Mushaf Page 599
صفحة ٥٩٩
- Ghunnah
- Qalqalah
- Ikhfa (Haqiqi)
- Ikhfa Shafawi
- Idgham with Ghunnah
- Idgham without Ghunnah
- Idgham Shafawi (Mimi)
- Madd Lazim (6 counts)
- Madd Wajib Muttasil (4-5 counts)
- Madd Jaiz Munfasil (2, 4, 6 counts)
Each word’s meaning appears right below it; the transliteration follows below the words.
Surah al-bayyinah
- جَزَاؤُهُمْ عِندَ رَبِّهِمْ جَنَّاتُ عَدْنٍ تَجْرِي مِن تَحْتِهَا الْأَنْهَارُ خَالِدِينَ فِيهَا أَبَدًا ۖ رَّضِيَ اللَّهُ عَنْهُمْ وَرَضُوا عَنْهُ ۚ ذَٰلِكَ لِمَنْ خَشِيَ رَبَّهُSakamakonsu, a wurin Ubangijinsu, shi ne gidajen Aljannar zama, ƙoramu na gudãna daga ƙarƙashinsu sunã madawwama a cikinta har abada. Allah Ya yarda da su, kuma su, sun yarda da Shi. wannan sakamako ne ga wanda ya ji tsõron Ubangijinsa.2 Views
Surah az-zalzalah
Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
- إِذَا زُلْزِلَتِ الْأَرْضُ زِلْزَالَهَاIdan aka girgiza ƙasa, girgizawarta.0 Views
- وَأَخْرَجَتِ الْأَرْضُ أَثْقَالَهَاKuma ƙasa ta fitar da kayanta, masu nauyi.0 Views
- وَقَالَ الْإِنسَانُ مَا لَهَاKuma mutum ya ce "Mẽ neya same ta?"0 Views
- يَوْمَئِذٍ تُحَدِّثُ أَخْبَارَهَاA rãnar nan, zã ta faɗi lãbãrinta.0 Views
- بِأَنَّ رَبَّكَ أَوْحَىٰ لَهَاcewa Ubangijinka Ya yi umurni zuwa gare ta.0 Views
- يَوْمَئِذٍ يَصْدُرُ النَّاسُ أَشْتَاتًا لِّيُرَوْا أَعْمَالَهُمْA rãnar nan mutane za su fito dabam-dabam domin a nuna musu ayyukansu.0 Views
- فَمَن يَعْمَلْ مِثْقَالَ ذَرَّةٍ خَيْرًا يَرَهُTo, wanda ya aikata (wani aiki) gwargwadon nauyin zarra, na alheri, zai gan shi.0 Views
- وَمَن يَعْمَلْ مِثْقَالَ ذَرَّةٍ شَرًّا يَرَهُKuma wanda ya aikata gwargwadon nauyin zarra na sharri, zai gan shi.0 Views
Surah al-adiyat
Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
- وَالْعَادِيَاتِ ضَبْحًاIna rantsuwa da dawãki mãsu gudu suna fitar da kũkan ciki.0 Views
- فَالْمُورِيَاتِ قَدْحًاMãsu ƙyasta wuta (da kõfatansu a kan duwatsu) ƙyastawa.0 Views
- فَالْمُغِيرَاتِ صُبْحًاSa'an nan mãsu yin hari a lokacin asuba.0 Views
- فَأَثَرْنَ بِهِ نَقْعًاSai su motsar da ƙũra game da shi.0 Views
- فَوَسَطْنَ بِهِ جَمْعًاSai su shiga, game da ita (ƙũrar), a tsakãnin jama'ar maƙiya.0 Views
- إِنَّ الْإِنسَانَ لِرَبِّهِ لَكَنُودٌLalle ne mutum mai tsananin butulci ne ga Ubangijinsa.0 Views
- وَإِنَّهُ عَلَىٰ ذَٰلِكَ لَشَهِيدٌLalle ne shi mai shaida ne a kan laifinsa dl haka.0 Views
- وَإِنَّهُ لِحُبِّ الْخَيْرِ لَشَدِيدٌKuma 1alle ne ga dũkiya shi mai tsananin so ne.0 Views
- ۞ أَفَلَا يَعْلَمُ إِذَا بُعْثِرَ مَا فِي الْقُبُورِShin, bã ya da sanin lõkacin da aka tõne abin da yake cikin kaburbura.0 Views