Mushaf Page 588
صفحة ٥٨٨
- Ghunnah
- Qalqalah
- Ikhfa (Haqiqi)
- Ikhfa Shafawi
- Idgham with Ghunnah
- Idgham without Ghunnah
- Idgham Shafawi (Mimi)
- Madd Lazim (6 counts)
- Madd Wajib Muttasil (4-5 counts)
- Madd Jaiz Munfasil (2, 4, 6 counts)
Each word’s meaning appears right below it; the transliteration follows below the words.
Surah al-mutaffifin
- كَلَّا إِنَّ كِتَابَ الْفُجَّارِ لَفِي سِجِّينٍHaƙĩƙa lalle ne littãfin fãjirai dãhir, yana a cikin Sijjĩn.1 Views
- وَمَا أَدْرَاكَ مَا سِجِّينٌKuma, mẽ ya sanar da kai abin da akẽ cẽ wa Sijjĩn?1 Views
- كِتَابٌ مَّرْقُومٌWani 1ittãfi ne rubũtacce.1 Views
- وَيْلٌ يَوْمَئِذٍ لِّلْمُكَذِّبِينَBone yã tabbata a rãnar nan ga mãsu ƙaryatãwa.1 Views
- الَّذِينَ يُكَذِّبُونَ بِيَوْمِ الدِّينِWaɗanda suke ƙaryatãwa game da rãnar sakamako.1 Views
- وَمَا يُكَذِّبُ بِهِ إِلَّا كُلُّ مُعْتَدٍ أَثِيمٍBabũ mai ƙaryatãwa gare shi fãce dukan mai ƙẽtare haddi mai yawan zunubi.1 Views
- إِذَا تُتْلَىٰ عَلَيْهِ آيَاتُنَا قَالَ أَسَاطِيرُ الْأَوَّلِينَIdan ana karãtun ãyõyinmu, a kansa, sai ya ce: tãtsũniyõyin mutãnen farko ne.1 Views
- كَلَّا ۖ بَلْ ۜ رَانَ عَلَىٰ قُلُوبِهِم مَّا كَانُوا يَكْسِبُونَA'aha! Bã haka ba, abin da suka kasance suna aikatãwa dai, yã yi tsãtsa a cikin zukãtãnsu.1 Views
- كَلَّا إِنَّهُمْ عَن رَّبِّهِمْ يَوْمَئِذٍ لَّمَحْجُوبُونَA'aha! Haƙĩƙa, lalle ne sũ daga Ubangijinsu, rãnar nan, waɗanda ake shãmakancẽwa ne.1 Views
- ثُمَّ إِنَّهُمْ لَصَالُو الْجَحِيمِSa'an nan, lalle ne, sũ mãsu shiga cikin Jahĩm ne.1 Views
- ثُمَّ يُقَالُ هَـٰذَا الَّذِي كُنتُم بِهِ تُكَذِّبُونَSa'an nan a ce: "Wannan shi ne abin da kuka kasance kuna ƙaryatãwa game da shi."1 Views
- كَلَّا إِنَّ كِتَابَ الْأَبْرَارِ لَفِي عِلِّيِّينَA'aha! Haƙĩƙa lalle ne littãfin mãsu ɗã'ã yana a cikin Illiyyĩna?1 Views
- وَمَا أَدْرَاكَ مَا عِلِّيُّونَKuma mẽne ne yã sanar da kai abin da ake cẽwa Illiyyũna?1 Views
- كِتَابٌ مَّرْقُومٌWani littãfi ne rubũtacce.1 Views
- يَشْهَدُهُ الْمُقَرَّبُونَMuƙarrabai suke halarta shi.1 Views
- إِنَّ الْأَبْرَارَ لَفِي نَعِيمٍLalle ne, mãsu ɗã'ã ga Allah tabbas suna cikin ni'ima.1 Views
- عَلَى الْأَرَائِكِ يَنظُرُونَA kan karagu, suna ta kallo.1 Views
- تَعْرِفُ فِي وُجُوهِهِمْ نَضْرَةَ النَّعِيمِKana sani a cikin huskõkinsu, akwai kwarjinin ni'ima.1 Views
- يُسْقَوْنَ مِن رَّحِيقٍ مَّخْتُومٍAna shãyar da sũ daga wata giya wadda aka yunƙe a kan rufinta.1 Views
- خِتَامُهُ مِسْكٌ ۚ وَفِي ذَٰلِكَ فَلْيَتَنَافَسِ الْمُتَنَافِسُونَ¡arshen kurɓinta miski ne. To, a cikin wannan, mãsu gwagwarmaya su yi ta gwagwarmayar nẽma.1 Views
- وَمِزَاجُهُ مِن تَسْنِيمٍKuma abin da ake gauraya ta da shi, daga tasnĩm yake.1 Views
- عَيْنًا يَشْرَبُ بِهَا الْمُقَرَّبُونَ(Wato) wani marmaro ne wanda muƙarrabai ke sha daga gare shi.1 Views
- إِنَّ الَّذِينَ أَجْرَمُوا كَانُوا مِنَ الَّذِينَ آمَنُوا يَضْحَكُونَLalle ne, waɗanda suka kãfirta sun kasance (a dũniya) suna yi wa waɗanda suka yi ĩmãni dãriya.4 Views
- وَإِذَا مَرُّوا بِهِمْ يَتَغَامَزُونَKuma idan sun shuɗe su sai su dinga yin zunɗe.4 Views
- وَإِذَا انقَلَبُوا إِلَىٰ أَهْلِهِمُ انقَلَبُوا فَكِهِينَKuma idan suka jũya zuwa ga iyãlansu, sai su tafi suna kãkãci.4 Views
- وَإِذَا رَأَوْهُمْ قَالُوا إِنَّ هَـٰؤُلَاءِ لَضَالُّونَKuma idan sun gan su sai su ce: "Lalle waɗannan ɓatattu ne."4 Views
- وَمَا أُرْسِلُوا عَلَيْهِمْ حَافِظِينَAlhãli kuwa, ba a aike su ba dõmin su zama mãsu tsaro a kansu.1 Views
- فَالْيَوْمَ الَّذِينَ آمَنُوا مِنَ الْكُفَّارِ يَضْحَكُونَTo, yau fa (a Lãhira] waɗanda suka yi ĩmãni, sũ ke yi wa kãfirai dãriya.1 Views