Mushaf Page 498
صفحة ٤٩٨
- Ghunnah
- Qalqalah
- Ikhfa (Haqiqi)
- Ikhfa Shafawi
- Idgham with Ghunnah
- Idgham without Ghunnah
- Idgham Shafawi (Mimi)
- Madd Lazim (6 counts)
- Madd Wajib Muttasil (4-5 counts)
- Madd Jaiz Munfasil (2, 4, 6 counts)
Each word’s meaning appears right below it; the transliteration follows below the words.
Surah ad-dukhan
- إِنَّ يَوْمَ الْفَصْلِ مِيقَاتُهُمْ أَجْمَعِينَLalle rãnar rarrabẽwa, ita ce lõkacin wa'adinsu gabã ɗaya.0 Views
- يَوْمَ لَا يُغْنِي مَوْلًى عَن مَّوْلًى شَيْئًا وَلَا هُمْ يُنصَرُونَRãnar da wani zumu bã ya amfãnin wani zumu da kõme kuma ba su zama anã taimakon su ba.0 Views
- إِلَّا مَن رَّحِمَ اللَّهُ ۚ إِنَّهُ هُوَ الْعَزِيزُ الرَّحِيمُfãce wanda Allah Ya yi wa rahama. Lalle Shi (Allah), shĩ ne Mabuwãyi, Mai jin ƙai.0 Views
- إِنَّ شَجَرَتَ الزَّقُّومِLalle itãciyar zaƙƙũm (ɗanyen wutã),0 Views
- طَعَامُ الْأَثِيمِIta ce abincin mai laifi.0 Views
- كَالْمُهْلِ يَغْلِي فِي الْبُطُونِKamar narkakken kwalta yanã tafasa a cikin cikunna.0 Views
- كَغَلْيِ الْحَمِيمِKamar tafasar ruwan zãfi.0 Views
- خُذُوهُ فَاعْتِلُوهُ إِلَىٰ سَوَاءِ الْجَحِيمِ(A cẽ wa malã'ikun wutã), "Ku kãmã shi, sa'an nan ku fizge shi zuwa ga tsakiyar Jahĩm."0 Views
- ثُمَّ صُبُّوا فَوْقَ رَأْسِهِ مِنْ عَذَابِ الْحَمِيمِ"Sa'an nan ku zuba, a kansa, daga azãbar ruwan zãfi."0 Views
- ذُقْ إِنَّكَ أَنتَ الْعَزِيزُ الْكَرِيمُ(A ce masã), "Ka ɗanɗana! Lalle kai, kai ne mabuwãyi mai girma!"0 Views
- إِنَّ هَـٰذَا مَا كُنتُم بِهِ تَمْتَرُونَ"Lalle wannan, shi ne abin da kuka kasance kunã shakka game da shi."0 Views
- إِنَّ الْمُتَّقِينَ فِي مَقَامٍ أَمِينٍLalle mãsu taƙawa sunã cikin matsayi amintacce.0 Views
- فِي جَنَّاتٍ وَعُيُونٍA cikin gidãjen Aljanna da marẽmari.0 Views
- يَلْبَسُونَ مِن سُندُسٍ وَإِسْتَبْرَقٍ مُّتَقَابِلِينَSunã tufanta daga tufãfin alharĩni raƙĩƙi, da mai kauri, sunã mãsu zaman fuskantar jũna.0 Views
- كَذَٰلِكَ وَزَوَّجْنَاهُم بِحُورٍ عِينٍKamar haka, kuma Mun aurar da su da mãtã mãsu kyaun idãnu, mãsu girmansu.0 Views
- يَدْعُونَ فِيهَا بِكُلِّ فَاكِهَةٍ آمِنِينَSunã kira, a cikinsu (gidẽjen) ga dukan 'ya'yan itãcen marmari, sunã amintattu (daga dukan abin tsõro).0 Views
- لَا يَذُوقُونَ فِيهَا الْمَوْتَ إِلَّا الْمَوْتَةَ الْأُولَىٰ ۖ وَوَقَاهُمْ عَذَابَ الْجَحِيمِBã su ɗanɗanar mutuwa, a cikinsu, fãce mutuwar farko, kuma (Allah), Ya tsare musu azãbar Jahĩm.0 Views
- فَضْلًا مِّن رَّبِّكَ ۚ ذَٰلِكَ هُوَ الْفَوْزُ الْعَظِيمُSabõda falala daga Ubangijinka. Wancan shi ne babban rabo, mai girma.0 Views
- فَإِنَّمَا يَسَّرْنَاهُ بِلِسَانِكَ لَعَلَّهُمْ يَتَذَكَّرُونَDõmin haka kawai Muka sauƙaƙar da shi (Alƙur'ãni) da harshenka, tsammãninsu, su riƙa tunãwa.0 Views
- فَارْتَقِبْ إِنَّهُم مُّرْتَقِبُونَSai ka yi jira. Lalle sũ, mãsu jira ne.0 Views