Juz 25
الجزء ٢٥
- Ghunnah
- Qalqalah
- Ikhfa (Haqiqi)
- Ikhfa Shafawi
- Idgham with Ghunnah
- Idgham without Ghunnah
- Idgham Shafawi (Mimi)
- Madd Lazim (6 counts)
- Madd Wajib Muttasil (4-5 counts)
- Madd Jaiz Munfasil (2, 4, 6 counts)
Each word’s meaning appears right below it; the transliteration follows below the words.
Surah fussilat
- ۞ إِلَيْهِ يُرَدُّ عِلْمُ السَّاعَةِ ۚ وَمَا تَخْرُجُ مِن ثَمَرَاتٍ مِّنْ أَكْمَامِهَا وَمَا تَحْمِلُ مِنْ أُنثَىٰ وَلَا تَضَعُ إِلَّا بِعِلْمِهِ ۚ وَيَوْمَ يُنَادِيهِمْ أَيْنَ شُرَكَائِي قَالُوا آذَنَّاكَ مَا مِنَّا مِن شَهِيدٍZuwa gare Shi ake mayar da sanin Sa'a. Kuma waɗansu 'yã'yan itãce bã su fita daga kwasfõfinsu, kuma wata mace bã ta yin ciki, kuma bã ta haihuwa, fãce da saninSa, kuma a rãnar da Yake kiran su (Ya ce): "Inã abõkan tãrayyaTa?" Sai su ce, "Mun sanar da Kai bãbu mai bãyar da shaida da haka nan daga gare mu."0 Views
- وَضَلَّ عَنْهُم مَّا كَانُوا يَدْعُونَ مِن قَبْلُ ۖ وَظَنُّوا مَا لَهُم مِّن مَّحِيصٍKuma abin da suka kasance sunã kira a gabãnin haka ya ɓace musu, kuma suka yi zaton cẽwa bã su da wata mafakã.0 Views
- لَّا يَسْأَمُ الْإِنسَانُ مِن دُعَاءِ الْخَيْرِ وَإِن مَّسَّهُ الشَّرُّ فَيَئُوسٌ قَنُوطٌMutum bã ya kõsãwa daga addu 'ar nẽman alhẽri kuma idan sharri ya shãfe shi, sai ya zama mai yanke kauna, Mai nũna kãsãwa.0 Views
- وَلَئِنْ أَذَقْنَاهُ رَحْمَةً مِّنَّا مِن بَعْدِ ضَرَّاءَ مَسَّتْهُ لَيَقُولَنَّ هَـٰذَا لِي وَمَا أَظُنُّ السَّاعَةَ قَائِمَةً وَلَئِن رُّجِعْتُ إِلَىٰ رَبِّي إِنَّ لِي عِندَهُ لَلْحُسْنَىٰ ۚ فَلَنُنَبِّئَنَّ الَّذِينَ كَفَرُوا بِمَا عَمِلُوا وَلَنُذِيقَنَّهُم مِّنْ عَذَابٍ غَلِيظٍKuma lalle idan Mun ɗanɗana masa wata rahama daga gareMu, daga bãyan wata cũta ta shãfe shi, lalle zai ce, "Wannan (ni'ima) tãwa ce kuma bã ni zaton Sã'a mai tsayuwa ce, kuma lalle idan aka mayar da ni zuwa ga Ubangijĩna, haƙĩƙa, inã da makõma mafi kyau, a wurinSa." To, lalle zã Mu bã da lãbãri ga waɗanda suka kãfirta game da abin da suka aikata, kuma lalle Munã ɗanɗana musu daga azãba, Mai kauri.0 Views
- وَإِذَا أَنْعَمْنَا عَلَى الْإِنسَانِ أَعْرَضَ وَنَأَىٰ بِجَانِبِهِ وَإِذَا مَسَّهُ الشَّرُّ فَذُو دُعَاءٍ عَرِيضٍKuma idan Muka yi ni'ima ga mutum, sai ya bijire, kuma ya nĩsantar da gẽfensa, kuma idan sharri ya sãme shi, sai ya zama ma'abũcin addu'a mai fãɗi.0 Views
- قُلْ أَرَأَيْتُمْ إِن كَانَ مِنْ عِندِ اللَّهِ ثُمَّ كَفَرْتُم بِهِ مَنْ أَضَلُّ مِمَّنْ هُوَ فِي شِقَاقٍ بَعِيدٍKa ce: "Ashe, kun gani! Idan (Alƙur'ãni) ya kasance daga Allah ne, sa'an nan kun kãfirta a game da Shi, wãne ne mafi ɓata daga wanda yake yanã a cikin sãɓani manisanci (daga gaskiya)?"0 Views
- سَنُرِيهِمْ آيَاتِنَا فِي الْآفَاقِ وَفِي أَنفُسِهِمْ حَتَّىٰ يَتَبَيَّنَ لَهُمْ أَنَّهُ الْحَقُّ ۗ أَوَلَمْ يَكْفِ بِرَبِّكَ أَنَّهُ عَلَىٰ كُلِّ شَيْءٍ شَهِيدٌZã Mu nũna musu ãyõyinMu a cikin sãsanni da kuma cikin rãyukansu, har ya bayyana a gare su cẽwã lalle (Alƙur'ãni), shi ne gaskiya. Ashe, kuma Ubangijinka bai isa ba, ga cẽwa lalle Shĩ halartacce ne a kan kowane abu ne?0 Views
- أَلَا إِنَّهُمْ فِي مِرْيَةٍ مِّن لِّقَاءِ رَبِّهِمْ ۗ أَلَا إِنَّهُ بِكُلِّ شَيْءٍ مُّحِيطٌTo lalle sũ, sunã a cikin shakka daga gamuwa da Ubangijinsu. To, lalle Shĩ, Mai kẽwayẽwane ga dukan kõme ne.0 Views
Surah ash-shura
Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
- حمٓḤ. M̃.0 Views
- عٓسٓقٓĨ. Ṣ̃.0 Views
- كَذَٰلِكَ يُوحِي إِلَيْكَ وَإِلَى الَّذِينَ مِن قَبْلِكَ اللَّهُ الْعَزِيزُ الْحَكِيمُKamar wancãn (asĩrin) Allah, Mabuwayi, Mai hikima, ke yin wahayi zuwa gare ka da zuwa ga waɗanda ke gabãninka.0 Views
- لَهُ مَا فِي السَّمَاوَاتِ وَمَا فِي الْأَرْضِ ۖ وَهُوَ الْعَلِيُّ الْعَظِيمُ(Allah) Shi ne da abin da ke cikin sammai da abin da ke cikin ƙasa, kuma Shi ne Maɗaukaki, Mai girma.0 Views
- تَكَادُ السَّمَاوَاتُ يَتَفَطَّرْنَ مِن فَوْقِهِنَّ ۚ وَالْمَلَائِكَةُ يُسَبِّحُونَ بِحَمْدِ رَبِّهِمْ وَيَسْتَغْفِرُونَ لِمَن فِي الْأَرْضِ ۗ أَلَا إِنَّ اللَّهَ هُوَ الْغَفُورُ الرَّحِيمُSammai nã kusan su tsãge daga bisansu, kuma malã'iku nã yin tasĩhi game da gõdẽ wa Ubangijinsu kuma sunã istigfãri dõmin wanda ke cikin ƙasa. To, lalle Allah Shĩ ne Mai gãfara, Mai jin ƙai.0 Views
- وَالَّذِينَ اتَّخَذُوا مِن دُونِهِ أَوْلِيَاءَ اللَّهُ حَفِيظٌ عَلَيْهِمْ وَمَا أَنتَ عَلَيْهِم بِوَكِيلٍKuma waɗanda suka riƙi waɗansu majiɓinta waɗanda bã Shĩ ba Allah ne Mai tsaro a kansu, kuma kai, bã wakili ne a kansu ba.0 Views
- وَكَذَٰلِكَ أَوْحَيْنَا إِلَيْكَ قُرْآنًا عَرَبِيًّا لِّتُنذِرَ أُمَّ الْقُرَىٰ وَمَنْ حَوْلَهَا وَتُنذِرَ يَوْمَ الْجَمْعِ لَا رَيْبَ فِيهِ ۚ فَرِيقٌ فِي الْجَنَّةِ وَفَرِيقٌ فِي السَّعِيرِKuma kamar haka ne Muka yi wahayin abin karãntãwa (Alƙur'ãni) na Lãrabci zuwa gare ka, dõmin ka yi gargaɗi ga Uwar Alƙaryu (Makka) da wanda ke a kẽwayenta, kuma ka yi gargaɗi game da rãnar taruwa, bãbu shakka gare ta, wata ƙungiya tanã a cikin Aljanna kuma wata ƙungiya tãna a cikin sa'ĩr.0 Views
- وَلَوْ شَاءَ اللَّهُ لَجَعَلَهُمْ أُمَّةً وَاحِدَةً وَلَـٰكِن يُدْخِلُ مَن يَشَاءُ فِي رَحْمَتِهِ ۚ وَالظَّالِمُونَ مَا لَهُم مِّن وَلِيٍّ وَلَا نَصِيرٍKuma dã Allah Ya so, da Ya haɗã su al'umma guda, kuma Amma Yanã shigar da wanda Ya so a cikin rahamarSa alhãli kuwa azzãluMai bã su da, wani majiɓinci, kuma bã su da wani mataimaki.0 Views
- أَمِ اتَّخَذُوا مِن دُونِهِ أَوْلِيَاءَ ۖ فَاللَّهُ هُوَ الْوَلِيُّ وَهُوَ يُحْيِي الْمَوْتَىٰ وَهُوَ عَلَىٰ كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌKõ kuma sun riƙi waninSa majiɓinta? To Allah Shĩ ne Majiɓinci, kuma Shĩ ne ke rãyar da matattu alhãli kuwa Shĩ, Maiĩkon yi ne a kan dukan kõme.0 Views
- وَمَا اخْتَلَفْتُمْ فِيهِ مِن شَيْءٍ فَحُكْمُهُ إِلَى اللَّهِ ۚ ذَٰلِكُمُ اللَّهُ رَبِّي عَلَيْهِ تَوَكَّلْتُ وَإِلَيْهِ أُنِيبُKuma abin da kuka sãɓã wa jũna a cikinsa kõ mêne ne, to, hukuncinsa (a mayar da shi) zuwa ga Allah. Wancan Shĩ ne Allah Ubangijĩna, a gare Shi na dõgara, kuma zuwa gare Shi nake mayar da al'amarĩna.0 Views
- فَاطِرُ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ ۚ جَعَلَ لَكُم مِّنْ أَنفُسِكُمْ أَزْوَاجًا وَمِنَ الْأَنْعَامِ أَزْوَاجًا ۖ يَذْرَؤُكُمْ فِيهِ ۚ لَيْسَ كَمِثْلِهِ شَيْءٌ ۖ وَهُوَ السَّمِيعُ الْبَصِيرُ(Shĩ ne) Mai ƙãga halittar sammai da ƙasa, Ya sanya muku ma'aura daga jinsinku, kuma (Ya sanya) daga dabbõbi maza da mãtã, Yanã halitta ku a cikinsu, wani abu bai zama kamar tamkarSa ba, kuma Shĩ ne Mai ji, Mai gani.0 Views
- لَهُ مَقَالِيدُ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ ۖ يَبْسُطُ الرِّزْقَ لِمَن يَشَاءُ وَيَقْدِرُ ۚ إِنَّهُ بِكُلِّ شَيْءٍ عَلِيمٌShĩ ne da mabuɗan sammai da ƙasa Yanã shimfiɗa arziki ga wanda ya so kuma Yanã hukuntãwa. Lalle ne, Shĩ Masani ne ga dukan kõme.0 Views
- ۞ شَرَعَ لَكُم مِّنَ الدِّينِ مَا وَصَّىٰ بِهِ نُوحًا وَالَّذِي أَوْحَيْنَا إِلَيْكَ وَمَا وَصَّيْنَا بِهِ إِبْرَاهِيمَ وَمُوسَىٰ وَعِيسَىٰ ۖ أَنْ أَقِيمُوا الدِّينَ وَلَا تَتَفَرَّقُوا فِيهِ ۚ كَبُرَ عَلَى الْمُشْرِكِينَ مَا تَدْعُوهُمْ إِلَيْهِ ۚ اللَّهُ يَجْتَبِي إِلَيْهِ مَن يَشَاءُ وَيَهْدِي إِلَيْهِ مَن يُنِيبُYa shar'anta muku, game da addini, abin da Ya yi wasiyya da shi ga Nũhu da abin da Muka yi wahayi da shi zuwa gare ka, da abin da Muka yi wasiyya da shi ga Ibrãhĩm da Mũsã da Ĩsã, cẽwa ku tsayar da addini sõsai kuma kada ku rarrabu a cikinsa. Abin da kuke kira zuwa gare shi, ya yi nauyi a kan mãsu shirki. Allah na zãɓen wanda Yake so zuwa gare Shi, kuma Yanã shiryar da wanda ke tawakkali gare Shi, ga hanyarSa.0 Views
