44. ad-dukhan
الدخان
Read Surah ad-dukhan in full: surah 44, 59 verses, Meccan, Juz 25. Arabic text with Hausa translation.
- Ghunnah
- Qalqalah
- Ikhfa (Haqiqi)
- Ikhfa Shafawi
- Idgham with Ghunnah
- Idgham without Ghunnah
- Idgham Shafawi (Mimi)
- Madd Lazim (6 counts)
- Madd Wajib Muttasil (4-5 counts)
- Madd Jaiz Munfasil (2, 4, 6 counts)
Each word’s meaning appears right below it; the transliteration follows below the words.
Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
- حمٓḤ. M̃.0 Views
- وَالْكِتَابِ الْمُبِينِInã rantsuwa da Littãfi Mabayyani.0 Views
- إِنَّا أَنزَلْنَاهُ فِي لَيْلَةٍ مُّبَارَكَةٍ ۚ إِنَّا كُنَّا مُنذِرِينَLalle ne, Mũ, Muka saukar da shi a cikin wani dare mai albarka. Lalle Mũ' Mun kasance Mãsu yin gargaɗi.0 Views
- فِيهَا يُفْرَقُ كُلُّ أَمْرٍ حَكِيمٍA cikinsa (shi daren) ake rarrabe kõwane umurui bayyananne.0 Views
- أَمْرًا مِّنْ عِندِنَا ۚ إِنَّا كُنَّا مُرْسِلِينَUmurni na daga wurinMu. Lalle Mũ ne Muka kasanceMãsu aikãwã.0 Views
- رَحْمَةً مِّن رَّبِّكَ ۚ إِنَّهُ هُوَ السَّمِيعُ الْعَلِيمُSabõda rahama daga Ubangijinka. Lalle Shĩ, Shi ne Mai ji, Mãsani.0 Views
- رَبِّ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ وَمَا بَيْنَهُمَا ۖ إِن كُنتُم مُّوقِنِينَ(Shĩ ne) Ubangijin sammai da ƙasa da abin da ke a tsakãninsu, idan kun kasance mãsu yaƙĩni (za ku gãne haka).0 Views
- لَا إِلَـٰهَ إِلَّا هُوَ يُحْيِي وَيُمِيتُ ۖ رَبُّكُمْ وَرَبُّ آبَائِكُمُ الْأَوَّلِينَBabu abin bautãwa fãce Shi. Yana rãyarwa Kuma Yana kashẽwa. (Shi ne) Ubangijinku, kuma Ubangijin ubanninku na farko.0 Views
- بَلْ هُمْ فِي شَكٍّ يَلْعَبُونَA'a sũ, sunã wãsã a cikin shakka.0 Views
- فَارْتَقِبْ يَوْمَ تَأْتِي السَّمَاءُ بِدُخَانٍ مُّبِينٍSabõda haka, ka dakata rãnar da sama zã tã zo da hayãƙi bayyananne.0 Views
- يَغْشَى النَّاسَ ۖ هَـٰذَا عَذَابٌ أَلِيمٌYanã rufe mutãne. Wannan wata azãba ce mai raɗaɗi.0 Views
- رَّبَّنَا اكْشِفْ عَنَّا الْعَذَابَ إِنَّا مُؤْمِنُونَYa Ubangijinmu! Ka kuranye mana azãba. Lalle Mũ, mãsu ĩmãni ne.0 Views
- أَنَّىٰ لَهُمُ الذِّكْرَىٰ وَقَدْ جَاءَهُمْ رَسُولٌ مُّبِينٌInã tunãwa take a gare su, alhãli kuwa, haƙĩƙa, Manzo mai bayyanãwa Ya je musu (da gargaɗin saukar azãbar, ba su karɓa ba)?0 Views
- ثُمَّ تَوَلَّوْا عَنْهُ وَقَالُوا مُعَلَّمٌ مَّجْنُونٌSa'an nan suka jũya baya daga gare shi, Kuma suka ce: "Wanda ake gayãwa ne, mahaukaci."0 Views
- إِنَّا كَاشِفُو الْعَذَابِ قَلِيلًا ۚ إِنَّكُمْ عَائِدُونَLalle Mũ, Mãsu kuranyẽwar azãba ne, a ɗan lõkaci kaɗan, lalle kũ, mãsu kõmãwa ne (ga laifin).0 Views
- يَوْمَ نَبْطِشُ الْبَطْشَةَ الْكُبْرَىٰ إِنَّا مُنتَقِمُونَRãnar da Muke damƙa, damƙa mafi girma, lalle ne Mũ mãsu azãbar rãmuwa ne.0 Views
- ۞ وَلَقَدْ فَتَنَّا قَبْلَهُمْ قَوْمَ فِرْعَوْنَ وَجَاءَهُمْ رَسُولٌ كَرِيمٌKuma lalle ne haƙĩƙa a gabaninsu, Mun fitini mutãnen Fir'auna, kuma wani Manzo karĩmi ya jẽ musu.0 Views
