Mushaf Page 595
صفحة ٥٩٥
- Ghunnah
- Qalqalah
- Ikhfa (Haqiqi)
- Ikhfa Shafawi
- Idgham with Ghunnah
- Idgham without Ghunnah
- Idgham Shafawi (Mimi)
- Madd Lazim (6 counts)
- Madd Wajib Muttasil (4-5 counts)
- Madd Jaiz Munfasil (2, 4, 6 counts)
Each word’s meaning appears right below it; the transliteration follows below the words.
Surah ash-shams
Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
- وَالشَّمْسِ وَضُحَاهَاIna rantsuwa da rãnã da hantsinta.1 Views
- وَالْقَمَرِ إِذَا تَلَاهَاKuma da wata idan ya bi ta.1 Views
- وَالنَّهَارِ إِذَا جَلَّاهَاDa yini a lõkacin da ya bayyana ta.1 Views
- وَاللَّيْلِ إِذَا يَغْشَاهَاDa dare a lõkacin da ya ke rufe ta.1 Views
- وَالسَّمَاءِ وَمَا بَنَاهَاDa sama da abin da ya gina ta.1 Views
- وَالْأَرْضِ وَمَا طَحَاهَاDa ƙasã da abin da ya shimfiɗa ta.1 Views
- وَنَفْسٍ وَمَا سَوَّاهَاDa rai da abin da ya daidaita shi.1 Views
- فَأَلْهَمَهَا فُجُورَهَا وَتَقْوَاهَاSa'an nan ya sanar da shi fãjircinsa da shiryuwarsa.1 Views
- قَدْ أَفْلَحَ مَن زَكَّاهَاLalle ne wanda ya tsarkake shi (rai) ya sãmi babban rabo.1 Views
- وَقَدْ خَابَ مَن دَسَّاهَاKuma lalle ne wanda ya turbuɗe shi (da laifi) ya tãɓe.1 Views
- كَذَّبَتْ ثَمُودُ بِطَغْوَاهَاSamũdãwa sun ƙaryata (Annabinsu), dõmin girman kansu.1 Views
- إِذِ انبَعَثَ أَشْقَاهَاA lõkacin da mafi shaƙãwarsu ya tafi (wurin sõke rãkumar sãlihu).1 Views
- فَقَالَ لَهُمْ رَسُولُ اللَّهِ نَاقَةَ اللَّهِ وَسُقْيَاهَاSai Manzon Allah ya gaya musu cewa: "Ina tsõratar da ku ga rãƙumar Allah da ruwan shanta!"1 Views
- فَكَذَّبُوهُ فَعَقَرُوهَا فَدَمْدَمَ عَلَيْهِمْ رَبُّهُم بِذَنبِهِمْ فَسَوَّاهَاSai suka ƙaryata shi, sa'an nan suka sõke ta. Sabõda haka Ubangijinsu Ya darkãke su, sabõda zunubinsu. Sa'an nan Ya daidaita ta (azãbar ga mai laifi da maras laifi).1 Views
- وَلَا يَخَافُ عُقْبَاهَاKuma bã ya tsõron ãƙibarta (ita halakãwar).1 Views
Surah al-layl
Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
- وَاللَّيْلِ إِذَا يَغْشَىٰInã rantsuwa da dare a lõkacin da yake rufẽwa.1 Views
- وَالنَّهَارِ إِذَا تَجَلَّىٰDa yini a lõkacin da yake kuranyẽwa.1 Views
- وَمَا خَلَقَ الذَّكَرَ وَالْأُنثَىٰDa abin da ya halitta namiji da mace.1 Views
- إِنَّ سَعْيَكُمْ لَشَتَّىٰLãlle ne ayyukanku, dabam-dabam suke.1 Views
- فَأَمَّا مَنْ أَعْطَىٰ وَاتَّقَىٰTo, amma wanda ya yi kyauta, kuma ya yi taƙawa.1 Views
- وَصَدَّقَ بِالْحُسْنَىٰKuma ya gaskata kalma mai kyãwo.1 Views
- فَسَنُيَسِّرُهُ لِلْيُسْرَىٰTo, zã Mu sauƙaƙe masa har ya kai ga sauƙi.1 Views
- وَأَمَّا مَن بَخِلَ وَاسْتَغْنَىٰKuma amma wanda ya yi rõwa, kuma ya wadãtu da kansa.1 Views
- وَكَذَّبَ بِالْحُسْنَىٰKuma ya ƙaryatar da kalma mai kyãwo.1 Views
- فَسَنُيَسِّرُهُ لِلْعُسْرَىٰTo, zã Mu sauƙaƙke masa har ya kai ga tsanani.1 Views
- وَمَا يُغْنِي عَنْهُ مَالُهُ إِذَا تَرَدَّىٰKuma dũkiyarsa ba ta wadãtar masa da kõme ba, a lõkacin da ya gangara (a wuta).1 Views
- إِنَّ عَلَيْنَا لَلْهُدَىٰLãlle aikinMu ne, Mu bayyana shiriya.1 Views
- وَإِنَّ لَنَا لَلْآخِرَةَ وَالْأُولَىٰKuma lalle ne Lãhira da duniya Namu ne.1 Views
- فَأَنذَرْتُكُمْ نَارًا تَلَظَّىٰSabõda haka, Na yi maku gargaɗi da wuta mai babbaka.1 Views