- وَمَا تَفَرَّقُوا إِلَّا مِن بَعْدِ مَا جَاءَهُمُ الْعِلْمُ بَغْيًا بَيْنَهُمْ ۚ وَلَوْلَا كَلِمَةٌ سَبَقَتْ مِن رَّبِّكَ إِلَىٰ أَجَلٍ مُّسَمًّى لَّقُضِيَ بَيْنَهُمْ ۚ وَإِنَّ الَّذِينَ أُورِثُوا الْكِتَابَ مِن بَعْدِهِمْ لَفِي شَكٍّ مِّنْهُ مُرِيبٍKuma ba su rarraba ba fãce bãyan da ilmi ya jẽ musu, dõmin zãlunci a tsakãninsu kuma bã dõmin wata kalma tã gabata ba daga Ubangijinka, zuwa ga wani ajali ambatacce, dã an yi hukunci a tsakaninsu. Kuma lalle ne waɗanda aka gãdar wa Littafi daga bãyansu, haƙiƙa, sunã cikin shakka a gare shi, mai sanya kokanto.0 Views
- فَلِذَٰلِكَ فَادْعُ ۖ وَاسْتَقِمْ كَمَا أُمِرْتَ ۖ وَلَا تَتَّبِعْ أَهْوَاءَهُمْ ۖ وَقُلْ آمَنتُ بِمَا أَنزَلَ اللَّهُ مِن كِتَابٍ ۖ وَأُمِرْتُ لِأَعْدِلَ بَيْنَكُمُ ۖ اللَّهُ رَبُّنَا وَرَبُّكُمْ ۖ لَنَا أَعْمَالُنَا وَلَكُمْ أَعْمَالُكُمْ ۖ لَا حُجَّةَ بَيْنَنَا وَبَيْنَكُمُ ۖ اللَّهُ يَجْمَعُ بَيْنَنَا ۖ وَإِلَيْهِ الْمَصِيرُSabõda haka, sai ka yi kira kuma kai ka daidaitu kamar yadda aka umurce ka, kuma kada ka bi son zũciyõyinsu, kumaka ce, "Nã yi ĩmãni da abin da Allah Ya saukar na littãfi, kuma an umurce ni da in yi ãdalci a tsakãninku. Allah ne Ubangijinmu, kuma Shĩ ne Ubangijinku, ayyukanmu nã gare mu, kuma ayyukanku nã gare ku, kuma bãbu wata hujja a tsakãninmu da tsakãninku. Allah zai tara mu, kuma zuwa gare Shi makõma take."0 Views
- وَالَّذِينَ يُحَاجُّونَ فِي اللَّهِ مِن بَعْدِ مَا اسْتُجِيبَ لَهُ حُجَّتُهُمْ دَاحِضَةٌ عِندَ رَبِّهِمْ وَعَلَيْهِمْ غَضَبٌ وَلَهُمْ عَذَابٌ شَدِيدٌKuma waɗannan da ke jãyayya a cikin al'amarin Allah daga bãyan an karɓa masa, hujjarsu ɓãtãcciya ce a wurin Ubangijinsu, kuma akwai fushi a kansu, kuma sunã da wata azãba mai tsanani.0 Views
- اللَّهُ الَّذِي أَنزَلَ الْكِتَابَ بِالْحَقِّ وَالْمِيزَانَ ۗ وَمَا يُدْرِيكَ لَعَلَّ السَّاعَةَ قَرِيبٌAllah ne Wanda Ya saukar da Littãfi da gaskiya, da sikeli. Kuma me ya sanar da kai (cẽwa anã) tsammãnin Sa'ar kusa take?0 Views
- يَسْتَعْجِلُ بِهَا الَّذِينَ لَا يُؤْمِنُونَ بِهَا ۖ وَالَّذِينَ آمَنُوا مُشْفِقُونَ مِنْهَا وَيَعْلَمُونَ أَنَّهَا الْحَقُّ ۗ أَلَا إِنَّ الَّذِينَ يُمَارُونَ فِي السَّاعَةِ لَفِي ضَلَالٍ بَعِيدٍWaɗanda ba su yi ĩmãnida ita ba, (sũ) ke nẽman gaggautõwarta. Alhãli kuwa waɗanda suka yi ĩmãni, mãsu tsõro ne daga gare ta, kuma sun sani, cẽwa ita gaskiya ce. To, lalle ne waɗanda ke shakka a cikin Sa'a, haƙĩƙa, sunã a cikin ɓata Mai nĩsa.0 Views
- اللَّهُ لَطِيفٌ بِعِبَادِهِ يَرْزُقُ مَن يَشَاءُ ۖ وَهُوَ الْقَوِيُّ الْعَزِيزُAllah Mai tausasãwa ne ga bãyinsa. Yanã azurta wanda yake so, alhãli kuma Shĩ ne Maiƙarfi, Mabuwãyi.0 Views
- مَن كَانَ يُرِيدُ حَرْثَ الْآخِرَةِ نَزِدْ لَهُ فِي حَرْثِهِ ۖ وَمَن كَانَ يُرِيدُ حَرْثَ الدُّنْيَا نُؤْتِهِ مِنْهَا وَمَا لَهُ فِي الْآخِرَةِ مِن نَّصِيبٍWanda ya kasance yanã nufin nõman Lãhira zã Mu ƙãra masa a cikin nõmansa, kuma wanda ya kasance yanã nufin nõman dũniya, zã Mu sam masa daga gare ta, alhãli kuwa bã shi da wani rabo a cikin Lãhira.0 Views
- أَمْ لَهُمْ شُرَكَاءُ شَرَعُوا لَهُم مِّنَ الدِّينِ مَا لَمْ يَأْذَن بِهِ اللَّهُ ۚ وَلَوْلَا كَلِمَةُ الْفَصْلِ لَقُضِيَ بَيْنَهُمْ ۗ وَإِنَّ الظَّالِمِينَ لَهُمْ عَذَابٌ أَلِيمٌKõ sunã da waɗansu abõkan tãrayya (da Allah) waɗanda suka shar'anta musu, game da addini, abin da Allah bai yi izni ba da shi? Kuma bã dõmin kalmar hukunci ba, da lalle, an yi hukunci a tsakãninsu. Kuma lalle azzãlumai sunã da azãba mai raɗaɗi.0 Views
- تَرَى الظَّالِمِينَ مُشْفِقِينَ مِمَّا كَسَبُوا وَهُوَ وَاقِعٌ بِهِمْ ۗ وَالَّذِينَ آمَنُوا وَعَمِلُوا الصَّالِحَاتِ فِي رَوْضَاتِ الْجَنَّاتِ ۖ لَهُم مَّا يَشَاءُونَ عِندَ رَبِّهِمْ ۚ ذَٰلِكَ هُوَ الْفَضْلُ الْكَبِيرُKanã ganin azzãlumai sunã mãsu tsõro daga abin da suka sanã'anta alhãli kuwa shi abin tsoron, mai aukuwa ne gare su, kuma waɗanda suka yi ĩmãni kuma suka aikata ayyukan ƙwarai sunã a cikin fadamun Aljanna sunã da abin da suke so a wurin Ubangijinsu. Waccan fa ita ce falala mai girma.0 Views
- ذَٰلِكَ الَّذِي يُبَشِّرُ اللَّهُ عِبَادَهُ الَّذِينَ آمَنُوا وَعَمِلُوا الصَّالِحَاتِ ۗ قُل لَّا أَسْأَلُكُمْ عَلَيْهِ أَجْرًا إِلَّا الْمَوَدَّةَ فِي الْقُرْبَىٰ ۗ وَمَن يَقْتَرِفْ حَسَنَةً نَّزِدْ لَهُ فِيهَا حُسْنًا ۚ إِنَّ اللَّهَ غَفُورٌ شَكُورٌWancan shĩ ne Allah ke bãyar da bushãra da shi ga bãyinSa waɗanda suka yi ĩmãni kuma suka aikata ayyukan ƙwarai. Ka ce: "Bã ni tambayar ku wata ijãra a kansa, fãce dai sõyayya ta cikin zumunta." Kuma wanda ya aikata wani abu mai kyau, zã Mu ƙarã masa kyau a cikinsa, lalle Allah Mai gãfara ne, Mai gõdiya.3 Views
- أَمْ يَقُولُونَ افْتَرَىٰ عَلَى اللَّهِ كَذِبًا ۖ فَإِن يَشَإِ اللَّهُ يَخْتِمْ عَلَىٰ قَلْبِكَ ۗ وَيَمْحُ اللَّهُ الْبَاطِلَ وَيُحِقُّ الْحَقَّ بِكَلِمَاتِهِ ۚ إِنَّهُ عَلِيمٌ بِذَاتِ الصُّدُورِKõ zã su ce: "Ya ƙirƙira ƙarya ga Allah ne?" To, idan Allah Ya so, zai yunƙe a kan zũciyarka, kuma Allah Yana shãfe ƙarya kuma Yana tabbatar da gaskiya da kalmõminSa. Lalle ne Shĩ Masani ne ga abin da ke cikin zukata.0 Views
- وَهُوَ الَّذِي يَقْبَلُ التَّوْبَةَ عَنْ عِبَادِهِ وَيَعْفُو عَنِ السَّيِّئَاتِ وَيَعْلَمُ مَا تَفْعَلُونَKuma Shi ne ke karɓar tũba daga bãyinSa, kuma Yanã Yafe ƙananan laifuffuka, alhãli kuwa Yanã sanin abin da kuke aikatãwa.0 Views
- وَيَسْتَجِيبُ الَّذِينَ آمَنُوا وَعَمِلُوا الصَّالِحَاتِ وَيَزِيدُهُم مِّن فَضْلِهِ ۚ وَالْكَافِرُونَ لَهُمْ عَذَابٌ شَدِيدٌKuma Yanã karɓa wa waɗannan da suka yi ĩmãni kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, kuma Yanã ƙãra musu (sakamako) daga falalarSa. Kuma kãfirai sunã da wata azãba mai tsanani.0 Views
- ۞ وَلَوْ بَسَطَ اللَّهُ الرِّزْقَ لِعِبَادِهِ لَبَغَوْا فِي الْأَرْضِ وَلَـٰكِن يُنَزِّلُ بِقَدَرٍ مَّا يَشَاءُ ۚ إِنَّهُ بِعِبَادِهِ خَبِيرٌ بَصِيرٌKuma dã Allah Ya shimfiɗa arziki ga bãyinSa, dã sun yi zãluncin rarraba jama'a a cikin ƙasa, kuma amma Yanã sassaukarwa gwargwado ga abin da Yake so. Lalle ne Shĩ, game da bãyinSa, Mai labartawa ne, Mai gani.0 Views
- وَهُوَ الَّذِي يُنَزِّلُ الْغَيْثَ مِن بَعْدِ مَا قَنَطُوا وَيَنشُرُ رَحْمَتَهُ ۚ وَهُوَ الْوَلِيُّ الْحَمِيدُKuma Shĩ ne ke sassaukar da girgije (ruwa) a bãyan sun yanke ƙauna kuma Yana wãtsa rahamarSa, alhãli kuwa Shĩ ne Majiɓinci, Mai gõdiya.0 Views
- وَمِنْ آيَاتِهِ خَلْقُ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ وَمَا بَثَّ فِيهِمَا مِن دَابَّةٍ ۚ وَهُوَ عَلَىٰ جَمْعِهِمْ إِذَا يَشَاءُ قَدِيرٌKuma akwai daga ãyõyinSa, halittar sammai da ƙasa da abin da Ya wãtsa a cikinsu na dabba alhãli kuwa Shĩ Mai ĩko ne ga tãra su, a lõkacin da Yake so.0 Views
- وَمَا أَصَابَكُم مِّن مُّصِيبَةٍ فَبِمَا كَسَبَتْ أَيْدِيكُمْ وَيَعْفُو عَن كَثِيرٍKuma abin da ya sãme ku na wata masifa, to, game da abin da hannãyenku suka sana' anta ne kuma (Alah) Yanã Yafẽwar (waɗansu laifuffuka) mãsu yawa.0 Views
- وَمَا أَنتُم بِمُعْجِزِينَ فِي الْأَرْضِ ۖ وَمَا لَكُم مِّن دُونِ اللَّهِ مِن وَلِيٍّ وَلَا نَصِيرٍKuma ba ku zama mãsu buwãya ba a cikin ƙasa kuma bã ku da wani majiɓinci, wanin Allah, kuma bã ku da wani mataimaki.0 Views
- وَمِنْ آيَاتِهِ الْجَوَارِ فِي الْبَحْرِ كَالْأَعْلَامِKuma akwai daga ãyõyinsa, jirãge mãsu gudãna a cikin tẽku kamar duwãtsu.0 Views
- إِن يَشَأْ يُسْكِنِ الرِّيحَ فَيَظْلَلْنَ رَوَاكِدَ عَلَىٰ ظَهْرِهِ ۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَآيَاتٍ لِّكُلِّ صَبَّارٍ شَكُورٍIdan Ya so, sai Ya kwantar da iskar, sai jirãgen su yini sunã mãsu kawaici a kan bãyan tẽkun, Lalle ne ga wancan, haƙĩƙa, akwai ãyõyi ga dukan mai haƙuri, Mai gõdiya.0 Views