- أَنْ أَدُّوا إِلَيَّ عِبَادَ اللَّهِ ۖ إِنِّي لَكُمْ رَسُولٌ أَمِينٌ(Mazon ya ce): "Ku kãwo mini (ĩmãninku) ya bayin Allah! Lalle ni, Manzo ne amintacce zuwa gare ku."0 Views
- وَأَن لَّا تَعْلُوا عَلَى اللَّهِ ۖ إِنِّي آتِيكُم بِسُلْطَانٍ مُّبِينٍ"Kuma kada ku nẽmi ɗaukaka a kan Allah. Lalle nĩ mai zo muku ne da dalĩli bayyananne."0 Views
- وَإِنِّي عُذْتُ بِرَبِّي وَرَبِّكُمْ أَن تَرْجُمُونِ"Kuma lalle nĩ na nẽmi tsari da Ubangijĩna, kuma Ubangijinku, dõmin kada ku jẽfe ni."0 Views
- وَإِن لَّمْ تُؤْمِنُوا لِي فَاعْتَزِلُونِ"Kuma idan ba ku yi ĩmãni sabõda nĩ ba, to, ku nĩsance ni."0 Views
- فَدَعَا رَبَّهُ أَنَّ هَـٰؤُلَاءِ قَوْمٌ مُّجْرِمُونَSai ya kirayi Ubangjinsa cẽwa waɗannan mutãnene mãsu laifi.0 Views
- فَأَسْرِ بِعِبَادِي لَيْلًا إِنَّكُم مُّتَّبَعُونَ(Allah Ya ce): "To, ka yi tafiyar dare da bayiNa, da dare. Lalle kũ, waɗanda ake bĩ ne (dõmin a kãma ku.)"0 Views
- وَاتْرُكِ الْبَحْرَ رَهْوًا ۖ إِنَّهُمْ جُندٌ مُّغْرَقُونَ"Kuma ka bar tẽku rarrabe. Lalle sũ, runduna ce abar nutsarwa."0 Views
- كَمْ تَرَكُوا مِن جَنَّاتٍ وَعُيُونٍDa yawa suka bar gõnaki da marẽmari.0 Views
- وَزُرُوعٍ وَمَقَامٍ كَرِيمٍDa shuke-shuke da matsayi mai kyau.0 Views
- وَنَعْمَةٍ كَانُوا فِيهَا فَاكِهِينَDa wata ni'ima da suka kasance a cikinta sunã mãsu hutu.0 Views
- كَذَٰلِكَ ۖ وَأَوْرَثْنَاهَا قَوْمًا آخَرِينَKamar haka! Kuma Muka gãdar da ita ga waɗansu mutãne na dabam.0 Views
- فَمَا بَكَتْ عَلَيْهِمُ السَّمَاءُ وَالْأَرْضُ وَمَا كَانُوا مُنظَرِينَSa'an nan samã da ƙasã ba su yi kũka a kansu ba, Kuma ba su kasance waɗanda ake yi wa jinkiri ba.0 Views
- وَلَقَدْ نَجَّيْنَا بَنِي إِسْرَائِيلَ مِنَ الْعَذَابِ الْمُهِينِKuma lalle ne, haƙĩƙa Mun tsĩrar da Banĩ Isrã'ĩla daga, azãba mai wulãkantãwa.0 Views
- مِن فِرْعَوْنَ ۚ إِنَّهُ كَانَ عَالِيًا مِّنَ الْمُسْرِفِينَDaga Fir'auna. Lalle shi, ya kasance maɗaukaki daga cikin mãsu ɓarna.0 Views
- وَلَقَدِ اخْتَرْنَاهُمْ عَلَىٰ عِلْمٍ عَلَى الْعَالَمِينَKuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun zãɓe su sabõda wani ilmi (na Taurata) a kan mutãne.0 Views
- وَآتَيْنَاهُم مِّنَ الْآيَاتِ مَا فِيهِ بَلَاءٌ مُّبِينٌKuma Muka bã su, daga ãyõyin mu'ujizõji, abin da yake a cikinsa, akwai ni'ima bayyananna0 Views
- إِنَّ هَـٰؤُلَاءِ لَيَقُولُونَLalle waɗannan mutãne, haƙĩka, sunã cẽwa,0 Views
- إِنْ هِيَ إِلَّا مَوْتَتُنَا الْأُولَىٰ وَمَا نَحْنُ بِمُنشَرِينَ"Babu wani abu sai mutuwarmu ta farko, kuma ba mu zama waɗanda ake tãyarwa ba."0 Views
- فَأْتُوا بِآبَائِنَا إِن كُنتُمْ صَادِقِينَ"Sai ku zo da ubanninmu, idan kun kasance mãsu gaskiya."0 Views
- أَهُمْ خَيْرٌ أَمْ قَوْمُ تُبَّعٍ وَالَّذِينَ مِن قَبْلِهِمْ ۚ أَهْلَكْنَاهُمْ ۖ إِنَّهُمْ كَانُوا مُجْرِمِينَshin, sũ ne mafĩfĩta kõ kuwa mutãnen Tubba'u, kuma da waɗanda ke a gabãninsu? Mun halaka su, lalle sũ, sun kasance mãsu laifi.0 Views
