91. ash-shams
الشمس
Read Surah ash-shams in full: surah 91, 15 verses, Meccan, Juz 30. Arabic text with Hausa translation.
- Ghunnah
- Qalqalah
- Ikhfa (Haqiqi)
- Ikhfa Shafawi
- Idgham with Ghunnah
- Idgham without Ghunnah
- Idgham Shafawi (Mimi)
- Madd Lazim (6 counts)
- Madd Wajib Muttasil (4-5 counts)
- Madd Jaiz Munfasil (2, 4, 6 counts)
Each word’s meaning appears right below it; the transliteration follows below the words.
Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
- وَالشَّمْسِ وَضُحَاهَاIna rantsuwa da rãnã da hantsinta.1 Views
- وَالْقَمَرِ إِذَا تَلَاهَاKuma da wata idan ya bi ta.1 Views
- وَالنَّهَارِ إِذَا جَلَّاهَاDa yini a lõkacin da ya bayyana ta.1 Views
- وَاللَّيْلِ إِذَا يَغْشَاهَاDa dare a lõkacin da ya ke rufe ta.1 Views
- وَالسَّمَاءِ وَمَا بَنَاهَاDa sama da abin da ya gina ta.1 Views
- وَالْأَرْضِ وَمَا طَحَاهَاDa ƙasã da abin da ya shimfiɗa ta.1 Views
- وَنَفْسٍ وَمَا سَوَّاهَاDa rai da abin da ya daidaita shi.1 Views
- فَأَلْهَمَهَا فُجُورَهَا وَتَقْوَاهَاSa'an nan ya sanar da shi fãjircinsa da shiryuwarsa.1 Views
- قَدْ أَفْلَحَ مَن زَكَّاهَاLalle ne wanda ya tsarkake shi (rai) ya sãmi babban rabo.1 Views
- وَقَدْ خَابَ مَن دَسَّاهَاKuma lalle ne wanda ya turbuɗe shi (da laifi) ya tãɓe.1 Views
- كَذَّبَتْ ثَمُودُ بِطَغْوَاهَاSamũdãwa sun ƙaryata (Annabinsu), dõmin girman kansu.1 Views
- إِذِ انبَعَثَ أَشْقَاهَاA lõkacin da mafi shaƙãwarsu ya tafi (wurin sõke rãkumar sãlihu).1 Views
- فَقَالَ لَهُمْ رَسُولُ اللَّهِ نَاقَةَ اللَّهِ وَسُقْيَاهَاSai Manzon Allah ya gaya musu cewa: "Ina tsõratar da ku ga rãƙumar Allah da ruwan shanta!"1 Views
- فَكَذَّبُوهُ فَعَقَرُوهَا فَدَمْدَمَ عَلَيْهِمْ رَبُّهُم بِذَنبِهِمْ فَسَوَّاهَاSai suka ƙaryata shi, sa'an nan suka sõke ta. Sabõda haka Ubangijinsu Ya darkãke su, sabõda zunubinsu. Sa'an nan Ya daidaita ta (azãbar ga mai laifi da maras laifi).1 Views
- وَلَا يَخَافُ عُقْبَاهَاKuma bã ya tsõron ãƙibarta (ita halakãwar).1 Views
Teks Al-Qur'an: Tanzil Project (https://tanzil.net), lisensi CC BY 3.0. · Abubakar Mahmoud Gumi (Tanzil Project, tanzil.net)