- أَوْ يُوبِقْهُنَّ بِمَا كَسَبُوا وَيَعْفُ عَن كَثِيرٍKõ Ya halakã su (sũ jirãgen) sabõda abin da mãsu su suka sanã'anta, alhãli kuwa Yanã yãfe (laifuffuka) mãsu yawa.0 Views
- وَيَعْلَمَ الَّذِينَ يُجَادِلُونَ فِي آيَاتِنَا مَا لَهُم مِّن مَّحِيصٍKuma dõmin waɗanda ke jãyayya a cikin ãyõyinMu su sani (cẽwa) bã su da wata mafaka.0 Views
- فَمَا أُوتِيتُم مِّن شَيْءٍ فَمَتَاعُ الْحَيَاةِ الدُّنْيَا ۖ وَمَا عِندَ اللَّهِ خَيْرٌ وَأَبْقَىٰ لِلَّذِينَ آمَنُوا وَعَلَىٰ رَبِّهِمْ يَتَوَكَّلُونَSabõda haka abin da aka bã ku, kõ mẽne ne, to, jin dãɗin rayuwar dũniya ne, kuma abin da ke a wurin Allah Shĩ ne mafĩfĩci, kuma Shĩ ne mafi wanzuwa ga waɗanda suka yi ĩmãni kuma sunã dõgara a kan Ubangijinsu kawai.0 Views
- وَالَّذِينَ يَجْتَنِبُونَ كَبَائِرَ الْإِثْمِ وَالْفَوَاحِشَ وَإِذَا مَا غَضِبُوا هُمْ يَغْفِرُونَKuma waɗanda ke nisantar manyan zunubbai da ayyukan alfãsha, kuma idan sun yi fushi, sũ, sunã gãfartawa.0 Views
- وَالَّذِينَ اسْتَجَابُوا لِرَبِّهِمْ وَأَقَامُوا الصَّلَاةَ وَأَمْرُهُمْ شُورَىٰ بَيْنَهُمْ وَمِمَّا رَزَقْنَاهُمْ يُنفِقُونَDa waɗanda suka karɓa kira ga Ubangijinsu, kuma suka tsayar da salla, kuma al'amarinsu shãwara ne a tsakãninsu, kuma daga abin da Muka azurta su sunã ciyarwa.0 Views
- وَالَّذِينَ إِذَا أَصَابَهُمُ الْبَغْيُ هُمْ يَنتَصِرُونَDa waɗanda idan zãlunci ya sãme su, sunã nẽman taimako (su rãma).0 Views
- وَجَزَاءُ سَيِّئَةٍ سَيِّئَةٌ مِّثْلُهَا ۖ فَمَنْ عَفَا وَأَصْلَحَ فَأَجْرُهُ عَلَى اللَّهِ ۚ إِنَّهُ لَا يُحِبُّ الظَّالِمِينَKuma sakamakon cũta shĩ ne wata cũta kamarta, sai dai wanda Ya yãfe kuma ya kyautata, to lãdarsa nã ga Allah. Lalle ne, Shĩ (Allah) bã Ya son azzãlumai.0 Views
- وَلَمَنِ انتَصَرَ بَعْدَ ظُلْمِهِ فَأُولَـٰئِكَ مَا عَلَيْهِم مِّن سَبِيلٍKuma Lalle ne, wanda ya nẽmi taimakon rãmãwa a bãyan an zãlunce shi, to waɗannan bãbu wata hanyar zargi a kansu.0 Views
- إِنَّمَا السَّبِيلُ عَلَى الَّذِينَ يَظْلِمُونَ النَّاسَ وَيَبْغُونَ فِي الْأَرْضِ بِغَيْرِ الْحَقِّ ۚ أُولَـٰئِكَ لَهُمْ عَذَابٌ أَلِيمٌlnda hanyar zargi kawai take, shĩ ne a kan waɗanda ke zãluntar mutãne kuma sunã ƙẽtare haddin shari'a cikin ƙasa bã tare da haƙƙi ba. Waɗannan sunã da azãba Mai raɗaɗi.0 Views
- وَلَمَن صَبَرَ وَغَفَرَ إِنَّ ذَٰلِكَ لَمِنْ عَزْمِ الْأُمُورِKuma Lalle ne, wanda ya yi haƙuri kuma ya gãfarta (wa wanda ya zãlunce shi), to shĩ wancan aiki haƙĩƙa, yanã daga manyan al'amura (da Allah ke so).0 Views
- وَمَن يُضْلِلِ اللَّهُ فَمَا لَهُ مِن وَلِيٍّ مِّن بَعْدِهِ ۗ وَتَرَى الظَّالِمِينَ لَمَّا رَأَوُا الْعَذَابَ يَقُولُونَ هَلْ إِلَىٰ مَرَدٍّ مِّن سَبِيلٍKuma wanda (Allah Ya ɓatar, to, bã shi da wani majiɓinci bãyanSa, kuma zã ka ga azzãlumai, a lõkacin da suka ga azãba, sunã cẽwa, "Shin, akwai hanya zuwa ga kõmãwa?"0 Views
- وَتَرَاهُمْ يُعْرَضُونَ عَلَيْهَا خَاشِعِينَ مِنَ الذُّلِّ يَنظُرُونَ مِن طَرْفٍ خَفِيٍّ ۗ وَقَالَ الَّذِينَ آمَنُوا إِنَّ الْخَاسِرِينَ الَّذِينَ خَسِرُوا أَنفُسَهُمْ وَأَهْلِيهِمْ يَوْمَ الْقِيَامَةِ ۗ أَلَا إِنَّ الظَّالِمِينَ فِي عَذَابٍ مُّقِيمٍKuma kanã ganin su anã gitta su a kanta, sunã ƙasƙantattu sabõda wulãkanci, sunã hange daga gefen gani ɓoyayye. Kuma waɗanda suka yi ĩmãni sai su ce, "Lalle ne, mãsu hasãra, sũ ne waɗanda suka yi hasãrar rãyukansu da iyãlansu a Rãnar ¡iyãma." To, lalle ne, azzãlumai sunã a cikin wata azãba zaunanniya.0 Views
- وَمَا كَانَ لَهُم مِّنْ أَوْلِيَاءَ يَنصُرُونَهُم مِّن دُونِ اللَّهِ ۗ وَمَن يُضْلِلِ اللَّهُ فَمَا لَهُ مِن سَبِيلٍKuma waɗansu majiɓinta ba su kasance ba a gare su, waɗanda ke iya taimakonsu, baicin Allah. Kuma wanda Allah Ya ɓatar, to, bã shi da wani gõdabe na tsĩra.0 Views
- اسْتَجِيبُوا لِرَبِّكُم مِّن قَبْلِ أَن يَأْتِيَ يَوْمٌ لَّا مَرَدَّ لَهُ مِنَ اللَّهِ ۚ مَا لَكُم مِّن مَّلْجَإٍ يَوْمَئِذٍ وَمَا لَكُم مِّن نَّكِيرٍKu karɓã wa Ubangijinku tun gabãnin wani yini ya zo, bãbu makawa gare shi daga Allah, bã ku da wata mafaka a rãnar nan, kuma bã ku iya yin wani musu.0 Views
- فَإِنْ أَعْرَضُوا فَمَا أَرْسَلْنَاكَ عَلَيْهِمْ حَفِيظًا ۖ إِنْ عَلَيْكَ إِلَّا الْبَلَاغُ ۗ وَإِنَّا إِذَا أَذَقْنَا الْإِنسَانَ مِنَّا رَحْمَةً فَرِحَ بِهَا ۖ وَإِن تُصِبْهُمْ سَيِّئَةٌ بِمَا قَدَّمَتْ أَيْدِيهِمْ فَإِنَّ الْإِنسَانَ كَفُورٌTo, idan sun bijire, to, ba Mu aike ka kanã mai tsaro a kansu ba, bãbu abin da ke a kanka fãce iyar da Manzanci. Kuma lalle ne, Mũ idan Mun ɗanɗana wa mutum wata rahama daga gare Mu, sai ya yi farin ciki da ita, kuma idan wata masĩfa ta sãme su sabõda abin da hannayensu suka gabãtar, to, lalle ne mutum mai tsananin kãfirci ne.3 Views
- لِّلَّهِ مُلْكُ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ ۚ يَخْلُقُ مَا يَشَاءُ ۚ يَهَبُ لِمَن يَشَاءُ إِنَاثًا وَيَهَبُ لِمَن يَشَاءُ الذُّكُورَMulkin sammai da ƙasa na Allah kawai ne. Yanã halitta abin da Yake so. Yanã bãyar da 'ya'ya mãtã ga wanda yake so, kuma Yanã bãyar da ɗiya maza ga wanda Yake so.0 Views
- أَوْ يُزَوِّجُهُمْ ذُكْرَانًا وَإِنَاثًا ۖ وَيَجْعَلُ مَن يَشَاءُ عَقِيمًا ۚ إِنَّهُ عَلِيمٌ قَدِيرٌKõ kuma Ya haɗa su maza da mãtã, kuma Yanã sanya wanda Ya so bakarãre. Lalle shi, Mai ilmi ne, Mai ĩkon yi.0 Views
- ۞ وَمَا كَانَ لِبَشَرٍ أَن يُكَلِّمَهُ اللَّهُ إِلَّا وَحْيًا أَوْ مِن وَرَاءِ حِجَابٍ أَوْ يُرْسِلَ رَسُولًا فَيُوحِيَ بِإِذْنِهِ مَا يَشَاءُ ۚ إِنَّهُ عَلِيٌّ حَكِيمٌKuma bã ya kasancẽwa ga wani mutum Allah Ya yi masa magana fãce da wahayi, kõ daga bãYan wani shãmaki, kõ Ya aika wani Manzo, sa'an nan Ya yi wahayi, da izninsa ga abin da Yake so. Lalle Shĩ, Maɗaukaki ne Mai hikima.0 Views
- وَكَذَٰلِكَ أَوْحَيْنَا إِلَيْكَ رُوحًا مِّنْ أَمْرِنَا ۚ مَا كُنتَ تَدْرِي مَا الْكِتَابُ وَلَا الْإِيمَانُ وَلَـٰكِن جَعَلْنَاهُ نُورًا نَّهْدِي بِهِ مَن نَّشَاءُ مِنْ عِبَادِنَا ۚ وَإِنَّكَ لَتَهْدِي إِلَىٰ صِرَاطٍ مُّسْتَقِيمٍKuma kamar wancan Mun aika wani rũhi (rai mai haɗa jama'a) zuwa gare ka, daga gare Mu. Ba ka kasance kã san abin da yake littãfi ba, kõ abin da Yake ĩmãni, kuma amma Mun sanya shi (rũhin, watau Alƙur'ãni) wani haske ne, Munã shiryar da wanda Muke so daga cikin bãyĩnMu game da shi. Kuma Lalle kai, haƙĩƙa, kanã shiryarwa zuwa ga hanya, madaidaiciya.0 Views
- صِرَاطِ اللَّهِ الَّذِي لَهُ مَا فِي السَّمَاوَاتِ وَمَا فِي الْأَرْضِ ۗ أَلَا إِلَى اللَّهِ تَصِيرُ الْأُمُورُHanyar Allah wanda ke da mulkin abin da ke cikin sammai da abin da ke cikin ƙasa. To, zuwa ga Allah kawai al'amura ke kõmãwa.0 Views
Surah az-zukhruf
Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
- حمٓḤ. M̃.0 Views
- وَالْكِتَابِ الْمُبِينِIna rantsuwa da Littãfi Mabayyani.0 Views
- إِنَّا جَعَلْنَاهُ قُرْآنًا عَرَبِيًّا لَّعَلَّكُمْ تَعْقِلُونَLalle Mũ, Mun sanya shi abin karãtu na Lãrabci, tsammãninku, kunã hankalta.0 Views
- وَإِنَّهُ فِي أُمِّ الْكِتَابِ لَدَيْنَا لَعَلِيٌّ حَكِيمٌKuma lalle, shĩ, a cikin uwar littãfi a wurin Mu, haƙĩƙa, maɗaukaki ne, bayyananne.0 Views
- أَفَنَضْرِبُ عَنكُمُ الذِّكْرَ صَفْحًا أَن كُنتُمْ قَوْمًا مُّسْرِفِينَShin, zã Mu kau da kai daga saukar da hukunci daga gare ku ne dõmin kun kasance mutane mãsu ɓarna?0 Views
- وَكَمْ أَرْسَلْنَا مِن نَّبِيٍّ فِي الْأَوَّلِينَAlhãli kuwa sau nawa Muka aika wani Annabi a cikin mutãnen fãrko!0 Views
- وَمَا يَأْتِيهِم مِّن نَّبِيٍّ إِلَّا كَانُوا بِهِ يَسْتَهْزِئُونَKuma wani Annabi bai je musu ba fãce sun kasance, game da shi, sunã mãsu yin izgili.0 Views