- وَمَا خَلَقْنَا السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضَ وَمَا بَيْنَهُمَا لَاعِبِينَKuma ba Mu halitta slmmai da ƙasa da abin da ke a tsakãninsu ba, alhãli kuwa Munã mãsu wãsã.0 Views
- مَا خَلَقْنَاهُمَا إِلَّا بِالْحَقِّ وَلَـٰكِنَّ أَكْثَرَهُمْ لَا يَعْلَمُونَBa Mu halitta su ba fãce da manufa ta gaskiya, kuma amma mafi yawansu, ba su sani ba.0 Views
- إِنَّ يَوْمَ الْفَصْلِ مِيقَاتُهُمْ أَجْمَعِينَLalle rãnar rarrabẽwa, ita ce lõkacin wa'adinsu gabã ɗaya.0 Views
- يَوْمَ لَا يُغْنِي مَوْلًى عَن مَّوْلًى شَيْئًا وَلَا هُمْ يُنصَرُونَRãnar da wani zumu bã ya amfãnin wani zumu da kõme kuma ba su zama anã taimakon su ba.0 Views
- إِلَّا مَن رَّحِمَ اللَّهُ ۚ إِنَّهُ هُوَ الْعَزِيزُ الرَّحِيمُfãce wanda Allah Ya yi wa rahama. Lalle Shi (Allah), shĩ ne Mabuwãyi, Mai jin ƙai.0 Views
- إِنَّ شَجَرَتَ الزَّقُّومِLalle itãciyar zaƙƙũm (ɗanyen wutã),0 Views
- طَعَامُ الْأَثِيمِIta ce abincin mai laifi.0 Views
- كَالْمُهْلِ يَغْلِي فِي الْبُطُونِKamar narkakken kwalta yanã tafasa a cikin cikunna.0 Views
- كَغَلْيِ الْحَمِيمِKamar tafasar ruwan zãfi.0 Views
- خُذُوهُ فَاعْتِلُوهُ إِلَىٰ سَوَاءِ الْجَحِيمِ(A cẽ wa malã'ikun wutã), "Ku kãmã shi, sa'an nan ku fizge shi zuwa ga tsakiyar Jahĩm."0 Views
- ثُمَّ صُبُّوا فَوْقَ رَأْسِهِ مِنْ عَذَابِ الْحَمِيمِ"Sa'an nan ku zuba, a kansa, daga azãbar ruwan zãfi."0 Views
- ذُقْ إِنَّكَ أَنتَ الْعَزِيزُ الْكَرِيمُ(A ce masã), "Ka ɗanɗana! Lalle kai, kai ne mabuwãyi mai girma!"0 Views
- إِنَّ هَـٰذَا مَا كُنتُم بِهِ تَمْتَرُونَ"Lalle wannan, shi ne abin da kuka kasance kunã shakka game da shi."0 Views
- إِنَّ الْمُتَّقِينَ فِي مَقَامٍ أَمِينٍLalle mãsu taƙawa sunã cikin matsayi amintacce.0 Views
- فِي جَنَّاتٍ وَعُيُونٍA cikin gidãjen Aljanna da marẽmari.0 Views
- يَلْبَسُونَ مِن سُندُسٍ وَإِسْتَبْرَقٍ مُّتَقَابِلِينَSunã tufanta daga tufãfin alharĩni raƙĩƙi, da mai kauri, sunã mãsu zaman fuskantar jũna.0 Views
- كَذَٰلِكَ وَزَوَّجْنَاهُم بِحُورٍ عِينٍKamar haka, kuma Mun aurar da su da mãtã mãsu kyaun idãnu, mãsu girmansu.0 Views
- يَدْعُونَ فِيهَا بِكُلِّ فَاكِهَةٍ آمِنِينَSunã kira, a cikinsu (gidẽjen) ga dukan 'ya'yan itãcen marmari, sunã amintattu (daga dukan abin tsõro).0 Views
- لَا يَذُوقُونَ فِيهَا الْمَوْتَ إِلَّا الْمَوْتَةَ الْأُولَىٰ ۖ وَوَقَاهُمْ عَذَابَ الْجَحِيمِBã su ɗanɗanar mutuwa, a cikinsu, fãce mutuwar farko, kuma (Allah), Ya tsare musu azãbar Jahĩm.0 Views
- فَضْلًا مِّن رَّبِّكَ ۚ ذَٰلِكَ هُوَ الْفَوْزُ الْعَظِيمُSabõda falala daga Ubangijinka. Wancan shi ne babban rabo, mai girma.0 Views
- فَإِنَّمَا يَسَّرْنَاهُ بِلِسَانِكَ لَعَلَّهُمْ يَتَذَكَّرُونَDõmin haka kawai Muka sauƙaƙar da shi (Alƙur'ãni) da harshenka, tsammãninsu, su riƙa tunãwa.0 Views
- فَارْتَقِبْ إِنَّهُم مُّرْتَقِبُونَSai ka yi jira. Lalle sũ, mãsu jira ne.0 Views
Teks Al-Qur'an: Tanzil Project (https://tanzil.net), lisensi CC BY 3.0. · Abubakar Mahmoud Gumi (Tanzil Project, tanzil.net)