) ana wãtsãwa0 Views
- كَلَّا ۖ بَل لَّا يَخَافُونَ الْآخِرَةَA'aha! Kai dai, bã su jin tsõron Lãhira.0 Views
- كَلَّا إِنَّهُ تَذْكِرَةٌA'aha! Lalle ne, shi (Alƙur'ãni) tunãtarwa ce.0 Views
- فَمَن شَاءَ ذَكَرَهُDõmin wanda ya so, ya tuna.0 Views
- وَمَا يَذْكُرُونَ إِلَّا أَن يَشَاءَ اللَّهُ ۚ هُوَ أَهْلُ التَّقْوَىٰ وَأَهْلُ الْمَغْفِرَةِKuma bã zã su tuna ba fãce idan Allah Ya so, Shi ne Ya cancanta a bi Shi da taƙawa kuma Ya cancanta ga Ya yi gãfara.0 Views
Teks Al-Qur'an: Tanzil Project (https://tanzil.net), lisensi CC BY 3.0. · Abubakar Mahmoud Gumi (Tanzil Project, tanzil.net)