- فَأَهْلَكْنَا أَشَدَّ مِنْهُم بَطْشًا وَمَضَىٰ مَثَلُ الْأَوَّلِينَSai Muka halakar da waɗanda suke sũ ne mafiya ƙarfin damƙa daga gare su. Kuma abin misãlin mutãnen farkon ya shũɗe.0 Views
- وَلَئِن سَأَلْتَهُم مَّنْ خَلَقَ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضَ لَيَقُولُنَّ خَلَقَهُنَّ الْعَزِيزُ الْعَلِيمُKuma lalle ne, idan ka tambaye su, "Wãne ne ya halitta sammai da ƙasa?" Lalle zã su ce, "Mabuwãyi Mai ilmi ne Ya halitta su."0 Views
- الَّذِي جَعَلَ لَكُمُ الْأَرْضَ مَهْدًا وَجَعَلَ لَكُمْ فِيهَا سُبُلًا لَّعَلَّكُمْ تَهْتَدُونَWanda Ya sanya muku ƙasa shimfiɗa kuma Ya sanya muku hanyõyi a cikinta, tsammãninku za ku nẽmi shiryuwa.'0 Views
- وَالَّذِي نَزَّلَ مِنَ السَّمَاءِ مَاءً بِقَدَرٍ فَأَنشَرْنَا بِهِ بَلْدَةً مَّيْتًا ۚ كَذَٰلِكَ تُخْرَجُونَKuma Wanda Ya saukar da ruwa daga sama, a kan wani gwargwado, sai Muka rãyar da gari matacce game da shi. Kamar haka nan ake fitar da ku (daga kabari).0 Views
- وَالَّذِي خَلَقَ الْأَزْوَاجَ كُلَّهَا وَجَعَلَ لَكُم مِّنَ الْفُلْكِ وَالْأَنْعَامِ مَا تَرْكَبُونَKuma Wanda Ya halitta ma'aura dukansu, kuma Ya sanya muku, daga jirgi da dabbõbin ni'ima, abin da kuke hawa.0 Views
- لِتَسْتَوُوا عَلَىٰ ظُهُورِهِ ثُمَّ تَذْكُرُوا نِعْمَةَ رَبِّكُمْ إِذَا اسْتَوَيْتُمْ عَلَيْهِ وَتَقُولُوا سُبْحَانَ الَّذِي سَخَّرَ لَنَا هَـٰذَا وَمَا كُنَّا لَهُ مُقْرِنِينَDomin ku daidaitu a kan bãyansa, sa'an nan ku tuna ni'imar Ubangijinku a lõkacin da kuka daidaita a kansa kuma ku ce, "Tsarki ya tabbata ga Wanda Ya hõre mana wannan alhãli kuwa ba mu kasance mãsu iya rinjãya gare Shi ba.0 Views
- وَإِنَّا إِلَىٰ رَبِّنَا لَمُنقَلِبُونَ"Kuma lalle mũ haƙĩƙa mãsu jũyãwa muke, zuwa ga Ubangijinmu."0 Views
- وَجَعَلُوا لَهُ مِنْ عِبَادِهِ جُزْءًا ۚ إِنَّ الْإِنسَانَ لَكَفُورٌ مُّبِينٌKuma suka sanya Masa juz'i daga bãyinsa. Lalle ne mutum, haƙĩƙa, mai yawan kãfirci ne, mai bayyanãwar kãfircin.0 Views
- أَمِ اتَّخَذَ مِمَّا يَخْلُقُ بَنَاتٍ وَأَصْفَاكُم بِالْبَنِينَKõ zã Ya ɗauki 'ya'ya mãtã daga abin da Yake halittawa ne, kuma Ya zãɓe ku da ɗiya maza?0 Views
- وَإِذَا بُشِّرَ أَحَدُهُم بِمَا ضَرَبَ لِلرَّحْمَـٰنِ مَثَلًا ظَلَّ وَجْهُهُ مُسْوَدًّا وَهُوَ كَظِيمٌAlhãli kuwa idan an bãyar da bushãra ga ɗayansu da abin da ya buga misãli da shi ga Mai rahama, sai fuskarsa ta yini tanã wadda aka baƙanta launinta, kuma yanã cike da baƙin ciki.0 Views
- أَوَمَن يُنَشَّأُ فِي الْحِلْيَةِ وَهُوَ فِي الْخِصَامِ غَيْرُ مُبِينٍAshe, kuma (Allah zai zãɓi) wanda ake rẽno a cikin ƙawa alhãli kuwa gã shi a husũma bã mai iya bayyanawar magana ba?0 Views
- وَجَعَلُوا الْمَلَائِكَةَ الَّذِينَ هُمْ عِبَادُ الرَّحْمَـٰنِ إِنَاثًا ۚ أَشَهِدُوا خَلْقَهُمْ ۚ سَتُكْتَبُ شَهَادَتُهُمْ وَيُسْأَلُونَKuma suka mayar da malã'iku ('yã'ya) mãtã, alhãli kuwa sũ, waɗanda suke bãyin (Allah) Mai rahama ne! Shin, sun halarci halittarsu ne? zã a rubũta shaidarsu kuma a tambaye su.0 Views
- وَقَالُوا لَوْ شَاءَ الرَّحْمَـٰنُ مَا عَبَدْنَاهُم ۗ مَّا لَهُم بِذَٰلِكَ مِنْ عِلْمٍ ۖ إِنْ هُمْ إِلَّا يَخْرُصُونَKuma suka ce: "Dã Mai rahama ya so, dã ba mu bauta musu ba." Bã su da wani ilmi game da wancan! Bãbu abin da suke yi fãce yanki-faɗi.0 Views
- أَمْ آتَيْنَاهُمْ كِتَابًا مِّن قَبْلِهِ فَهُم بِهِ مُسْتَمْسِكُونَKõ Mun bã su wani littãfi ne a gabãninsa (Alƙur'ãni) sabõda haka da shĩ suke riƙe?0 Views
- بَلْ قَالُوا إِنَّا وَجَدْنَا آبَاءَنَا عَلَىٰ أُمَّةٍ وَإِنَّا عَلَىٰ آثَارِهِم مُّهْتَدُونَÃ'a, sun ce dai, "Lalle mũ, mun sãmi ubanninmu a kan wani addini (na al'ãda) kuma lalle mũ, a kan gurãbunsu muke mãsu nẽman shiryuwa."3 Views
- وَكَذَٰلِكَ مَا أَرْسَلْنَا مِن قَبْلِكَ فِي قَرْيَةٍ مِّن نَّذِيرٍ إِلَّا قَالَ مُتْرَفُوهَا إِنَّا وَجَدْنَا آبَاءَنَا عَلَىٰ أُمَّةٍ وَإِنَّا عَلَىٰ آثَارِهِم مُّقْتَدُونَKuma kamar haka, ba Mu aika wani mai gargaɗi ba a gabãninka, a cikin wata alƙarya, fãce mani'imtanta sun ce, "Lalle mũ, mun sãmi ubanninmu a kan wani addini kuma lalle mũ, mãsu kõyi nea kan gurãbunsu."3 Views
- ۞ قَالَ أَوَلَوْ جِئْتُكُم بِأَهْدَىٰ مِمَّا وَجَدتُّمْ عَلَيْهِ آبَاءَكُمْ ۖ قَالُوا إِنَّا بِمَا أُرْسِلْتُم بِهِ كَافِرُونَ(Sai mai gargaɗin) ya ce: "Shin, ban zo muku da abin da ya fi zama shiriya daga abin da kuka sãmi ubanninku a kansa ba?" Suka ce, "Lalle mũ dai mãsu kafirta ne game da abin da aka aiko ku da shi."3 Views
- فَانتَقَمْنَا مِنْهُمْ ۖ فَانظُرْ كَيْفَ كَانَ عَاقِبَةُ الْمُكَذِّبِينَSabõda haka Muka yi musu azãbar rãmuwa. To, ka dũbi yadda ãƙibar mãsu ƙaryatãwa take.0 Views
- وَإِذْ قَالَ إِبْرَاهِيمُ لِأَبِيهِ وَقَوْمِهِ إِنَّنِي بَرَاءٌ مِّمَّا تَعْبُدُونَKuma (ka ambaci) lõkacin da Ibrãhĩm ya ce wa ubansada mutãnensa, "Lalle nĩ mai barranta ne daga abin da kuke bautãwa."0 Views
- إِلَّا الَّذِي فَطَرَنِي فَإِنَّهُ سَيَهْدِينِ"Fãce wannan da Ya ƙãga halittata, to, lalle Shĩ ne zai shiryar da ni."0 Views
- وَجَعَلَهَا كَلِمَةً بَاقِيَةً فِي عَقِبِهِ لَعَلَّهُمْ يَرْجِعُونَKuma (Ibrãhĩm) ya sanya (ita wannan magana) kalma mai wanzuwa a cikin zuriyarsa, tsammãninsu su kõmo daga ɓata.0 Views
- بَلْ مَتَّعْتُ هَـٰؤُلَاءِ وَآبَاءَهُمْ حَتَّىٰ جَاءَهُمُ الْحَقُّ وَرَسُولٌ مُّبِينٌÃ'a, Na jiyar da waɗannan mutãne dãɗi sũ da ubanninsu har gaskiya, da Manzo mai bayyanawar gaskiyar, ya zo musu.0 Views
- وَلَمَّا جَاءَهُمُ الْحَقُّ قَالُوا هَـٰذَا سِحْرٌ وَإِنَّا بِهِ كَافِرُونَKuma a lõkacin da gaskiyar ta jẽ musu sai suka ce: "Wannan sihiri ne kuma mũ mãsu kãfirta da shi ne."0 Views
- وَقَالُوا لَوْلَا نُزِّلَ هَـٰذَا الْقُرْآنُ عَلَىٰ رَجُلٍ مِّنَ الْقَرْيَتَيْنِ عَظِيمٍKuma suka ce: "Don me ba a saukar da wannan Alƙur'ãni a kan wani mutum mai girma daga alƙaryun nan biyu ba?"0 Views
- أَهُمْ يَقْسِمُونَ رَحْمَتَ رَبِّكَ ۚ نَحْنُ قَسَمْنَا بَيْنَهُم مَّعِيشَتَهُمْ فِي الْحَيَاةِ الدُّنْيَا ۚ وَرَفَعْنَا بَعْضَهُمْ فَوْقَ بَعْضٍ دَرَجَاتٍ لِّيَتَّخِذَ بَعْضُهُم بَعْضًا سُخْرِيًّا ۗ وَرَحْمَتُ رَبِّكَ خَيْرٌ مِّمَّا يَجْمَعُونَShin, sũ ne ke raba rahamar Ubangijinka? Mũ ne, Muka raba musu abincinsu a cikin rãyuwar dũniya, kuma Muka ɗaukaka waɗansunsu a kan waɗansu da darajõji dõmin waɗansunsu su riƙi waɗansu lẽburori kumarahamar Ubangijinka (ta Annabci), ita ce mafificiya daga abin da suke tãrãwa.0 Views
- وَلَوْلَا أَن يَكُونَ النَّاسُ أُمَّةً وَاحِدَةً لَّجَعَلْنَا لِمَن يَكْفُرُ بِالرَّحْمَـٰنِ لِبُيُوتِهِمْ سُقُفًا مِّن فِضَّةٍ وَمَعَارِجَ عَلَيْهَا يَظْهَرُونَKuma bã dõmin mutane su kasance al'umma ɗaya ba, lalle ne, dã Mun sanya wa mãsu kãfircẽ wa Mai Rahama, a gidãjensu, rufi na azurfa, kuma da matãkalai, ya zama a kanta suke tãƙãwa.0 Views
- وَلِبُيُوتِهِمْ أَبْوَابًا وَسُرُرًا عَلَيْهَا يَتَّكِئُونَKuma a gidãjensu, Mu sanya) ƙyamãre da gadãje, a kansu suke kishingiɗa.0 Views
- وَزُخْرُفًا ۚ وَإِن كُلُّ ذَٰلِكَ لَمَّا مَتَاعُ الْحَيَاةِ الدُّنْيَا ۚ وَالْآخِرَةُ عِندَ رَبِّكَ لِلْمُتَّقِينَDa zĩnãriya. Kuma dukan wancan abu bai zama ba, sai jin dãɗin rãyuwar dũniya nekawai' alhãli kuwa Lãhira, a wurin Ubangijinka, ta mãsu taƙawa ce.0 Views
- وَمَن يَعْشُ عَن ذِكْرِ الرَّحْمَـٰنِ نُقَيِّضْ لَهُ شَيْطَانًا فَهُوَ لَهُ قَرِينٌKuma wanda ya makanta daga barin hukuncin Mai rahama, to, zã Mu lulluɓe shi da shaiɗan, watau shĩ ne abõkinsa.0 Views
- وَإِنَّهُمْ لَيَصُدُّونَهُمْ عَنِ السَّبِيلِ وَيَحْسَبُونَ أَنَّهُم مُّهْتَدُونَKuma lalle su haƙĩƙa sunã kange su daga hanya, kuma sunã Zaton cẽwa sũ mãsu shiryuwa ne.0 Views
