87. al-ala
الأعلى
Read Surah al-ala in full: surah 87, 19 verses, Meccan, Juz 30. Arabic text with Hausa translation.
- Ghunnah
- Qalqalah
- Ikhfa (Haqiqi)
- Ikhfa Shafawi
- Idgham with Ghunnah
- Idgham without Ghunnah
- Idgham Shafawi (Mimi)
- Madd Lazim (6 counts)
- Madd Wajib Muttasil (4-5 counts)
- Madd Jaiz Munfasil (2, 4, 6 counts)
Each word’s meaning appears right below it; the transliteration follows below the words.
Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
- سَبِّحِ اسْمَ رَبِّكَ الْأَعْلَىKa tsarkake sũnan Ubangijinka Mafi ɗaukaka.3 Views
- الَّذِي خَلَقَ فَسَوَّىٰWanda Yã yi halitta sa'an nan Ya daidaita abin halittar.3 Views
- وَالَّذِي قَدَّرَ فَهَدَىٰKuma Wanda Ya ƙaddara (abin da Ya so) sannan Ya shiryar, (da mutum ga hanyar alhẽri da ta sharri).3 Views
- وَالَّذِي أَخْرَجَ الْمَرْعَىٰKuma Wanda Ya fitar da makiyãyã.3 Views
- فَجَعَلَهُ غُثَاءً أَحْوَىٰSa'an nan Ya mayar da ita ƙeƙasassa, baƙa.3 Views
- سَنُقْرِئُكَ فَلَا تَنسَىٰZa mu karantar da kai (Alƙur'ãni) sabõda haka bã zã ka mantã (shi) ba.3 Views
- إِلَّا مَا شَاءَ اللَّهُ ۚ إِنَّهُ يَعْلَمُ الْجَهْرَ وَمَا يَخْفَىٰFãce abin da Allah Ya so, lalle ne Shi (Allah) Ya san bayyane da abin da yake bõye.3 Views
- وَنُيَسِّرُكَ لِلْيُسْرَىٰKuma za Mu sauƙaƙe maka (al'amari) zuwa ga (Shari'a) mai sauƙi.3 Views
- فَذَكِّرْ إِن نَّفَعَتِ الذِّكْرَىٰSabõda baka, ka tunãtar, idan tunatarwa zã ta yi amfãni.3 Views
- سَيَذَّكَّرُ مَن يَخْشَىٰWanda yake tsõron (Allah) Zai tuna.3 Views
- وَيَتَجَنَّبُهَا الْأَشْقَىKuma shaƙiyyi, zai nisanceta,3 Views
- الَّذِي يَصْلَى النَّارَ الْكُبْرَىٰWanda zai shiga wutar da tã fi girma.3 Views
- ثُمَّ لَا يَمُوتُ فِيهَا وَلَا يَحْيَىٰSa'an nan bã zai mutu ba a cikinta, kuma bã zai rãyu ba.3 Views
- قَدْ أَفْلَحَ مَن تَزَكَّىٰLalle ne wanda ya tsarkaka (da ĩmãni) yã sãmu babban rabo.3 Views
- وَذَكَرَ اسْمَ رَبِّهِ فَصَلَّىٰKuma ya ambaci sũnan Ubangijinsa, sa'an nan yã yi salla.3 Views
- بَلْ تُؤْثِرُونَ الْحَيَاةَ الدُّنْيَاBa haka ba! Kunã zãɓin rãyuwa ta kusa dũniya.4 Views
- وَالْآخِرَةُ خَيْرٌ وَأَبْقَىٰAlhãli Lãhira ita ce mafi alheri kuma mafi wanzuwa.4 Views
- إِنَّ هَـٰذَا لَفِي الصُّحُفِ الْأُولَىٰLalle ne, wannan yanã a cikin littafan farko.1 Views
- صُحُفِ إِبْرَاهِيمَ وَمُوسَىٰLittaffan Ibrãhĩm da Mũsã.1 Views
Teks Al-Qur'an: Tanzil Project (https://tanzil.net), lisensi CC BY 3.0. · Abubakar Mahmoud Gumi (Tanzil Project, tanzil.net)