- حَتَّىٰ إِذَا جَاءَنَا قَالَ يَا لَيْتَ بَيْنِي وَبَيْنَكَ بُعْدَ الْمَشْرِقَيْنِ فَبِئْسَ الْقَرِينُHar a lõkacin da (abõkin Shaiɗan) ya zo Mana (ya mutu) sai ya ce: (wa Shaiɗan) "Dã dai a tsakãnina da tsakãninka akwai nĩsan gabas da yamma, sabõda haka, tir da kai ga zama abõkin mutum!"0 Views
- وَلَن يَنفَعَكُمُ الْيَوْمَ إِذ ظَّلَمْتُمْ أَنَّكُمْ فِي الْعَذَابِ مُشْتَرِكُونَKuma (wannan magana) bã za ta amfãne ku ba, a yau, dõmin kun yi zãlunci, lalle ku mãsu tãrẽwa ne a cikin azãba.0 Views
- أَفَأَنتَ تُسْمِعُ الصُّمَّ أَوْ تَهْدِي الْعُمْيَ وَمَن كَانَ فِي ضَلَالٍ مُّبِينٍShin to, kai kanã jiyar da kurma ne, ko kanã shiryar da makãho da wanda ke a cikin ɓata bayyananna?0 Views
- فَإِمَّا نَذْهَبَنَّ بِكَ فَإِنَّا مِنْهُم مُّنتَقِمُونَTo, kõ dai Mu tafi da kai to, lalle Mũ, mãsu yin azãbarrãmu, wa ne a kansu.0 Views
- أَوْ نُرِيَنَّكَ الَّذِي وَعَدْنَاهُمْ فَإِنَّا عَلَيْهِم مُّقْتَدِرُونَKõ kuma Mu nũna maka abin da Muka yi musu wa'adi, to, lalle Mũ, Mãsu ĩkon tasarrufi a kansu ne.0 Views
- فَاسْتَمْسِكْ بِالَّذِي أُوحِيَ إِلَيْكَ ۖ إِنَّكَ عَلَىٰ صِرَاطٍ مُّسْتَقِيمٍSabõda haka, ka yi riƙo ga abin da aka yi wahayi da shi zuwa gaie ka. Lalle ne kai, kanã a kan hanya madaidaiciyl.0 Views
- وَإِنَّهُ لَذِكْرٌ لَّكَ وَلِقَوْمِكَ ۖ وَسَوْفَ تُسْأَلُونَKuma shi (abin wahayin) ambato (na ɗaukaka) ne a gare ka da kuma ga mutãnenka, kuma zã a tambaye ku.0 Views
- وَاسْأَلْ مَنْ أَرْسَلْنَا مِن قَبْلِكَ مِن رُّسُلِنَا أَجَعَلْنَا مِن دُونِ الرَّحْمَـٰنِ آلِهَةً يُعْبَدُونَKuma ka tambayi waɗanda Muka aika a gabãninka daga Manzannin Mu, "Shin, Mun sanya waɗansu gumãka, wasun (Allah), Mai rahama, anã bauta musu?"0 Views
- وَلَقَدْ أَرْسَلْنَا مُوسَىٰ بِآيَاتِنَا إِلَىٰ فِرْعَوْنَ وَمَلَئِهِ فَقَالَ إِنِّي رَسُولُ رَبِّ الْعَالَمِينَKuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun aika Mũsã, game da ãyõyin Mu, zuwa ga Fir'auna da mashãwartansa, sai ya ce: "Lalle nĩ, Manzo ne daga Ubangijin halittu."0 Views
- فَلَمَّا جَاءَهُم بِآيَاتِنَا إِذَا هُم مِّنْهَا يَضْحَكُونَTo, a lõkacin da ya jẽ musu da ãyõyinMu, sai gã su sunã yi musu dãriya.0 Views
- وَمَا نُرِيهِم مِّنْ آيَةٍ إِلَّا هِيَ أَكْبَرُ مِنْ أُخْتِهَا ۖ وَأَخَذْنَاهُم بِالْعَذَابِ لَعَلَّهُمْ يَرْجِعُونَKuma ba Mu nũna musu wata ãyã ba, fãce ita ce mafi girma daga 'yar'uwarta. Kuma Muka kãma su da azãba, tsammãninsu kõ sunã kõmõwa.0 Views
- وَقَالُوا يَا أَيُّهَ السَّاحِرُ ادْعُ لَنَا رَبَّكَ بِمَا عَهِدَ عِندَكَ إِنَّنَا لَمُهْتَدُونَKuma suka ce: "Yã kai mai sihiri! Ka rõƙa mana Ubangijinka da albarkacin abin da yi alkawari a wurinka, lalle mũ, haƙĩƙa, mãsu shiryuwa ne."0 Views
- فَلَمَّا كَشَفْنَا عَنْهُمُ الْعَذَابَ إِذَا هُمْ يَنكُثُونَTo, a lõkacin da duk Muka kuranye musu azãba, sai gã su sunã warware alkawarinsu.0 Views
- وَنَادَىٰ فِرْعَوْنُ فِي قَوْمِهِ قَالَ يَا قَوْمِ أَلَيْسَ لِي مُلْكُ مِصْرَ وَهَـٰذِهِ الْأَنْهَارُ تَجْرِي مِن تَحْتِي ۖ أَفَلَا تُبْصِرُونَKuma Fir'auna ya yi kira a cikin mutãnensa, ya ce: "Ya mutãnẽna! Ashe mulkin Masar bã a gare ni yake ba, kuma waɗannan kõguna sunã gudãna daga ƙarƙashĩna? Ashe, ba ku gani ba?"0 Views
- أَمْ أَنَا خَيْرٌ مِّنْ هَـٰذَا الَّذِي هُوَ مَهِينٌ وَلَا يَكَادُ يُبِينُ"Kõ kuma bã nĩ ne mafĩfĩci ba daga wannan wanda yake shĩ wulakantacce ne kuma bã ya iya bayyanawar magana sai da ƙyar?0 Views
- فَلَوْلَا أُلْقِيَ عَلَيْهِ أَسْوِرَةٌ مِّن ذَهَبٍ أَوْ جَاءَ مَعَهُ الْمَلَائِكَةُ مُقْتَرِنِينَ"To, don me, ba a jẽfa mundãye na zĩnãriya a kansaba, kõ kuma malã'iku su taho tãre da shi haɗe?"0 Views
- فَاسْتَخَفَّ قَوْمَهُ فَأَطَاعُوهُ ۚ إِنَّهُمْ كَانُوا قَوْمًا فَاسِقِينَSai ya sassabce hankalin mutãnensa, sabõda haka suka bĩ shi. Lalle sũ, sun kasance waɗansu irin mutãne ne fãsiƙai.0 Views
- فَلَمَّا آسَفُونَا انتَقَمْنَا مِنْهُمْ فَأَغْرَقْنَاهُمْ أَجْمَعِينَSabõda haka a lõkacin da suka husãtar da Mu, Muka yi musu azãbar rãmuwa sai Muka nutsar da su gabã ɗaya.0 Views
- فَجَعَلْنَاهُمْ سَلَفًا وَمَثَلًا لِّلْآخِرِينَSai Muka sanya su magabãta kuma abin misãli ga mutãnen ƙarshe.0 Views
- ۞ وَلَمَّا ضُرِبَ ابْنُ مَرْيَمَ مَثَلًا إِذَا قَوْمُكَ مِنْهُ يَصِدُّونَKuma a lõkacin da aka buga misãli da ¦an Maryama, sai gã mutãnenka daga gare shi (shi misalin) sunã dãriya da izgili.0 Views
- وَقَالُوا أَآلِهَتُنَا خَيْرٌ أَمْ هُوَ ۚ مَا ضَرَبُوهُ لَكَ إِلَّا جَدَلًا ۚ بَلْ هُمْ قَوْمٌ خَصِمُونَKuma suka ce: "Shin, gumãkanmu ne mafĩfĩta kõ shi (¦an Maryama)?" Ba su buga wannan misãli ba a gare ka fãce dõmin yin jidãli. Ã'a, sũ mutãne nemãsu husũma.0 Views
- إِنْ هُوَ إِلَّا عَبْدٌ أَنْعَمْنَا عَلَيْهِ وَجَعَلْنَاهُ مَثَلًا لِّبَنِي إِسْرَائِيلَShi (¦an Maryama) bai zama ba fãce wani bãwa ne, Mun yi ni'ima a gare shi, kuma Muka sanya shi abin kõyi ga Banĩ Isrã'ĩla.0 Views
- وَلَوْ نَشَاءُ لَجَعَلْنَا مِنكُم مَّلَائِكَةً فِي الْأَرْضِ يَخْلُفُونَKuma dã Munã so lalle ne dã Mun sanya malã'iku, daga ci, kinku, a cikin ƙasa, sunã mayẽwa0 Views
- وَإِنَّهُ لَعِلْمٌ لِّلسَّاعَةِ فَلَا تَمْتَرُنَّ بِهَا وَاتَّبِعُونِ ۚ هَـٰذَا صِرَاطٌ مُّسْتَقِيمٌKuma lalle shĩ, haƙĩƙa, wani ilmi ne na Sa'a, sabõda haka, kada ku yi shakka a gare ta, kuma ku bĩ Ni. Wannan ita ce hanya madaidaiciya.0 Views
- وَلَا يَصُدَّنَّكُمُ الشَّيْطَانُ ۖ إِنَّهُ لَكُمْ عَدُوٌّ مُّبِينٌKuma kada Shaiɗan ya taushe ku (daga hanyar). Lalle shĩ maƙiyi ne a gare ku, mai bayyanãwar ƙiyayya.0 Views
- وَلَمَّا جَاءَ عِيسَىٰ بِالْبَيِّنَاتِ قَالَ قَدْ جِئْتُكُم بِالْحِكْمَةِ وَلِأُبَيِّنَ لَكُم بَعْضَ الَّذِي تَخْتَلِفُونَ فِيهِ ۖ فَاتَّقُوا اللَّهَ وَأَطِيعُونِKuma a lõkacin da Ĩsã ya jẽ da hujjõji bayyanannu, ya ce: "Lalle ne nã zo muku da hikima kuma dõmin in bayyana muku, sãshen abin da kuke sãɓã wa jũna acikinsa, sabõda haka ku bi Allah da taƙawa, kuma ku yi mini ɗã'a."0 Views
- إِنَّ اللَّهَ هُوَ رَبِّي وَرَبُّكُمْ فَاعْبُدُوهُ ۚ هَـٰذَا صِرَاطٌ مُّسْتَقِيمٌ"Lalle ne, Allah Shĩ ne Ubangijina kuma Shi ne Ubangijinku sabõda haka ku bauta Masa. Wannan ita ce hanya madaidaiciya."0 Views
- فَاخْتَلَفَ الْأَحْزَابُ مِن بَيْنِهِمْ ۖ فَوَيْلٌ لِّلَّذِينَ ظَلَمُوا مِنْ عَذَابِ يَوْمٍ أَلِيمٍSai ƙungiyõyi suka sãɓa a tsakãninsu. To, bone yã tabbata ga waɗanda suka yi zãlunci daga azãbar yini mai raɗaɗi!0 Views
- هَلْ يَنظُرُونَ إِلَّا السَّاعَةَ أَن تَأْتِيَهُم بَغْتَةً وَهُمْ لَا يَشْعُرُونَShin sunã jiran wani abu ne? sai dai Sa'a ta jẽ musu bisaga abke, alhãli kuwa ba su sani ba.0 Views
- الْأَخِلَّاءُ يَوْمَئِذٍ بَعْضُهُمْ لِبَعْضٍ عَدُوٌّ إِلَّا الْمُتَّقِينَMasõya a yinin nan, sãshensu zuwa ga sãshe maƙiya ne, fãce mãsu taƙawa (sũ kam mãsu son jũna ne).0 Views
- يَا عِبَادِ لَا خَوْفٌ عَلَيْكُمُ الْيَوْمَ وَلَا أَنتُمْ تَحْزَنُونَYa bãyĩNa! Bãbu tsõro a kanku a yau, kuma bã zã ku yi baƙin ciki ba.0 Views
- الَّذِينَ آمَنُوا بِآيَاتِنَا وَكَانُوا مُسْلِمِينَWaɗanda suka yi ĩmãni da ãyõyinMu, kuma suka kasance mãsu sallamawar al'amari (ga Allah).0 Views
- ادْخُلُوا الْجَنَّةَ أَنتُمْ وَأَزْوَاجُكُمْ تُحْبَرُونَKu shiga Aljanna, kũ da mãtan aurenku, anã girmama ku.0 Views
- يُطَافُ عَلَيْهِم بِصِحَافٍ مِّن ذَهَبٍ وَأَكْوَابٍ ۖ وَفِيهَا مَا تَشْتَهِيهِ الْأَنفُسُ وَتَلَذُّ الْأَعْيُنُ ۖ وَأَنتُمْ فِيهَا خَالِدُونَAnã kẽwayãwa a kansu da akussa na zĩnãriya da kõfuna, alhãli kuwa a cikinsu akwai abin da rãyuka ke marmari kuma idãnu su ji dãɗi, kuma kũ, a cikinta (Aljannar), madawwama ne.0 Views
- وَتِلْكَ الْجَنَّةُ الَّتِي أُورِثْتُمُوهَا بِمَا كُنتُمْ تَعْمَلُونَKuma waccan ita ce Aljannar, wannan da aka gãdar da ku ita sabõda abin da kuka kasance kunã aikatãwa.0 Views
- لَكُمْ فِيهَا فَاكِهَةٌ كَثِيرَةٌ مِّنْهَا تَأْكُلُونَKunã sãmu, a cikinta, 'yã'yan itãcen marmari mãsu yawa, daga cikinsu kuke ci.0 Views
- إِنَّ الْمُجْرِمِينَ فِي عَذَابِ جَهَنَّمَ خَالِدُونَLalle mãsu laifi madawwama ne a cikin azãbar Jahannama.0 Views
- لَا يُفَتَّرُ عَنْهُمْ وَهُمْ فِيهِ مُبْلِسُونَBã a sauƙaƙar da ita (azãbar) daga gare su, alhãli kuwa sũ, a cikinta, mãsu kãsa magana ne.0 Views
- وَمَا ظَلَمْنَاهُمْ وَلَـٰكِن كَانُوا هُمُ الظَّالِمِينَKuma ba Mu zãlunce su ba, amma sũ ne suka kasance azzãlumai.0 Views
- وَنَادَوْا يَا مَالِكُ لِيَقْضِ عَلَيْنَا رَبُّكَ ۖ قَالَ إِنَّكُم مَّاكِثُونَKuma suka yi kira, "Ya Mãliku! Ubangijinka Ya kashe mu mana " (Mãliku) ya ce: "Lalle kũ mazauna ne."0 Views
- لَقَدْ جِئْنَاكُم بِالْحَقِّ وَلَـٰكِنَّ أَكْثَرَكُمْ لِلْحَقِّ كَارِهُونَLalle ne, haƙĩƙa, Mun jẽ muku da gaskiya, kuma amma mafi yawanku mãsu ƙi ga gaskiyar ne.0 Views
- أَمْ أَبْرَمُوا أَمْرًا فَإِنَّا مُبْرِمُونَKõ kuma sun tukka wani al'amari ne? To, lalle Mũ, Mãsu tukkãwa ne.0 Views
- أَمْ يَحْسَبُونَ أَنَّا لَا نَسْمَعُ سِرَّهُمْ وَنَجْوَاهُم ۚ بَلَىٰ وَرُسُلُنَا لَدَيْهِمْ يَكْتُبُونَKo sunã zaton lalle Mũ, bã Mu jin asĩrinsu da gãnãwarsu? Na'am! Kuma manzannin Mu na tãre da su sunã rubũtãwa.0 Views
- قُلْ إِن كَانَ لِلرَّحْمَـٰنِ وَلَدٌ فَأَنَا أَوَّلُ الْعَابِدِينَKa ce: "Idan har akwai ɗã ga Mai rahama, to, nĩ ne farkon mãsu bauta (wa ɗan)."0 Views
- سُبْحَانَ رَبِّ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ رَبِّ الْعَرْشِ عَمَّا يَصِفُونَTsarkin Ubangijin sammai da ƙasa, Ubangijin Al'arshi, ya tabbata daga abin da suke sifantãwa.0 Views
- فَذَرْهُمْ يَخُوضُوا وَيَلْعَبُوا حَتَّىٰ يُلَاقُوا يَوْمَهُمُ الَّذِي يُوعَدُونَSabõda haka, ka ƙyãlẽ su, su kũtsa kuma su yi wãsã har su haɗu da yininsu, wanda ake yi musu wa'adi da shi.0 Views
- وَهُوَ الَّذِي فِي السَّمَاءِ إِلَـٰهٌ وَفِي الْأَرْضِ إِلَـٰهٌ ۚ وَهُوَ الْحَكِيمُ الْعَلِيمُKuma Shĩ ne wanda ke abin bautãwa a sama kuma abin bautãwa a ƙasa, kuma, Shĩ ne Mai hikima, Masani.0 Views
- وَتَبَارَكَ الَّذِي لَهُ مُلْكُ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ وَمَا بَيْنَهُمَا وَعِندَهُ عِلْمُ السَّاعَةِ وَإِلَيْهِ تُرْجَعُونَKuma albarkar wanda ke da mulkin sammai da ƙasã abin da ke a tsakãninsu tã bayyana, kuma a wurinSa ne ilmin Sa'a yake, kuma zuwa gare Shi ake mayar da ku.0 Views
- وَلَا يَمْلِكُ الَّذِينَ يَدْعُونَ مِن دُونِهِ الشَّفَاعَةَ إِلَّا مَن شَهِدَ بِالْحَقِّ وَهُمْ يَعْلَمُونَKuma waɗanda suke kira baicinSa ba su mallaki cẽto ba, fãce wanda ya yi shaida da gaskiya, kuma sũ, sunã sane (da haka).0 Views
- وَلَئِن سَأَلْتَهُم مَّنْ خَلَقَهُمْ لَيَقُولُنَّ اللَّهُ ۖ فَأَنَّىٰ يُؤْفَكُونَKuma lalle idan ka tambaye su: "Wãne ne ya halitta su?" Lalle ne zã su ce Allah ne. To, yãya ake jũyar da su?0 Views
- وَقِيلِهِ يَا رَبِّ إِنَّ هَـٰؤُلَاءِ قَوْمٌ لَّا يُؤْمِنُونَKuma da (ilmin) maganarSa (Annabi) "Ya Ubangijĩna! Lalle waɗannan mutãne ne waɗanda bã zã su yi ĩmãni ba."0 Views
- فَاصْفَحْ عَنْهُمْ وَقُلْ سَلَامٌ ۚ فَسَوْفَ يَعْلَمُونَTo, sai ka kau da kai daga gare su, kuma ka ce, "salãmã." Sa'an nan kuma zã su sani.0 Views
Surah ad-dukhan
Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
- حمٓḤ. M̃.0 Views
- وَالْكِتَابِ الْمُبِينِInã rantsuwa da Littãfi Mabayyani.0 Views
- إِنَّا أَنزَلْنَاهُ فِي لَيْلَةٍ مُّبَارَكَةٍ ۚ إِنَّا كُنَّا مُنذِرِينَLalle ne, Mũ, Muka saukar da shi a cikin wani dare mai albarka. Lalle Mũ' Mun kasance Mãsu yin gargaɗi.0 Views
- فِيهَا يُفْرَقُ كُلُّ أَمْرٍ حَكِيمٍA cikinsa (shi daren) ake rarrabe kõwane umurui bayyananne.0 Views
- أَمْرًا مِّنْ عِندِنَا ۚ إِنَّا كُنَّا مُرْسِلِينَUmurni na daga wurinMu. Lalle Mũ ne Muka kasanceMãsu aikãwã.0 Views
- رَحْمَةً مِّن رَّبِّكَ ۚ إِنَّهُ هُوَ السَّمِيعُ الْعَلِيمُSabõda rahama daga Ubangijinka. Lalle Shĩ, Shi ne Mai ji, Mãsani.0 Views
- رَبِّ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ وَمَا بَيْنَهُمَا ۖ إِن كُنتُم مُّوقِنِينَ(Shĩ ne) Ubangijin sammai da ƙasa da abin da ke a tsakãninsu, idan kun kasance mãsu yaƙĩni (za ku gãne haka).0 Views
- لَا إِلَـٰهَ إِلَّا هُوَ يُحْيِي وَيُمِيتُ ۖ رَبُّكُمْ وَرَبُّ آبَائِكُمُ الْأَوَّلِينَBabu abin bautãwa fãce Shi. Yana rãyarwa Kuma Yana kashẽwa. (Shi ne) Ubangijinku, kuma Ubangijin ubanninku na farko.0 Views
- بَلْ هُمْ فِي شَكٍّ يَلْعَبُونَA'a sũ, sunã wãsã a cikin shakka.0 Views
- فَارْتَقِبْ يَوْمَ تَأْتِي السَّمَاءُ بِدُخَانٍ مُّبِينٍSabõda haka, ka dakata rãnar da sama zã tã zo da hayãƙi bayyananne.0 Views
- يَغْشَى النَّاسَ ۖ هَـٰذَا عَذَابٌ أَلِيمٌYanã rufe mutãne. Wannan wata azãba ce mai raɗaɗi.0 Views
- رَّبَّنَا اكْشِفْ عَنَّا الْعَذَابَ إِنَّا مُؤْمِنُونَYa Ubangijinmu! Ka kuranye mana azãba. Lalle Mũ, mãsu ĩmãni ne.0 Views
- أَنَّىٰ لَهُمُ الذِّكْرَىٰ وَقَدْ جَاءَهُمْ رَسُولٌ مُّبِينٌInã tunãwa take a gare su, alhãli kuwa, haƙĩƙa, Manzo mai bayyanãwa Ya je musu (da gargaɗin saukar azãbar, ba su karɓa ba)?0 Views
- ثُمَّ تَوَلَّوْا عَنْهُ وَقَالُوا مُعَلَّمٌ مَّجْنُونٌSa'an nan suka jũya baya daga gare shi, Kuma suka ce: "Wanda ake gayãwa ne, mahaukaci."0 Views
- إِنَّا كَاشِفُو الْعَذَابِ قَلِيلًا ۚ إِنَّكُمْ عَائِدُونَLalle Mũ, Mãsu kuranyẽwar azãba ne, a ɗan lõkaci kaɗan, lalle kũ, mãsu kõmãwa ne (ga laifin).0 Views
- يَوْمَ نَبْطِشُ الْبَطْشَةَ الْكُبْرَىٰ إِنَّا مُنتَقِمُونَRãnar da Muke damƙa, damƙa mafi girma, lalle ne Mũ mãsu azãbar rãmuwa ne.0 Views
- ۞ وَلَقَدْ فَتَنَّا قَبْلَهُمْ قَوْمَ فِرْعَوْنَ وَجَاءَهُمْ رَسُولٌ كَرِيمٌKuma lalle ne haƙĩƙa a gabaninsu, Mun fitini mutãnen Fir'auna, kuma wani Manzo karĩmi ya jẽ musu.0 Views
- أَنْ أَدُّوا إِلَيَّ عِبَادَ اللَّهِ ۖ إِنِّي لَكُمْ رَسُولٌ أَمِينٌ(Mazon ya ce): "Ku kãwo mini (ĩmãninku) ya bayin Allah! Lalle ni, Manzo ne amintacce zuwa gare ku."0 Views
- وَأَن لَّا تَعْلُوا عَلَى اللَّهِ ۖ إِنِّي آتِيكُم بِسُلْطَانٍ مُّبِينٍ"Kuma kada ku nẽmi ɗaukaka a kan Allah. Lalle nĩ mai zo muku ne da dalĩli bayyananne."0 Views
- وَإِنِّي عُذْتُ بِرَبِّي وَرَبِّكُمْ أَن تَرْجُمُونِ"Kuma lalle nĩ na nẽmi tsari da Ubangijĩna, kuma Ubangijinku, dõmin kada ku jẽfe ni."0 Views
- وَإِن لَّمْ تُؤْمِنُوا لِي فَاعْتَزِلُونِ"Kuma idan ba ku yi ĩmãni sabõda nĩ ba, to, ku nĩsance ni."0 Views
- فَدَعَا رَبَّهُ أَنَّ هَـٰؤُلَاءِ قَوْمٌ مُّجْرِمُونَSai ya kirayi Ubangjinsa cẽwa waɗannan mutãnene mãsu laifi.0 Views
- فَأَسْرِ بِعِبَادِي لَيْلًا إِنَّكُم مُّتَّبَعُونَ(Allah Ya ce): "To, ka yi tafiyar dare da bayiNa, da dare. Lalle kũ, waɗanda ake bĩ ne (dõmin a kãma ku.)"0 Views
- وَاتْرُكِ الْبَحْرَ رَهْوًا ۖ إِنَّهُمْ جُندٌ مُّغْرَقُونَ"Kuma ka bar tẽku rarrabe. Lalle sũ, runduna ce abar nutsarwa."0 Views
- كَمْ تَرَكُوا مِن جَنَّاتٍ وَعُيُونٍDa yawa suka bar gõnaki da marẽmari.0 Views
- وَزُرُوعٍ وَمَقَامٍ كَرِيمٍDa shuke-shuke da matsayi mai kyau.0 Views
- وَنَعْمَةٍ كَانُوا فِيهَا فَاكِهِينَDa wata ni'ima da suka kasance a cikinta sunã mãsu hutu.0 Views
- كَذَٰلِكَ ۖ وَأَوْرَثْنَاهَا قَوْمًا آخَرِينَKamar haka! Kuma Muka gãdar da ita ga waɗansu mutãne na dabam.0 Views
- فَمَا بَكَتْ عَلَيْهِمُ السَّمَاءُ وَالْأَرْضُ وَمَا كَانُوا مُنظَرِينَSa'an nan samã da ƙasã ba su yi kũka a kansu ba, Kuma ba su kasance waɗanda ake yi wa jinkiri ba.0 Views
- وَلَقَدْ نَجَّيْنَا بَنِي إِسْرَائِيلَ مِنَ الْعَذَابِ الْمُهِينِKuma lalle ne, haƙĩƙa Mun tsĩrar da Banĩ Isrã'ĩla daga, azãba mai wulãkantãwa.0 Views
- مِن فِرْعَوْنَ ۚ إِنَّهُ كَانَ عَالِيًا مِّنَ الْمُسْرِفِينَDaga Fir'auna. Lalle shi, ya kasance maɗaukaki daga cikin mãsu ɓarna.0 Views
- وَلَقَدِ اخْتَرْنَاهُمْ عَلَىٰ عِلْمٍ عَلَى الْعَالَمِينَKuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun zãɓe su sabõda wani ilmi (na Taurata) a kan mutãne.0 Views
- وَآتَيْنَاهُم مِّنَ الْآيَاتِ مَا فِيهِ بَلَاءٌ مُّبِينٌKuma Muka bã su, daga ãyõyin mu'ujizõji, abin da yake a cikinsa, akwai ni'ima bayyananna0 Views
- إِنَّ هَـٰؤُلَاءِ لَيَقُولُونَLalle waɗannan mutãne, haƙĩka, sunã cẽwa,0 Views
- إِنْ هِيَ إِلَّا مَوْتَتُنَا الْأُولَىٰ وَمَا نَحْنُ بِمُنشَرِينَ"Babu wani abu sai mutuwarmu ta farko, kuma ba mu zama waɗanda ake tãyarwa ba."0 Views
- فَأْتُوا بِآبَائِنَا إِن كُنتُمْ صَادِقِينَ"Sai ku zo da ubanninmu, idan kun kasance mãsu gaskiya."0 Views
- أَهُمْ خَيْرٌ أَمْ قَوْمُ تُبَّعٍ وَالَّذِينَ مِن قَبْلِهِمْ ۚ أَهْلَكْنَاهُمْ ۖ إِنَّهُمْ كَانُوا مُجْرِمِينَshin, sũ ne mafĩfĩta kõ kuwa mutãnen Tubba'u, kuma da waɗanda ke a gabãninsu? Mun halaka su, lalle sũ, sun kasance mãsu laifi.0 Views
- وَمَا خَلَقْنَا السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضَ وَمَا بَيْنَهُمَا لَاعِبِينَKuma ba Mu halitta slmmai da ƙasa da abin da ke a tsakãninsu ba, alhãli kuwa Munã mãsu wãsã.0 Views
- مَا خَلَقْنَاهُمَا إِلَّا بِالْحَقِّ وَلَـٰكِنَّ أَكْثَرَهُمْ لَا يَعْلَمُونَBa Mu halitta su ba fãce da manufa ta gaskiya, kuma amma mafi yawansu, ba su sani ba.0 Views
- إِنَّ يَوْمَ الْفَصْلِ مِيقَاتُهُمْ أَجْمَعِينَLalle rãnar rarrabẽwa, ita ce lõkacin wa'adinsu gabã ɗaya.0 Views
- يَوْمَ لَا يُغْنِي مَوْلًى عَن مَّوْلًى شَيْئًا وَلَا هُمْ يُنصَرُونَRãnar da wani zumu bã ya amfãnin wani zumu da kõme kuma ba su zama anã taimakon su ba.0 Views
- إِلَّا مَن رَّحِمَ اللَّهُ ۚ إِنَّهُ هُوَ الْعَزِيزُ الرَّحِيمُfãce wanda Allah Ya yi wa rahama. Lalle Shi (Allah), shĩ ne Mabuwãyi, Mai jin ƙai.0 Views
- إِنَّ شَجَرَتَ الزَّقُّومِLalle itãciyar zaƙƙũm (ɗanyen wutã),0 Views
- طَعَامُ الْأَثِيمِIta ce abincin mai laifi.0 Views
- كَالْمُهْلِ يَغْلِي فِي الْبُطُونِKamar narkakken kwalta yanã tafasa a cikin cikunna.0 Views
- كَغَلْيِ الْحَمِيمِKamar tafasar ruwan zãfi.0 Views
- خُذُوهُ فَاعْتِلُوهُ إِلَىٰ سَوَاءِ الْجَحِيمِ(A cẽ wa malã'ikun wutã), "Ku kãmã shi, sa'an nan ku fizge shi zuwa ga tsakiyar Jahĩm."0 Views
- ثُمَّ صُبُّوا فَوْقَ رَأْسِهِ مِنْ عَذَابِ الْحَمِيمِ"Sa'an nan ku zuba, a kansa, daga azãbar ruwan zãfi."0 Views
- ذُقْ إِنَّكَ أَنتَ الْعَزِيزُ الْكَرِيمُ(A ce masã), "Ka ɗanɗana! Lalle kai, kai ne mabuwãyi mai girma!"0 Views
- إِنَّ هَـٰذَا مَا كُنتُم بِهِ تَمْتَرُونَ"Lalle wannan, shi ne abin da kuka kasance kunã shakka game da shi."0 Views
- إِنَّ الْمُتَّقِينَ فِي مَقَامٍ أَمِينٍLalle mãsu taƙawa sunã cikin matsayi amintacce.0 Views
- فِي جَنَّاتٍ وَعُيُونٍA cikin gidãjen Aljanna da marẽmari.0 Views
- يَلْبَسُونَ مِن سُندُسٍ وَإِسْتَبْرَقٍ مُّتَقَابِلِينَSunã tufanta daga tufãfin alharĩni raƙĩƙi, da mai kauri, sunã mãsu zaman fuskantar jũna.0 Views
- كَذَٰلِكَ وَزَوَّجْنَاهُم بِحُورٍ عِينٍKamar haka, kuma Mun aurar da su da mãtã mãsu kyaun idãnu, mãsu girmansu.0 Views
- يَدْعُونَ فِيهَا بِكُلِّ فَاكِهَةٍ آمِنِينَSunã kira, a cikinsu (gidẽjen) ga dukan 'ya'yan itãcen marmari, sunã amintattu (daga dukan abin tsõro).0 Views
- لَا يَذُوقُونَ فِيهَا الْمَوْتَ إِلَّا الْمَوْتَةَ الْأُولَىٰ ۖ وَوَقَاهُمْ عَذَابَ الْجَحِيمِBã su ɗanɗanar mutuwa, a cikinsu, fãce mutuwar farko, kuma (Allah), Ya tsare musu azãbar Jahĩm.0 Views
- فَضْلًا مِّن رَّبِّكَ ۚ ذَٰلِكَ هُوَ الْفَوْزُ الْعَظِيمُSabõda falala daga Ubangijinka. Wancan shi ne babban rabo, mai girma.0 Views
- فَإِنَّمَا يَسَّرْنَاهُ بِلِسَانِكَ لَعَلَّهُمْ يَتَذَكَّرُونَDõmin haka kawai Muka sauƙaƙar da shi (Alƙur'ãni) da harshenka, tsammãninsu, su riƙa tunãwa.0 Views
- فَارْتَقِبْ إِنَّهُم مُّرْتَقِبُونَSai ka yi jira. Lalle sũ, mãsu jira ne.0 Views
Surah al-jathiyah
Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
- حمٓḤ. M̃.0 Views
- تَنزِيلُ الْكِتَابِ مِنَ اللَّهِ الْعَزِيزِ الْحَكِيمِSaukar Littãfi daga Allah Mabuwãyi Mai hikima yake.0 Views
- إِنَّ فِي السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ لَآيَاتٍ لِّلْمُؤْمِنِينَLalle ne a cikin sammai da ƙasa akwai ãyõyi ga mãsu ĩmãni.0 Views
- وَفِي خَلْقِكُمْ وَمَا يَبُثُّ مِن دَابَّةٍ آيَاتٌ لِّقَوْمٍ يُوقِنُونَKuma a cikin halittarku da abin da ke watsuwa na dabba akwai ãyõyi ga mutãne mãsu yaƙĩni.0 Views
- وَاخْتِلَافِ اللَّيْلِ وَالنَّهَارِ وَمَا أَنزَلَ اللَّهُ مِنَ السَّمَاءِ مِن رِّزْقٍ فَأَحْيَا بِهِ الْأَرْضَ بَعْدَ مَوْتِهَا وَتَصْرِيفِ الرِّيَاحِ آيَاتٌ لِّقَوْمٍ يَعْقِلُونَKuma da sãɓawar dare da yini da abin da Allah Ya saukar daga sama na arziki, sa'an nan Ya rãyar da ƙasa game da shi a bãyan mutuwarta, da jũyawar iskõki, akwai ãyõyi ga mutãne mãsu yin hankali.0 Views
- تِلْكَ آيَاتُ اللَّهِ نَتْلُوهَا عَلَيْكَ بِالْحَقِّ ۖ فَبِأَيِّ حَدِيثٍ بَعْدَ اللَّهِ وَآيَاتِهِ يُؤْمِنُونَWaɗancan ãyõyin Allah ne, Munã karanta su gare ka da gaskiya. To, da wane lãbãri bãyan Allah da ãyõyinSa suke yin ĩmãni?0 Views
- وَيْلٌ لِّكُلِّ أَفَّاكٍ أَثِيمٍBone ya tabbata ga dukan mai yawan ƙiren ƙarya, mai laifi.0 Views
- يَسْمَعُ آيَاتِ اللَّهِ تُتْلَىٰ عَلَيْهِ ثُمَّ يُصِرُّ مُسْتَكْبِرًا كَأَن لَّمْ يَسْمَعْهَا ۖ فَبَشِّرْهُ بِعَذَابٍ أَلِيمٍYanã jin ãyõyin Allah anã karanta su a kansa, sa'an nan ya dõge yanã makãngari, kamar bai jĩ su ba. To, ka yi masa bushara da azãba mai raɗaɗi.3 Views
- وَإِذَا عَلِمَ مِنْ آيَاتِنَا شَيْئًا اتَّخَذَهَا هُزُوًا ۚ أُولَـٰئِكَ لَهُمْ عَذَابٌ مُّهِينٌKuma har idan ya san wani abu daga ãyõyinMu, sai ya rika su da izgili. Waɗancan sunã da wata azãba mai wulãkantãwa (a dũniya).3 Views
- مِّن وَرَائِهِمْ جَهَنَّمُ ۖ وَلَا يُغْنِي عَنْهُم مَّا كَسَبُوا شَيْئًا وَلَا مَا اتَّخَذُوا مِن دُونِ اللَّهِ أَوْلِيَاءَ ۖ وَلَهُمْ عَذَابٌ عَظِيمٌGaba gare su (a Lãhira) akwai Jahannama, kuma abin da suka sanã'anta bã ya wadãtar da su daga kõme, kuma abũbuwan da suka riƙa majiɓinta, baicin Allah, bã su wãdatar da su daga kõme. Kuma sunã da wata azãba mai girma.0 Views
- هَـٰذَا هُدًى ۖ وَالَّذِينَ كَفَرُوا بِآيَاتِ رَبِّهِمْ لَهُمْ عَذَابٌ مِّن رِّجْزٍ أَلِيمٌWannan (Alƙur'ãni) shi ne shiryuwa. Kuma waɗanda suka kãfirta game da ãyõyin Ubangijinsu, sunã da wata azãba ta wulãkanci mai raɗaɗi.0 Views
- ۞ اللَّهُ الَّذِي سَخَّرَ لَكُمُ الْبَحْرَ لِتَجْرِيَ الْفُلْكُ فِيهِ بِأَمْرِهِ وَلِتَبْتَغُوا مِن فَضْلِهِ وَلَعَلَّكُمْ تَشْكُرُونَAllah ne wanda Ya hõre muku tẽku dõmin jirgi ya gudãna a cikinta da umurninSa, kuma dõmin ku nẽma daga falalarSa, kuma tsammãninku zã ku gõde.0 Views
- وَسَخَّرَ لَكُم مَّا فِي السَّمَاوَاتِ وَمَا فِي الْأَرْضِ جَمِيعًا مِّنْهُ ۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَآيَاتٍ لِّقَوْمٍ يَتَفَكَّرُونَKuma Ya hõre muku abin da ke a cikin sammai da abin da ke a cikin ƙasa, gabã ɗaya daga gare Shi yake. Lalle ne, a cikin wancan, haƙĩƙa, akwai ãyõyi ga mutãne waɗanda ke yin tunãni.0 Views
- قُل لِّلَّذِينَ آمَنُوا يَغْفِرُوا لِلَّذِينَ لَا يَرْجُونَ أَيَّامَ اللَّهِ لِيَجْزِيَ قَوْمًا بِمَا كَانُوا يَكْسِبُونَKa ce wa waɗanda suka yi ĩmãni, su yi gãfara ga waɗanda bã su fãtan rahama ga kwãnukan Allah, dõmin (Allah) Ya sãka wa mutãne da abin da suka kasance sunã aikatãwa.0 Views
- مَنْ عَمِلَ صَالِحًا فَلِنَفْسِهِ ۖ وَمَنْ أَسَاءَ فَعَلَيْهَا ۖ ثُمَّ إِلَىٰ رَبِّكُمْ تُرْجَعُونَWanda ya aikata aikin ƙwarai, to, dõmin kansã, kuma wanda ya mũnana aki, to, a kansa. Sa'an nan zuwa ga Ubangijinku ake mayar da ku.0 Views
- وَلَقَدْ آتَيْنَا بَنِي إِسْرَائِيلَ الْكِتَابَ وَالْحُكْمَ وَالنُّبُوَّةَ وَرَزَقْنَاهُم مِّنَ الطَّيِّبَاتِ وَفَضَّلْنَاهُمْ عَلَى الْعَالَمِينَKuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun bai (wa Bãnĩ Isrã'ĩla Littãfi da hukunci da Annabci, Kuma Mun azurta su daga abũbuwa mãsudãɗi, Kuma Mun fĩfta su a kan mutãnen dũniya (a zãmaninsu).0 Views
- وَآتَيْنَاهُم بَيِّنَاتٍ مِّنَ الْأَمْرِ ۖ فَمَا اخْتَلَفُوا إِلَّا مِن بَعْدِ مَا جَاءَهُمُ الْعِلْمُ بَغْيًا بَيْنَهُمْ ۚ إِنَّ رَبَّكَ يَقْضِي بَيْنَهُمْ يَوْمَ الْقِيَامَةِ فِيمَا كَانُوا فِيهِ يَخْتَلِفُونَKuma Muka bã su hujjõji na umurni. Ba su sãɓa ba fãce bãyan ilmi ya jẽ musu, sabõda zãlunci a tsakãninsu. Lalle ne, Ubangijinka zai yi hukunci a tsakãninsu, a Rãnar ƙiyãma a cikin abin da suka kasance sunã sãɓa wa (jũna).0 Views
- ثُمَّ جَعَلْنَاكَ عَلَىٰ شَرِيعَةٍ مِّنَ الْأَمْرِ فَاتَّبِعْهَا وَلَا تَتَّبِعْ أَهْوَاءَ الَّذِينَ لَا يَعْلَمُونَSa'an nan Muka sanya ka a kan wata sharĩ'a ta al'amarin. Sai ka bĩ ta, Kuma kada kã bi son zũciyõyin waɗannan daba su sani ba.0 Views
- إِنَّهُمْ لَن يُغْنُوا عَنكَ مِنَ اللَّهِ شَيْئًا ۚ وَإِنَّ الظَّالِمِينَ بَعْضُهُمْ أَوْلِيَاءُ بَعْضٍ ۖ وَاللَّهُ وَلِيُّ الْمُتَّقِينَLalle ne sũ, bã zã su wadãtar da kai da kõme ba daga Allah. Kuma lalle ne azzãlumai sãshensu majiɓintan sãshe ne. Kuma Allah ne Majiɓincin mãsu taƙawa.0 Views
- هَـٰذَا بَصَائِرُ لِلنَّاسِ وَهُدًى وَرَحْمَةٌ لِّقَوْمٍ يُوقِنُونَwannan (Alkur'ãni) hukunce-hukuncen natsuwa ne ga mutãne, da shiryuwa, da rahama, ga mutãne waɗanda ke da yaƙĩni.0 Views
- أَمْ حَسِبَ الَّذِينَ اجْتَرَحُوا السَّيِّئَاتِ أَن نَّجْعَلَهُمْ كَالَّذِينَ آمَنُوا وَعَمِلُوا الصَّالِحَاتِ سَوَاءً مَّحْيَاهُمْ وَمَمَاتُهُمْ ۚ سَاءَ مَا يَحْكُمُونَKõ waɗanda suka yãgi miyãgun ayyuka sunã zaton Mu sanyã su kamar waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, su zama daidai ga rãyuwarsu da mutuwarsu? Abin da suke hukuntãwa yã mũnanã!0 Views
- وَخَلَقَ اللَّهُ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضَ بِالْحَقِّ وَلِتُجْزَىٰ كُلُّ نَفْسٍ بِمَا كَسَبَتْ وَهُمْ لَا يُظْلَمُونَAlhãli kuwa Allah ne Ya halitta sammai da ƙasã sabõda gaskiya, Kuma dõmin a sãka wa kõwane rai da abin da ya sanã'anta, kuma su, bã zã a zãlunce su ba.0 Views
- أَفَرَأَيْتَ مَنِ اتَّخَذَ إِلَـٰهَهُ هَوَاهُ وَأَضَلَّهُ اللَّهُ عَلَىٰ عِلْمٍ وَخَتَمَ عَلَىٰ سَمْعِهِ وَقَلْبِهِ وَجَعَلَ عَلَىٰ بَصَرِهِ غِشَاوَةً فَمَن يَهْدِيهِ مِن بَعْدِ اللَّهِ ۚ أَفَلَا تَذَكَّرُونَShin, kã ga wanda ya riƙi son zũciyarsa sĩh ne abin bautawarsa, kuma Allah Ya ɓatar da shi a kan wani ilmi, Kuma Ya sa hatini a kan jinsa, da zũciyarsa, kuma Ya sa wata yãnã ã kan ganinsa? To, wãne ne zai shiryar da shi bãyan Allah? Shin to, bã zã ku yi tunãni ba?0 Views
- وَقَالُوا مَا هِيَ إِلَّا حَيَاتُنَا الدُّنْيَا نَمُوتُ وَنَحْيَا وَمَا يُهْلِكُنَا إِلَّا الدَّهْرُ ۚ وَمَا لَهُم بِذَٰلِكَ مِنْ عِلْمٍ ۖ إِنْ هُمْ إِلَّا يَظُنُّونَKuma suka ce: "Bãbu kõme fãce rãyuwarmu ta dũniya; munã mutuwa kuma munã rãyuwa (da haihuwa) kuma bãbu abin da ke halaka mu sai zãmani." Alhãli kuwa (ko da suke faɗar maganar) bã su da wani ilmi game da wannan, bã su bin kõme face zato.3 Views
- وَإِذَا تُتْلَىٰ عَلَيْهِمْ آيَاتُنَا بَيِّنَاتٍ مَّا كَانَ حُجَّتَهُمْ إِلَّا أَن قَالُوا ائْتُوا بِآبَائِنَا إِن كُنتُمْ صَادِقِينَKuma idan anã karanta ãyõyinMu bayyanannu a kansu, bãbu abin da ya kasance hujjarsu fãce suka ce: "Ku zo mana da ubanninmu, idan kun kasance mãsu gaskiya."0 Views
- قُلِ اللَّهُ يُحْيِيكُمْ ثُمَّ يُمِيتُكُمْ ثُمَّ يَجْمَعُكُمْ إِلَىٰ يَوْمِ الْقِيَامَةِ لَا رَيْبَ فِيهِ وَلَـٰكِنَّ أَكْثَرَ النَّاسِ لَا يَعْلَمُونَKa ce: "Allah ne ke rãyar da ku kuma Shĩ ne ke matarda ku, sa'an nan Ya tãra ku zuwa ga Rãnar ¡iyãma, bãbu shakka a gare ta, kuma amma mafi yawan mutãne ba su sani ba."0 Views
- وَلِلَّهِ مُلْكُ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ ۚ وَيَوْمَ تَقُومُ السَّاعَةُ يَوْمَئِذٍ يَخْسَرُ الْمُبْطِلُونَ"Kuma mulkin sammai da ƙasa na Allah ne, Shĩ kaɗai. Kuma rãnar da Sa'a ke tsayuwa, a rãnar nan mãsu ɓãtãwã (ga hujjõjin Allah dõmin su ki bin sharĩ'arSa) zã su yi hasãra."0 Views
- وَتَرَىٰ كُلَّ أُمَّةٍ جَاثِيَةً ۚ كُلُّ أُمَّةٍ تُدْعَىٰ إِلَىٰ كِتَابِهَا الْيَوْمَ تُجْزَوْنَ مَا كُنتُمْ تَعْمَلُونَKuma zã ka ga kõwace al'umma tanã gurfãne, kõwace al'umma anã kiran ta zuwa ga littãfinta. (A ce musu) "A yau anã sãka muku da abin da kuka kasance kunã aikatãwa."0 Views
- هَـٰذَا كِتَابُنَا يَنطِقُ عَلَيْكُم بِالْحَقِّ ۚ إِنَّا كُنَّا نَسْتَنسِخُ مَا كُنتُمْ تَعْمَلُونَ"Wannan littãfinMu ne yanã yin magana a kanku da gas, kiya. Lalle Mũ, Mun kasanceMuna sauya rubũtun tamkar abin dakuka kasance kunã aikãtãwa."0 Views
- فَأَمَّا الَّذِينَ آمَنُوا وَعَمِلُوا الصَّالِحَاتِ فَيُدْخِلُهُمْ رَبُّهُمْ فِي رَحْمَتِهِ ۚ ذَٰلِكَ هُوَ الْفَوْزُ الْمُبِينُTo, amma waɗanda suka yi ĩmãni kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, to, Ubangijinsu zai sanya su a cikin rahamarsa. Wannan shĩ ne babban rabo bayyananne.0 Views
- وَأَمَّا الَّذِينَ كَفَرُوا أَفَلَمْ تَكُنْ آيَاتِي تُتْلَىٰ عَلَيْكُمْ فَاسْتَكْبَرْتُمْ وَكُنتُمْ قَوْمًا مُّجْرِمِينَKuma amma waɗanda suka kãfirtã (Allah zai ce musu): "Shin, ãyõyĩNã ba su kasance anã karãnta su ã kanku ba sai kuka kangare, Kuma kuka kasance mutãne mãsu laifi?"0 Views
- وَإِذَا قِيلَ إِنَّ وَعْدَ اللَّهِ حَقٌّ وَالسَّاعَةُ لَا رَيْبَ فِيهَا قُلْتُم مَّا نَدْرِي مَا السَّاعَةُ إِن نَّظُنُّ إِلَّا ظَنًّا وَمَا نَحْنُ بِمُسْتَيْقِنِينَ"Kuma idan aka ce, lalle wa'ãdin Allah gaskiya ne, kuma Sa'a, bãbu shakka a cikinta sai kuka ce, 'Ba mu san abin da ake cẽwa Sa'a ba, bã mu zãto (game da ita) fãce zato mai rauni, Kuma ba mu zama mãsu yaƙni ba."'0 Views
- وَبَدَا لَهُمْ سَيِّئَاتُ مَا عَمِلُوا وَحَاقَ بِهِم مَّا كَانُوا بِهِ يَسْتَهْزِئُونَKuma mũnanan abin da suka aikata ya bayyana a gare su, kuma abin da suka kasance sunã yi na izgili ya wajaba a kansu.0 Views
- وَقِيلَ الْيَوْمَ نَنسَاكُمْ كَمَا نَسِيتُمْ لِقَاءَ يَوْمِكُمْ هَـٰذَا وَمَأْوَاكُمُ النَّارُ وَمَا لَكُم مِّن نَّاصِرِينَKuma aka ce: "A yau zã Mu manta da ku, kamar yadda kuka manta da gamuwa da yininku wannan. Kuma mãkõmarku wutã ce, Kuma bã ku da waɗansu mãsu taimako.0 Views
- ذَٰلِكُم بِأَنَّكُمُ اتَّخَذْتُمْ آيَاتِ اللَّهِ هُزُوًا وَغَرَّتْكُمُ الْحَيَاةُ الدُّنْيَا ۚ فَالْيَوْمَ لَا يُخْرَجُونَ مِنْهَا وَلَا هُمْ يُسْتَعْتَبُونَ"Wancan dõmin lalle kũ, kun riƙi ãyõyin Allah da izgili, Kuma rãyuwar dũniya ta rũɗe ku. To, a yau bã zã su fita daga gare ta ba, Kuma bã zã su zama waɗanda ake nẽman yardarsu ba."0 Views
- فَلِلَّهِ الْحَمْدُ رَبِّ السَّمَاوَاتِ وَرَبِّ الْأَرْضِ رَبِّ الْعَالَمِينَSabõda haka, gõdiya ta tabbata ga Allah Ubangijin sammai, kuma Ubangijin ƙasã, Ubangijin halittu.0 Views
- وَلَهُ الْكِبْرِيَاءُ فِي السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ ۖ وَهُوَ الْعَزِيزُ الْحَكِيمُKuma gare Shi girma yake, a cikin sammai da ƙasã, kuma Shĩ ne Mabuwãyi, Mai Hikima.0 Views